Taron kasa karkatar da hankalin jama’a ne – Kwankwaso
Gwamnan Jihar Kano Injiniyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce taron kasa da Gwamnatin Tarayya take kokarin kira ba ya da wani alfanu ga ’yan Najeriya in ban da bata lokaci da yaudara da karkatar da hankalin jama’a.Gwanna Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido […]
Gwamnan Jihar Kano Injiniyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce taron kasa da Gwamnatin Tarayya take kokarin kira ba ya da wani alfanu ga ’yan Najeriya in ban da bata lokaci da yaudara da karkatar da hankalin jama’a.
Gwanna Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido a tsakiyar wannan mako, inda ya ce ya je jihar ce a kokarinsu na nemo mafita idan ba su samu daidaitawa ba a tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya kan rikicin da ke tsakaninsu.
Gwamna Kwankwaso ya ce sun kuma yi musayyar ra’ayi kan ayyukan da za su yi wa talakawan jihohinsu biyu a kokarinsu na samar da ayyukan raya kasa a jihohin.
Ya hori ’yan siyasa su rika yi wa talakawa aikin da aka zabe su maimakon bata lokacinsu a kan taron kasa.”Burinmu a samu ci gaba ba a yi amfani da wata dama a wawure dukiyar talakawa da wata manufa ta daban ba.
Da yake bayani kan jita-jitar za su koma Jam’iyyar APC ya ce babu gaskiya kan haka, domin har zuwa lokacin da yake magana da manema labarai babuwata shaida data nuna cewa za su koma sabuwar Jam’iyyar ta APC domin haryanzu kararsu tana gaban kotu sai kotu ta zartar da hukunci ne daga baya za su yi maganar ko ina za su dosa.