‘Taron Miyetti-Allah da gwamnoni ya haifar da da mai ido’

An dai shirya taron ne da nufin lalubo bakin zaren matsalar da Fulani suka tsinci kansu a Kudu maso Yamma

‘Taron Miyetti-Allah da gwamnoni ya haifar da da mai ido’

Wasu gwamnonin Kudu Maso Yamma da na Arewa yayin taron tattaunawa da kungiyar Miyetti-Allah

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Kasa ta cimma yarjejeniyar daina kiwo da daddare, yin amfani da kananan yara wurin kiwon da kuma tsallake shingen filayen da ba su da hurumi.

An cimma matsayar ne a karshen tattaunawar da kungiyar ta yi da Kungiyar Gwamnonin Najeriya wanda shugabansu, kuma Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya jagoranta a birnin Akure ranar Litinin.

Taron dai ya kuma sami halartar gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi da Ekiti da Osun da Oyo da kuma Ondo.

An dai shirya taron ne da nufin lalubo bakin zaren matsalar kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma tashin-tashinar da aka samu tsakanin manoma da makiyaya da harin da aka kaiwa wasu Fulani a jihar Oyo a kwanan nan.

Batutuwan da taron ya amince da su

Daga cikin batutuwan da aka amince da su akwai batun ci gaba da mutunta juna da kuma kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya; kalubalen tsaro matsala ce da ta shafi kasar baki daya ba wani sashe nata ba; an yi wa kalaman Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu kan makiya mummunar fahimta.

Taron ya kuma amince a hada karfi da karfe da Miyetti-Allah wajen yaki da aikata laifuka ba tare da an kori kowanne mutum daga kowanne sashe na Najeriya ba.

Sauran batutuwan da taron ya amince da su sun hada da hana kiwo da daddare ko yin amfani da kananan yara wajen kiwon ko kuma tsallake filayen da ba a halasta kiwo a cikinsu ba.

Miyetti-Allah ta kuma ce ta amince da duk wani mataki da za a dauka domin kawo zaman lafiya tare da yin alkawarin ba jami’an tsaro duk irin hadin kan da suke bukata wajen yaki da bata gari, ko daga wacce kabila suka fito.

Gwamnonin sun kuma yi alkawarin bullo da hanyoyin kiwo na zamani ta hanyar tsugunar da dabbobin a wuri daya don su daina gararanba.

Dole makiyaya su yi rijista – Akeredolu

Tun da farko dai sai da Gwamna Akeredolu ya dage cewa dole sai wadanda suke zaune a cikin dazukan jihar ba bisa ka’ida ba sun yi rijista da Gwamnatin Jihar kamar yadda takwarorinsu manona suka yi.

Ya ce ya zuwa yanzu, sama da manoma 70,000 ne suka yi rijista da gwamnati, yana mai cewa ta hanyar rijistar ne kawai za a fitar da baragurbi daga cikinsu.

Shi kuwa Gwaman Fayemi cewa ya yi matsalar ba wai yankinsu kawai ta shafa ba, har da dukkan sassan kasa.

Sai dai ya zargi kafafen watsa labarai da rura wutar rikicin inda ya ce sai an hada hannu waje daya muddin ana son kawo karshen matsalar tsaron.

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara

Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama

Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano