Taron kasa domin taimakon manoma ya yi armashi

Daraktan kamfanin sayar da takin zamani na Tiger Agro Allied da ke Malumfashi a Jihar Katsina, Alhaji Babangida ’Yankara ya ce, taron masu ruwa da tsaki da Ma’aikatar Gona ta Tarayya da hadin gwiwar jihohi suka yi a Jihar Kebbi kwanakin baya, domin lalubo hanyoyin da takin zamani zai rika isa ga manoma cikin sauki […]

Taron kasa domin taimakon manoma ya yi armashi
Taron kasa domin taimakon manoma ya yi armashi

Daraktan kamfanin sayar da takin zamani na Tiger Agro Allied da ke Malumfashi a Jihar Katsina, Alhaji Babangida ’Yankara ya ce, taron masu ruwa da tsaki da Ma’aikatar Gona ta Tarayya da hadin gwiwar jihohi suka yi a Jihar Kebbi kwanakin baya, domin lalubo hanyoyin da takin zamani zai rika isa ga manoma cikin sauki ya fara haifar da da mai ido.
Daraktan, wanda yana daga cikin mahalarta taron, ya ce: “Sabon salon bai daya da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi wajen bayar da irin shuka kyauta ga manoma da sayar musu takin zamani ta cikin wayar salula mai dauke da sunayensu ya fara amfani kwarai ga kananan manoma a Najeriya.”
Ya kara da cewa: “Muhimman abubuwa guda biyu da suka hada da samun irin shuka mai kyau da isar takin zamani ga manoma cikin lokaci su ne suke taimakawa wajen habaka harkokin noma. Yanzu gwamnati ta fara gudanar da wadannan muhimman abubuwa da take yi sau biyu kafin damina ta sauka tare da wayar da kan manoma a kan yadda za su yi amfani da su, wanda ba a samu irin haka a shekarun baya ba. Saboda haka, ya kamata wadannan manoma da suka fara cin wannan moriya, su yi wa Allah da Annabi su yi amfani da irin shuka da takin zamani da aka ba su ta hanyar da ta dace. Su daina karkatar da su suna sayarwa. Yin haka, zai taimaka wajen durkushewar harkokin noma musamman a sashen Arewacin kasa.
Ya yi kira ga gwamnati cewa: “Muddin ana so wannan tsari ya kankama, dole ne Gwamnatin Tarayya ta hana shigowa da amfanin gona da wasu kasashe ke nomawa domin manoman Najeriya su mayar da hankalin ga noman irin nasu amfanin. Kuma, wajibi ne ta tashi tsaye wajen samo hanyar sayen amfanin da manoma suka girbe, wanda zai karfafa musu gwiwar rungumar wannan tsari a gaba kuma zai taimaka wajen samar da wadataccen kayan abinci da rage yawan marasa aikin yi a kasar nan.”