Taron kasa shirme ne da surkulle – Halifa Hassan Yusuf
Tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PRP a Jamhuriyya ta Biyu kuma wakili a wurin taron kasa, Halifa Hassan Yusuf ya ce babu abin da ke tare da taron kasar in ban da shirme da surkulle saboda babu wata kwakkwarar manufar ta shirya shi don amfani al’ummar kasa. ba hasali ma an kira shira […]
Tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PRP a Jamhuriyya ta Biyu kuma wakili a wurin taron kasa, Halifa Hassan Yusuf ya ce babu abin da ke tare da taron kasar in ban da shirme da surkulle saboda babu wata kwakkwarar manufar ta shirya shi don amfani al’ummar kasa.
ba hasali ma an kira shira taron ne ba tare da sahalewar kowace irin dokar kasa ba.
Alhaji Hassan Yusuf wanda shi ne Galadiman Damaturu ya bayyana haka ne a tattaunawa da Aminiya a Damaturu, inda ya ce, tun farko an kira taron ne ba tare da sahalewar kowace dokar kasa ba.
Halifa Hassan Yusuf ya ce tun farko da aka ce za a shirya taron kuma an sa sunansa daga Jihar Yobe a matsayin wakili na Arewa sai da ya tambayi kansa me zai kai wurin taron? Kuma mene ne makasudin shirya taron bayan akwai majalisun kasa biyu da na jihohi da suke da hakkin gyara tsarin mulki ko kafa dokoki ga kasa a matsayinsu na zababbun wakilan jama’a? Kuma in sun ba da shawarwari a ina za a ajiye su tunda a baya gwamnatin soja ta marigayi Sani Abaca ta shirya haka a 1994, kuma ba duka shawarwarin da suka bayar aka zartar ba, haka na lokacin Shugaba Obasanjo a shekarar 2004.
Ya ce daga bisani ya yanke shawarar halartar taron ne tunda an ce Shugaban kasa ne ya sa sunansa cikin mahalarta taron don haka akwai bukatar da ya je don kada a yi wa yankinsa na Arewa illa.
Halifa Yusuf ya ce bayan da ya samu kansa a zauren taro sai ya fahimci cewa lallai akwai boyayyiyar manufa ta shirya taron da ’yan Kudu suka shirya tunda Shugaban kasa daga bangarensu ya fito, kuma ga shi wakilan Arewa ba su fi 190 ba alhali mutanen Kudu Shugaban kasar ya ba su mambobi sama da 300, “A nan ne na ga fa’idar halartarta taron tunda mun hana ’yan Kudu cimma burinsu,” inji shi.
Galadiman Damaturun ya ce, duk kudirorin da ’yan Kudu suka kawo musamman kan abin da ya shafi mayar da kananan hukumomi zuwa jihohi da neman akalla kashi 50 cikin 100 na kudin mai da kuma kara musu jihohi da kafa ’yan sandan jihohi da uwa uba neman a sauya wa’adin mulki zuwa zango daya na shekara shida da makamantansu ba su cimma wadannan bukatu ba.
Ya ce don haka wannan taro da Shugaban kasa ya kira da ke gab da kawo karshe babu abin da ke tattare da shi in ba da kashe kudin al’ummar kasa haka siddan, “Kuma abin da ya rage shi ne al’ummar kasa su zuba ido su ga yadda za a yi da shawarwarin da taron ya zartar, kuma in har kun ga ’yan Kudu sun samu nasarar wannan taro, to sai dai in Shugaban kasa ne zai yi amfani da karfinsa ya rattaba hannu a kan wasu shawarwarin ba tare da amincewar majalisun kasa ba.