Taron kungiyar Muryar Talaka a Gusau ya yi armashi
A Ranar Juma’ar da ta gabata ce, wato16 ga wannan watan, memobin kngiyar Muryar Talaka suka gudanar da babban taronta da ta saba gudanarwa a kowace shekara, a garin Gusau na Jihar Zamfara. Ita dai kungiyar, wacce aka kirkire a shekarun baya ta tattara membobi ne daga sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma wadanda […]
A Ranar Juma’ar da ta gabata ce, wato16 ga wannan watan, memobin kngiyar Muryar Talaka suka gudanar da babban taronta da ta saba gudanarwa a kowace shekara, a garin Gusau na Jihar Zamfara.
Ita dai kungiyar, wacce aka kirkire a shekarun baya ta tattara membobi ne daga sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma wadanda suka shahara wajen saurare da yin sharhi ta kafafen watsa labarai, musamman ma rediyo.
Taken wannan taro, wanda shi ne irinsa karo na hudu shi ne: ‘Dimokuradiyya a Najeriya: kalubale, Fata da Mafita.’ Taron ya samu halartar dimbin jama’a, hadi da Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Muhammad Wakkala, wanda yana daya daga cikin iyayen wannan kungiya ta Muryar Talaka kuma shi ne mai masaukin baki.
Tun kafin taron, Babban Sakataren kungiyar na kasa, Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina ya shaida wa manema labarai cewa, taron wannan karon zai maida hankali ne a kan matsalolin da suka shafi dimokuradiyya, musamman saboda yadda ’yan Najeriya suka kasa fahimtar abin da ake nufi da ita kanta dimokuradiyya; inda kowa ke fassara ta bisa son zuciyarsa kawai.
A ranar farko, wacce ta kasance Juma’a, shugabanni da membobin kungiyar sun kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Dokta Muhammad Kabir danbaba. Tawagar, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Zaidu Bala kofa Sabuwa Birnin Kebbi da shugaban kungiyar Rundunar Adalci Ta kasa, Alhaji Abdulkarim dayyabu da Kwamared Ahmad Muhammad Bunza da sauran membobin kungiyar ne suka rufa masa baya.
A Jawabin shugaba Zaidu, ya ce sun ziyarci fadar ce domin mai martaba ya sanya masu albarka, ya kuma kara yi masu huduba da ya saba yi masu a matsayin uba.
Mai martaba sarki ya tunatar da membobi da shugabannin kungiya cewa lallai su sani suna dauke da nauyi mai girma, musamman in aka yi la’akari da sunan kungiyar. Ya kuma shawarce su da su zama masu ladabi da biyayya da girmama doka da oda. A ta bakinsa: “Kada ku karaya, kada ku gaji, ku ci gaba da ba da gudunmuwa domin kasarmu ta ci gaba.”
Shi ma shugaban kungiyar Rundunar Adalci Ta kasa kuma uba a kungiyar Muryar Talaka ta kasa, Alhaji Abdulkarim dayyabu, ya bayyana farin cikinsa na sake samun damar halartar garin taron kungiyar a Gusau. Ya ce shi ma dan Gusau ne, domin ya taba yin aikin kamfani a garin.
A dai ranar ta Juma’a da dare, kungiyar ta shirya wa ’ya’yanta liyafar cin abincin dare da kuma gasar Kacici-Kacici. An fara liyafar ne da misalin karfe goma da rabi na dare kuma shugaban kungiyar Muryar Talaka, reshen Jihar Zamfara, Kwamared Hafizu Balarabe Gusau ne ya yi jawabin maraba da baki. Ya kuma jinjina wa membobin kungiyar, wadanda suka fito daga jihohi daban-daban. Daga karshe ya yi fatan alheri tare da cewa Allah Ya sa a yi taro lafiya a watse lafiya. Sai dai a gasar Kacici-Kacici, Arewa maso Yamma ce ta lashe, inda ta yi nasara kan Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya. Tambayoyin sun shafi al’amuran yau da kullum game da kafafen watsa labarai da sauransu.
kungiyar Muryar Talaka dai an kafa ta domin wayar da kawunan al’umma kuma kungiya ce da membobinta kan tura sakonni zuwa kafafen watsa labarai na gida da na waje, ciki har da jaridar Aminiya.
Duk da cewa kungiyar ta fuskanci wasu matsaloli na cikin gida amma har yanzu tana daya daga cikin kungiyoyi masu a kima a Najeriya.
An kafa kungiyar ne a shekarar 2008 kuma ta gudanar da taruka daban-daban, ciki harda da taron da ta yi a Kano a 2010 da Kaduna a 2011 da Sakkwato a 2013 da kuma gudanar da babban zaben shugabanninta da ta gudanar a Katsina a 2013. Yanzu wannan taron shi ne karo na hudu.
A Ranar Asabar, 17 ga wata ita ce ranar da aka gabatar da
kasidu, inda masana da suka hada da Dokta Aliyu Muhammad Muri na Jami’ar Umaru Musa ’Yar-aduwa Katsina da Dokta Salisu Sadi Tsafe da Kwamared Ahmad Bunza da Alhaji Abdulkarim dayyabu. Kuma dukkanin kasidun sun ta’allaka ne a kan Dimokuradiyya da zaben da ke tafe na bana.
An bai wa mahalarta taron damar yin tambayoyi da sharhi. An dai kammala taron lafiya, sai dai kalubalen da aka fuskanta lokacin wannan taro sun hdda da kurarren lokaci da aka bai wa membobi. Wasu na ganin kamar ba a yi masu daidai ba. Amma duk da haka za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, tunda an yi lafiya an kammala lafiya kuma kowa ya kama hanyar komawa gida.