‘’Taron kasa alheri ne ga Arewa’’
A ranar litinin ce shugaban kasa Goodluck Jonathan a jawabin da ya yi wa kasar nan saboda cikarta shekara 53 da samun ‘yancin kanta, ya bayyana kafa wani kwamiti mai mutum goma sha uku a karkashin jagorancin Dokta Femi Okurounmu da Dokta Akilu Indabawa a matsayin sakatare, domin bayar da shawarar yadda za a gudanar […]

A ranar litinin ce shugaban kasa Goodluck Jonathan a jawabin da ya yi wa kasar nan saboda cikarta shekara 53 da samun ‘yancin kanta, ya bayyana kafa wani kwamiti mai mutum goma sha uku a karkashin jagorancin Dokta Femi Okurounmu da Dokta Akilu Indabawa a matsayin sakatare, domin bayar da shawarar yadda za a gudanar da taron kasa da zai bai wa al’ummomin kasar nan damar taruwa domin su tattauna matsalolin da suka shafe su.
A baya dai shugaba Jonathan ya sha sukar wannan ra’ayi na taron kasa, amma sai kwatsam aka wayi gari da wannan sanarwa da ta fito daga bakinsa. Kodayake wadansu na ganin ya yi haka ne domin ya karkatar da hankalin mutane daga sukar da ake yi masa na cewa yana kokarin yin ta-zarce. A yayin da wadansu kuma ke ganin so yake ya yi amfani da wannan damar ya tabbatar wa yankin Neja-delta burinsu na mallakar albarkatun kasa da ke yankinsu.
Sauran walikilan kwamitin su ne,Farfesa George Obiozor da Farfesa Ben Nwabueze da Sanata Khairat Gwadabe da Sanata Timothy Adudu da Kanar Tony Nyiam (ritaya) da Farfesa Funke Adebayo da Dokta Mairo Ahmad Amshi da Dokta Abubakar Sadik da Alhaji Dauda Birma da Malam Buhari Bello da kuma Mista Tony Uranta.
Aminiya ta tuntubi wadansu masana a harkar shari’a da ke yankin arewacin kasar nan domin su yi bayani a kan alfanun ko rashinsa da yankin Arewa za ta samu idan an gudanar da taron..
Taron zai kwato wa Arewa hakkinta ne -Solomon Dalung
Barista Solomon Dalung mai fafutukar kare hakkin dan’adam kuma mai shirhi kan al’amuran yau da kullum. A wannan tattauna da ya yi da wakilinmu Hussaini Isah, ya bayyana irin alfanun da Arewa za ta samu a wajen taron kasa da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce zai shirya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Wane tsoro ne kake ganin Arewa za ta ji dangane da taro kasa da Shugaban kasa Jonathan ya ce zai shirya?
Solomon Dalung. Idan dai har taron kasa ne za a shirya, tambayar da za mu yi ita ce, wane irin taron kasa ne za a shirya?. Domin ba yau ne aka fara shirya taron kasa a Nijeriya ba. An yi taron kasa kan duba tsarin mulkin kasar nan a shekara ta 1957 lokacin da aka samu tangarda tsakanin arewaci da kudancin kasar nan kan maganar ba da mulkin kan kasar nan ga ‘yan Nijeriya.
Bayan haka an sha kiran irin wannan taro da dama. Domin a duk lokacin da aka sam matsalar shugabanci da almubazaranci da zalunci sai a kira taron kasa don a samu mafaka. Saboda haka idan aka ce za a shirya taron kasa, to wanne irin taron kasa ne za a shirya?
Idan taron kasa mai cikakken iko ne da ake magana za a shirya. To idan Shugaban kasa ya shirya wannan taro dole ne ya sauka, dole ne ‘yan majalisu su sauka. Domin shugaban wannan taron kasa, shi ne zai zama shugaban kasa su kuma wakilan da za a tura zuwa wajen wannan taro su ne za su zama kamar ‘yan majalisa. Kuma su ne za su tattauna dukkan abubuwan da suka shafi kasar nan.
Amma idan shugaban kasa Goodluck Jonathan yana maganar zai shirya taron kasa na siyasa ne, wanda yake ganin zai iya amfani da shi wajen biya masa bukata kan zaben shekara ta 2015. To za mu ce wannan yaudara ce da aka saba yi wa ‘yan Nijeriya.
Amma a matsayinmu na Arewa idan za a kira taron kasa mai cikakken iko ba ma shakka a je wannan taro. Domin idan ana magana a Nijeriya mu Arewa mune muka fi kowa yawan al’umma, mune muka fi yawan fadin kasa, mune muka fi yawan arziki. Saboda haka tsoron meye za mu ji kan shirya taron kasa a Nijeriya? Ai mu shirya wannan taro gaba za ta kai mu, domin muma a Arewa an cuce mu a wurare da dama. Misali an debi dukiyoyinmu, kamar kuzurmu da gyada da auduga da fatu a wurare da dama a nan Arewa an je an gina kasar nan, an je an sayo kayayyakin da ake hako mai da su a yau.
Aminiya: Wato a ganinka Arewa za ta samu wani alfanu a wannan taron kasa da za a shirya?
Solomon Dalung. Ai mu wannan taro alheri ne a gare mu. Domin cutar da ake yi mana za mu samu wakilan da za su je su kwato mana hakkinmu. A yanzu haka a gwamnatin tarayya yawan ma’aikatan da suka fito daga Arewa kashi 18 bisa 100 ne kawai Arewa take da shi a jihohi 19 da muke da su a Arewa, wannan ba zalunci ba ne?. Saboda haka wannan taron kasa zai magance irin wannan zaluncin.
Kuma idan ana maganar man fetur ne mu ma idan aka yi wannan taro aka fasa kasar za a san muna da man fetur a nan Arewa ko ba mu da shi. Saboda haka a je a yi wannan taron kasa.
Bayan haka, babbar ribar da nake ganin za mu sam, idan an fasa kasa shi ne irin dimbin gidajen ‘yan kabilar Ibo da sauran mutanen kudu suke nan Arewa wadanda za mu samu. Idan muka sayar da wadannan gidaje za mu samu biliyoyin naira. Don haka mu Arewa ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba.
Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar arewa dangane da wannan taro?
Solomon Dalung. Abin da zan gaya wa mutanen Arewa shi ne an dade ana yaudararsu, ana cewa musulmi da kiristoci ne damurwarsu. Duk wadannan wadansu dabaru ne na wargaza hadin kan Arewa. To yanzu an ce za a kira taron kasa, saboda haka mu hada kanmu, mu rungumi junanmu, mu kwana da shirin wannan taro.
Na dade ina ce wa mutanen Arewa babu abin da ya fi kauna da son juna. Mu mutane ne masu dimbin al’adu da addinai daban-daban, haka Allah ya shinfida mana, dole ne mu rungumi juna. Kuma dole ne gwamnoninmu na Arewa su dawo su rungumi al’ummarsu. Mun dade muna kiran gwamnonin Arewa kan su dawo su rungumi al’ummarsu, amma sun yi banza da wadannan kiraye-kirayen suka je suka hada wani taron kuraye da sunan wai wata jam’iyya. Saboda haka dole ne mu dawo mu hada kai mu zabi wakilai na gari wadanda za su je su yi maganin abubuwan da suke damun Arewa.
…Ba abin damuwa ba ne ga Arewa – Farfesa Auwalu Yadudu
Isa Muhammad Inuwa, daga Kano
Farfesa Auwalu Yadudu na Jami’ar Bayero ta Kano ya bayyana cewa ko kadan taron kasa da shugaba Jonathan yake so a gudanar domin tattauna makomar kasar nan ba wani abin damuwa ba ne. Amma ya kamata a bi wadansu ka’idoji kuma a zabo mutanen da za su wakilci kowane bangare na kasar nan bisa dacewa da cancanta ta kwarewa da iliminsu da kuma ingancinsu.
Ya ce ya kamata su kuma wakilan da za a tura wajen tattaunawar su samu cikakkiyar fahimtar yanayi da al’adu da kuma bukatun mutanen da suke wakilta. Sannan kuma ya kamata su shigar da wadannan ra’ayoyi ko bukatu na mutanen nasu wajen wannan taron.
A game da tsoron da wadansu ke yi na cewa taron makomar kasa tamkar wata hanya ce ta neman raba kasar kuwa, sai Farfesa Yadudu ya ce shi yana ganin ba haka abin yake ba. Ya ce ai tattauna makomar kasa wata hanya ce ta lalubo mafita ta yadda kowane sashe zai san matsayinsa da ‘yancinsa a cikin kasar.
Ya kara da cewa, “yin taron a bisa kabilanci shi ne bai dace ba kuma ba shi da tushe a tsarin mulki. Amma yin taron tattauna makomar kasa yana da tushe a cikin kundin tsarin mulkin kasa, don haka muddin dai ba za a yi rashin gaskiya a wajen tsara abin ba, to babu laifi.”
Ya ce tunda tsarin Dimukuradiyya ko kuma na zabe yana la’akari ne da yawan jama’a, haka ma sakamakon tattaunawar taron zai bayyana mafi rinjaye ne na ra’ayoyin ‘yan Najeriya. Domin haka, “matukar ba za a yi wata ‘yar burun-burun a wajen shirya taron da kuma tattaunawar ba, bai kamata a ji wani tsoro ko shakka ta yin taron na makomar kasa ba.”
kungiyar ACF ta goyi bayan taron
kungiyar Kare Maradun Arewa (ACF) ta ce a shirye take ta amince da taron kasa da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamiti da zai samar da hanyoyin da za a bi wajen gudanar da shi.
Mai magana da yawun kungiyar ta ACF Mista Anthony Sani ne ya bayyana haka a zantarwarsa da kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) a lokacin da yake bayyana matsayin kungiyar a sakamakon wannan mataki da shugaban kasa ya dauka.
“ kungiyar ACF ta dade da bayyana matsayinta a kan wannan batu cewa ba ta adawa da taro na kasa wanda zai kawo kwanciyar hankali da cigaban Najeriya. Musamman idan wannan taro ba zai dauki matsayin taron sanin makoman kasar ba. Saboda taron sanin makoman kasa da wadansu ke yin kira a kai wata dama ce da za ta sa a ruguza tsarinmu na Damokradiyya, wanda kuma babu wani ko wata kungiya da ke da alhakin yin hakan. Saboda haka mun amince da taron kasa, amma ba mu yarda da taron sanin makomar kasa ba,” inji shi.
Mista Sani ya kuma cigaba da cewa, kungiyar ACF za ta bayyana cikekken ra’ayinta dangane da wannan batu idan gwamnatin tarayya ta fitar wa da ‘yan Najeriya manufofin wannan kwamiti da ta kafa.
Taron ya saba wa tsarin mulki
-Lauya Bello Jahun
Wani malamin a fannin karantar da aikin lauya na jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya Dokta Bello Ibrahim Jahun kuma lauya mai zaman kansa ya bayyana cewa, ‘tsirin mulkin Najeriya wanda yake da fitatun abubuwa halattatu da shugabanni za su yi bai kawo taron kasa a ciki ba kwata-kwata, kuma abin da tsirin mulki Najeriya bai kawo ba duk wanda ya ce zai aikata shi haramtace ne.’.yaci gaba da cewa, ‘Muna da majalisu tun daga kananan hukomomi zuwa na jahohi har zuwa na tarayya, wadanan majalisu sune suke da ikon yin wata doka ta karamar hukuma ko ta jiha ko ta kasa baki daya. Wadannan mutanen da suka samu kansu a wadannan mukamai mutane ne wadanda’yan Najeriya suka taru suka zabe domin su wakilice su daga kowane lungu na kasar nan, kuma sune suka san ko’ina, kuma an zabe su ne a karkashin tsarin mulkid da aka yarba da shi na 1999, ka ga mutanen da ake tsamani za a iya cewa an zabo su yi wannan taro na suke fasalin kasa mutane ne wadanda za su fito bisa tunaninsa shi kadai a bisa umurnin mutanen jeka-na yi ka, wato ba a demukaradiyya ba, wato a demokoradiyya kowane dan Najeriya yana da ikon fadin albarkacin bakinsa wajen zartar da hukunci da kuma dokokin kasa ta hanyar fadin dukkan bukatunsa ta hannun wakilansa.’
Dokta Jahun ya kara da cewa, ‘wadannan mutanen da Jonathan yake so su taru don yin wannan taro a ina ne tushen da suke da shi wanda ya ba su dammar su yi wannan taron, mun san cewa majalisun kasa suna da iko ne karkashin tsarin mulki da aka ba su ta hanyar zabe su wakilce jamarsu. To duk wanda ya tara mutane na daban domin su yi taro don su fitar da wani shiri yadda kasar za ta zama haka kawai, to ba shi da huruni a cikin tsarin mulkin Najeriya, saboda haka ya zama haramtace ne kuma kamar yin karan-tsaye ne a cikin kudin tsarin mulki.
Ya ce, ‘abin da shugaban kasa yake so ya yi shi,ne, ga wadansu mutane da mutanen Nejeriya suka sanda su a matsayin wakilansu domin su tsara musu dokoki, sai shi ya nuna kamar bai yarda da su ba kuma bai amince da su ba har zai nemo wadansu daga a waje domin su yi masa tsari na daban wanda doka ba ta ba su ba, don haka yin haka ya saba, dole ne a bar ‘yan majalisu na kasa su yi aikinsu.’