Taron kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya na bana zai gudana a Kano
kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya (Nigeria Folklore Society) da hadin gwiwar Cibiyar Bincike da Nazarin Harsunan Najeriya da Adabin Gargajiya ta Jami’ar Bayero Kano za ta gudanar da taronta na shekara-shekara a zauren taro na Musa Abdullahi da ke harabar jami’ar a Kano. Taron na bana mai taken ‘Adabin Gargajiya da Rayuwar Al’umma a […]
kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya (Nigeria Folklore Society) da hadin gwiwar Cibiyar Bincike da Nazarin Harsunan Najeriya da Adabin Gargajiya ta Jami’ar Bayero Kano za ta gudanar da taronta na shekara-shekara a zauren taro na Musa Abdullahi da ke harabar jami’ar a Kano.
Taron na bana mai taken ‘Adabin Gargajiya da Rayuwar Al’umma a Najeriya: Tasiri da kalubale a karni na 21” kuma zai hada da zaben shugabannin kungiyar karo na 13 tun kafa ta, inda za a shafe kwanaki uku ana yi. Za a bude shi ne ranar 29 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayun bana.
A wani jawabi da ya fito daga Shugaban kungiyar ta kasa, kuma marubucin littattafan adabin gargajiya da tarihi da hikimar mulki da tattalin arziki, Dokta Bukar Usman, ya ce: “Aikin farfado da kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya, kamar yadda aka kudurta a baya ya kammala a yanzu, don haka lokaci ya yi da ya kamata a waiwayi batun wakokin baka a Najeriya, ganin cewa wannan al’amari na wakar baka ne ya haifar da tunanin kafa wannan kungiya a Zariya a 1981.
“Mu sani cewa, wannan taro na Zariya, shi ne ya samar da ingantacce kuma bunkasasshen littafin nan mai suna “Wakokin Baka A Najeriya (Oral Poetry in Nigeria), wanda aka wallafa a 1982, wanda kuma a yanzu littafin ya bace. Littafin ya samu ne a karkashin tacewar Uchegbulam da wadansu da suka tallafa masa, kuma Sashin Kula Da Al’adu na Gwamnatin Tarayya ne ya dauki aikin wallafa shi. Lokaci ya yi a yanzu da ya kamata a shirya gagarumin taro a kan wannan muhimmin al’amari, domin samar da wani ingantaccen littafin, wanda zai ta’allaka kuma ya fito daga zababbun takardun da masana suka gabatar a kan maudu’in. Haka kuma za a tattara wadannan takardu da aka gabatar, domin wallafa su a cikin mujalla, inda haka zai farfado da Mujallar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya.
“Bisa ga haka, muna farin cikin gayyatar masana da manazarta da masu bincike su shirya ingantattun takardun nazari a kan maudu’an da aka samar domin wannan taro.”
Domin gudanar da wannan taro, an samar da maudu’ai daban-daban da ake son masana su gabatar da takardu a kai kamar haka: 1-Ayyukan Zahiri Dangane da Adabin Gargajiya a Najeriya. 2-Adabin Gargajiya da Sauyin Zamani A Duniya. 3-Ayyuka da Tasirin Adabin Gargajiya. 4-Al’amuran da Suka Shafi Jinsi a Adabin Gargajiya. 5-bangarorin Adabin Gargajiya. 6-Almara, Wakokin Gargajiya, Karin Magana, Zaurance, Barkwanci, Azancin Magana, karangiya da Sauransu. 7-Wasan Dabe, Fim da Wasan Kwaikwayo. 8-Adabin Gargajiya da Magungunan Gargajiya.
Sauran maudu’an sun hada da 9-Dangantakar Adabin Gargajiya da Harshe. 10-Wasannin Gargajiya da Bukukuwan Gargajiya. 11-Adabin Gargajiya da Kishin kasa. 12-Adabin Gargajiya da Tarihi. 13-Adabin Gargajiya da Tattalin Arziki. 14-Adabin Gargajiya da Al’amuran Shakatatawa da Bude Ido.
A yayin gudanar da taron, Babban Bako Mai jawabi shi ne Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed. Sauran manyan baki masu gabatar da kasidu sun hada da Farfesa Angela Miri da Farfesa Abdu Yahya Bichi da Farfesa Segun Adekoya da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Farfesa Sani Abba Aliyu da Farfesa Sa’idu babura Ahmad da Farfesa Nkem Okoh da kuma Farfesa Inuwa Umar Buratai.
Shugaban Taron shi ne Jakadan Najeriya a kasashen Masar da Eritriya, Farfesa dandatti Abdulkadir. Mai Masaukin Baki a yayin taron shi ne Shugaban kungiyar Manazarta Adabain Gargajiya ta Najeriya, Dokta Bukar Usman OON, a yayin da Babban Mai Masaukin Baki shi ne Shugaban Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Yahuza Bello.
Shugabannin kungiyar Adabin Gargajiya sun bayyana cewa duk masanin da ke son gabatar da kasida a wurin taron, zai aika tsakure na takardar tasa, da ba zai gaza kalmomi 300 ba, tare da sunayensu da sunayen makarantun da suka fito. Za su kuma aika da lambarsu ta tarho da adireshinsu na E-mail zuwa ga [email protected]