Taron kasa mai cikakken iko: Gobara daga rafi…
Labudda dimokuradiyya na aiki a Najeriya domin kuwa kan talakawa ya waye, sun fahimci abin da ake nufi da ‘yanci, sun kuma bazama wajen neman shi. Shi ya sa talakawa suka rungumi bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta kago kiran wani taron da zai kawo karshen fitintunun da suka tayar da zaune tsaye a kasar nan […]
Labudda dimokuradiyya na aiki a Najeriya domin kuwa kan talakawa ya waye, sun fahimci abin da ake nufi da ‘yanci, sun kuma bazama wajen neman shi. Shi ya sa talakawa suka rungumi bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta kago kiran wani taron da zai kawo karshen fitintunun da suka tayar da zaune tsaye a kasar nan da kuma tottoshe kafafen da suka kukkurdo don kada a sake maimaita mawuyacin halin da ake ciki a halin yanzu. Dangane da haka ne wasu daga cikin fitattun ‘yan bokon Arewa suka shiga jerin masu da’awar da kwakwazo game da kiran wani muhimmin taro mai cikakken iko wanda a Turance ake kira Sobereign National Conference, domin ya sha bamban da irin wanda Shugaba Jonathan ke son kira.
Ma’abuta wannan taron sun dage lallai sai a tattara dukkan al’ummomi masu dabi’u da al’adu iri guda, don su tatauna dukkan abubuwan da ke addabar Najeriya, suna hana ci gaba da zaman lafiya, sa’annan kuma babu wani madafar iko ko wata hukumar da za ta yi katsalandan ko tsoma baki cikin sakamakonsa, sa’annan kuma shi ne zai zamanto kundin tsarin dokokin gudanar da harkokin mulkin kasar, kamar yadda masu halartar taron suka cimma matsaya. Wannan ya saba irin kundin tsarin mulkin da sojoji suka saba samar wa kasar a dukkan lokutan da suka nemi mayar da mulkin da suka kwata da karfin tsiya daga farar hula ko kuma wajen ‘yanuwansu da ke sanye da khaki. Kamar yadda aka saba a kasar nan soja kan kafa wata majalisa ce wacce bayan an yi zaben gama-gari don fitar da wadanda za su wakilci jama’a a cikinta, sai kuma su surka da nasu wakilan da sukan tsintsinto, kusan sulusin (1/3) wadanda aka zaba cikinta, kuma su ne za su tsara kundin dokokin mulkin kasar wanda daga bisani sojoji za su yi masa kwaskwarima, su cire abin da bai kwanta masu a rai ba, su kuma lullube shi da tsumma makunshin cuta, kafin su zartar da shi a matsayin sabon kundin mulkin kasar. Irin wancan tsarin samar da kundin da ba mai iya tabawa bai yiwuwa sai idan an kawar da gwamnati da kuma majalisa, ko kuma a irin lokutan da sojoji ke kumbuya-kumbuyar samar da sabon kundin da za su mika wa farar hular da suka murda, aka zaba.
Wannan ne babban dalilin da ya sa ake ta hankoron ganin an samo wata sabuwar dabarar tsara kundin tsarin mulki, ganin yadda kundayen da sojoji suka yi ta samarwa ba su magance matsalolin da suke ta sanya al’amura na kwan-gaba-kwan-baya ba, aka kuma kasa gano dalili balle a yi tunanin mafita. To shi ne ake ganin cewa idan aka samu hannaye da yawa sai a yi maganin muguwar miyar da ta ki karewa, balle a kada wata sabuwa. daya daga cikin wadanan hannayen ita ce ta kiran wancan taron da ‘yan kudu suka dade da amincewa da shi, wanda kuma duk gwamnatin da aka kawo mata wannan batu takan yi watsi da shi, domin kuwa ba zai yiwu ta yi kirari, ta daba wa cikinta wuka ba.
Mutane da yawa suna ta dari-dari da wannan batun, domin kuwa sun zaci cewa yin haka zai yi sanadiyar rabuwar kasar, ko kuma a muzguna wa wani sashe, musamman ma Arewar da ake takurawa. Shi ya sa da farko ‘yan Arewa ke ta nokewa wajen goyon bayan taron ‘yan kasa, kowane iri ne kuwa. Hakan kuma ya sa aka yi ta zarginsu da mayar da hannun agogo baya. To yanzu sun ce ba su tsoron kowane irin taro, sun ma fi son a yi wanda kafin a tsunduma cikinsa sai an warware dukkan wani tsarin gwamnati, shugaban kasa kuma ya sauka, an kuma jingine majalisun kasa, a bar kotuna da alkalan cikinta kadai su gudanar da kasar, har a fitar da sakamakon da wakilan taron suka tsara a matsayin sabon kundin tsarin mulki. ‘Yan Arewa sun ce haka shi ne kawai mafita ga kowa da kowa, a zo a yi zube-ban-kwaryata, kowa ya amayo abin da ke cikinsa, domin ranar wanka ba a boyon cibi. Daga nan kuma sai a daina yi wa juna kallon hadarin kaji, kowa ya san matsayinsa, a kuma zauna a haka. Tun daga jin wannan sabuwar matsaya ta ‘yan Arewa game da taron da Shugaba Goodluck Jonathan ke so a yi, sai hankulan shugabanni suka tashi, suna ta kumfar baki wajen sukan lamirin masu sha’awar a yi irin wancan taron wanda a cewarsu yin haka zai sa Shugaban kasa ya fita da fitarsa, ya kuma share fagen afkuwar gobara daga rafi ne, wacce Allah ne kadai ke iya maganinta,.