Taron kasa da batun kananan kabilu da kashe-kashe a Arewa

Ya zuwa yanzu taron kasa yana neman shiga mako na uku da cigaba, bayan samun tabbatuwar tsarin irin yadda za a rika tafiyar da shi. Wakilai sun cigaba da bayyana ra`ayoyinsu kan jawabin kaddamarwa na Shugaba Goodluck Jonathan. Taron na da wa`adin watanni uku a kammala shi.A lokacin da ake cikin wancan hali a wajen […]

Taron kasa da batun kananan kabilu da kashe-kashe a Arewa
Taron kasa da batun kananan kabilu da kashe-kashe a Arewa

Ya zuwa yanzu taron kasa yana neman shiga mako na uku da cigaba, bayan samun tabbatuwar tsarin irin yadda za a rika tafiyar da shi. Wakilai sun cigaba da bayyana ra`ayoyinsu kan jawabin kaddamarwa na Shugaba Goodluck Jonathan. Taron na da wa`adin watanni uku a kammala shi.
A lokacin da ake cikin wancan hali a wajen taron, rikicin nan da ya dauko asali daga `yan kungiyar Boko Haram, da ma wani daban, ya ci gaba da yaduwa a wasu jihohin Arewa, ana kuma ta zubar da jinin bayin Allah da ba su ji ba su gani ba. Rikicin da aka fara daga Maiduguri a watan Yulin shekarar 2009 da yaduwarsa a shiyyar Arewa maso Gabas, ya sanya tun a watan Mayun bara gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci a jihohin Barno da Yobe da Adamawa. A baya-bayan nan kuma sai ga annobar fadace-fadacen Fulani makiyaya da Manoma da satar shanu, wadda aka dade ana fama da ita a Jihar Filato ta fantsama zuwa cikin jihohin Kaduna daNassarawa da Binuwai da Kaduna; baya ga rikicin da ake ta’allaka shi da barayin shanu ko `yan fashi da makami da take addabar jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara.
Idan mai karatu zai lissafa, sannu a hankali, zai ga cewa tun da aka fara wannan rikici na `yan Boko Haram, jihohi sama da 10 daga cikin 19 na Arewa suka fada cikin wannan annoba, wadda bayan haddasa kashe-kashen rayuka da jikkata al`umma, tana kuma haddasa asarar dukiya da ba wanda zai iya kiyasinta. A takaice dai Arewa da al`ummominta suna cikin annobar yakin da ba su taba gani ba a rayuwa, yakin da ake zargin, bayan kungiyar ta Boko Haram, jami`an tsaro da ke da alhakin kare rayukan jama`a da dukiyoyinsu, su ma suna taimakawa wajen kashe jama`a da ba su ji ba su gani ba, duk da irin dubban miliyoyin Naira da mahukunta ke kashe musu da sunan su iya kawo karshen annobar.
A kiyasin da kungiyar Muradin Kare Hakkin dan Adam ta kasar Amurka (Amnesty International) ta fitar kwanan nan ya tabbatar da cewa tsakanin watan Janairun bana zuwa na Maris, watanni uku ke nan, an kashe mutum 1,500 a cikin annobar,wanda yake adadi mafi yawa a tarihin rikicin, rahoton da jami`an tsaro suka karya. Ita ma a rahoton da ta dauko a shafinta na farko a ranar Lahadin wannan makon, jaridar Sunday Trust ta ruwaito cewa kasar nan, ita ce ta farko a cikin kasashen duniya a kan kashe-kashe na `yan kungiyoyi irin na Boko Haram. Ta ce a cikin watanni ukun, mutum 1,219, aka kashe a nan kasar. kasar Iraki ita ke bi ma kasar nan da mutum 559; sai ta Pakistan mai mutum 124; yayin da Afganistan take da mutum 89.  A wata kididdigar ma an ce mutum sama da 4,000 suka kwanta dama a rikicin na Boko Haram.
Mai karatu, abin da nake son in yi magana a yau shi ne, duk da irin wannan mummunar annoba da Arewa da ma kasar nan take ciki na tashe-tashen hankula, tashe-tashen hankulan da suka kai matsayin da shi kanshi taron kasar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da lallai ta san matakan da za ta dauka don kawo karshensa, bai wuce hirar da jaridar Sunday Trust din, a shafukanta na 13 da 14 ta dauko, wadda aka yi da Mista Leonard Nzodon, wani lauya mai zaman kasan daga Jihar Adamawa da yake cikin tsirarin kabilu 15 da suke wakiltar shiyyar ta Arewa maso Gabas ba, inda ya baje kolinsa a kan irin tsarabar da su tsirarun kabilu suka je da ita wajen taron kuma suke son su samu a yi na`am da ita.
Mista Leonard, ya koka a kan irin zaman da su tsirarun kabilu suke ciki a Jihar Adamawa a kan rashin masarautu na kansu, abin da ya ce ya dauko asali tun ma kafin jihadin Shehu Usman danfodiyo da bayan jihadin da zuwan Turawa da kuma bayan samun ’yancin kan kasar nan. A nasa tunanin, yana ganin ya kamata a ce an daina nada musu sarakuna daga Masarautar Lamido ana tura musu yankunansu na kananan kabilu. Ma`ana a rika ba su nasu. Wani batu da ya yi kuma shi ne irin yadda aka bi manya-manyan wurare a Yola aka sa musu sunan Modibbo Adama, wanda shi ne Lamidon da ya yi jihadi ya kafa Masarautar ta Adamawa, masarautar da jihadinta ya shiga har cikin kasar Kamaru. Ya kawo misalai da canjin sunan Jami`ar Fasaha ta Tarayya da ke Yola da shi kanshi sunan jihar daga wancan Basarake aka samo shi.
A kan manyan makaratu ma Mista Leonard ya koka cewa daga cikin 10 da ake da su a jihar, 6 daga cikinsu suna babban birnin jihar wato Yola ne, kuma akasari shugabanninsu `yan kabilar Fulani ne, alhali Fulanin ba su suka fi sauran tsirarin kabilu 88 da ake da su a jihar ilimi ba.
Daga waccan hira, Mista Leonard ya fadi cewa shi da `yan uwansa tsirarun kabilun Arewa gashin kansu suke so su ci a wannan karni na 21. Irin wadannan bukatu da ya ambata da su suka zo taron kasar, a daidai lokacin da Arewar ta kama da wuta, har ma wasu suke ganin taron ba shi da wata makoma, amma shi gare su suna ganin samun masarautun tsirarun kabilu da kuma nada  mutanensu a kan muhimman mikaman gwamnati, su za su mayar da hankali a wajen taron. Ni kuwa ina gani lokaci ya yi da tsirarun kabilun Arewa za su rika bin kundin tarihin kafuwar yankunansu tun asali, ba don yanzu suna iya magana ba, a kuma irin wannan mawuyacin hali su ce ga yadda suke so lallai a yi musu, duk da ba a yau suka fara irin wannan yunkuri ba.  
Ya kamata tsirarun kabilun kasar nan su tuna, in sun manta, cewa duk abin da ake a Arewa yau yana tafiya ne a kan tarihin kafuwarta, ko da Turawan mulkin mallaka da suka ci Arewa saboda sun taras da sarakunanta suna da tsarin mulkin tafiyar da jama`arsu ya sanya ba su kutsa kai suka karbe mulkin ba, sai suka koma daga baya suka sa sarakunan suna mulki a madadinsu, wato tsarin ‘Indirect rule’.
A nawa ra`ayin, kamar kuma yadda ake ta magana, babban batun da ya kamata, duk wani dan Arewa, wakili a taron kasa da wanda ma ba ya cikin taron, ya dage a kai shi ne yadda za a kawo karshen wannan annoba ta kashe-kashe. Batun neman masarauta ko ana kwarar su wane a kan rabon mukamai ko wasu abubuwan more jin dadin rayuwa, ba na `yan Arewa ba ne a halin yanzu.