Taron kasa ko taron kawar da hankalin jama’a?

Gaskiya ne jam’iyyar APC, rashin mika sunayen wakilci a taron nakasa kasa da almubazzarantar da dukiyar talakawa, wanda shugaba Goodluck ya shirya da sunan lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye Najeriya ya yi daidai.Taron, kawar da hankalin al’ummar Najeriya ne a kan zaben 2015. Domin mun fahimci cewa, take-taken gwamnatin Goodluck shi ne ko […]

Taron kasa ko taron kawar da hankalin jama’a?

Gaskiya ne jam’iyyar APC, rashin mika sunayen wakilci a taron nakasa kasa da almubazzarantar da dukiyar talakawa, wanda shugaba Goodluck ya shirya da sunan lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye Najeriya ya yi daidai.
Taron, kawar da hankalin al’ummar Najeriya ne a kan zaben 2015. Domin mun fahimci cewa, take-taken gwamnatin Goodluck shi ne ko ta halin kaka so yake ya sake darewa kan madafun iko, ko talakawa na so ko ba su so, in dai burinsa ya cika an gama.
Wannan ya sa yake ta daukar matakan da za su dauke hankulan al’ummar kasarmu ta haihuwa, su koma kan abin da ya shafi taron kasa, wanda ba zai amfani talakawa ba daidai da kwayar zarra, face kara lalata dukiyar kasa da sunan taron kasa. Maimakon talaka ya yi nazarin yadda zai tunkari zaben 2015, ta hanyar gano wanda zai share masa hawaye, sai Goodluck ya yi amfani da salonsu na siyasa, ya kirkiri wani abu da zai dauke hankalin al’umma don cin ma manufarsu ta ’yan siyasa.
Babu abin da al’ummar kasa ke bukata kamar tsaron rayukansu, dukiyoyinsu, mutuncinsu da addininsu, ba wai taron neman kuri’un jama’a da sunan ziyarar aiki ba. A dalilin yawon kamfen a fakaice da yake yi ya sa daya daga cikin gwamnonin Arewa, Wamako ya ce ba abin da Goodluck yake face yawon gantali.
Idan talakawa da masu kishin kasa za su hankalta su dawo cikin hayyacinsu tun kafin wankin hula ya kai su dare.
dandattijo Bayan NEPA Malumfashi, Jihar Katsina (07039018940).

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno