Taron kasa: Dalilin canja tunanina – Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce a baya yana shakkun kiran taron kasa saboda irin yadda ake fassara shi cewa zai tatule kafafun dimokuradiyyar da kasar nan ke da shi a yanzu.Sai dai ya ce ya canja tunaninsa ne saboda bukatar da ake da ita na nemo mafita ga matsalolin kasar da suka sa […]

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce a baya yana shakkun kiran taron kasa saboda irin yadda ake fassara shi cewa zai tatule kafafun dimokuradiyyar da kasar nan ke da shi a yanzu.
Sai dai ya ce ya canja tunaninsa ne saboda bukatar da ake da ita na nemo mafita ga matsalolin kasar da suka sa irin wannan taro yake da muhimmanci, taron da ya ce zai karfafa hadin kan kasa.
Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake kaddamar da Kwamitin Bayar da Shawara kan Taron kasa mai mutum 13 a Abuja.
Ya ce, “Akwai wasu masu ra’ayin babu bukatar mu zauna tare mu tattauna kan kalubalen rayuwa da siyasa da suke fuskantar kasarmu. Wasu kuma suna ganin saboda mun gudanar da tarurruka a baya, ba mu bukatar yin wani taron. Ina daga cikin wadanda suke nuna shakku kan bukatar yin wani taron tattaunawa. Shakkar da nake yi ta faru ne kan irin suna ko fassarar da ake ba irin wannan taro, lura da shika-shikan dimokuradiyya da muka aza a kasar nan da suke nuna bukatun mutane.”
Ya ce, sai dai a yayin da kalubale suke dada bayyana, wajibi ne shugabanni su tunkare su da dukkan dabarun da suka fi dacewa domin tabbatar da ginshikin kasancewar kasar nan yana nan daram.
“Ba za mu ba da maganin gyambo ga mai ciwon ciki ba. A fili yake tattaunawa na kara wata daraja ga dorewar kasarmu. Bai kamata a kawar da kai kan muhimmancin tattaunawa ta kasa a yanzu ba,” inji Jonathan.
Ya ce akidar dimokuradiyyya ta nuna koda bayan mutane sun zabi masu tsara dokoki, akwai fagen da wadanda ake mulka za su iya ba da tasu gudunmawa ga harkokin dimokuadiyya ba tare da samun tufka da warwara kan abin da banagrorin mulki suke yi ba. “karfin iko zai ci gaba da kasancewa na al’umma, musamman idan al’ummar suka yi amfani da dabaru da hanyoyin da za su karfafa ginshikin da zai amfani ’ya’yan da ke zuwa a bayansu. Kuma irin wannan hadin gwiwa tsakanin jama’a da masu mulki zai ba da damar kawo gagarumar fahimtar juna da hadin kai. Domin babu abin da ya kai hadin kai da adalci da daidaito a kasar da ke mulkin dimokuradiyya,” inji shi.
Ya ce sabanin tsoron da wasu ke nunawa cewa taron zai sai a tuhumi martabar Najeriya, ya ce maimakon haka zai karfafa hadin kai da dinkewar kasar nan ne tare da warware batutuwan da aka yi watsi da su.
Shugaban kasar ya ba kwamitin mako shida ya mika rahotonsa.
Da yake mayar da jawabi shugaban kwamitin Sanata Femi Okurounmu ya yi alkawarin cewa kwamitinsa ba zai kunyata kasar nan ba.
Dokta Akilu Indabawa ne sakataren kwamitin yayin da sauran wakilan kwamitin suka hada da Farfesa George Obiozo da Farfesa Ben Nwabueze da Sanata Khairat Gwadabe da Sanata Timothy Aduda da ritaya Kanar Tony Nyiam da Farfesa Funke Adebayo da Misis Mairo Ahmed Amshi da Dokta Abubakar Sadik da Alhaji Dauda Birma da Malam Buhari Bello da kuma Mista Tony Uranta. Sai dai Farfesa Nwabueze bai halarci bikin ba, inda aka ce yana kasar waje domin duba lafiyarsa.