Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe
Wasu ne kawai ke da haushin Izala suke ganin tunda ita ta shirya taron, to ga dama ta samu da za su ɓata mata suna.
![Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/Quran.jpg)
Babban taron Alkur’ani na farko a Nijeriya da za a yi a Abuja na daga cikin batutuwa da suka ɗaukar hankali a ’yan kwanakin nan.
Yanzu bai wuce makonni biyu a gudanar da taron a ranar 22 ga watan Fabrairun da muke ciki ba, inda za a tara mahaddata Al-Kur’ani daga sassan Nijeriya.
- Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?
- Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda
Sai dai har yanzu ana ta diga ayar tambaya kan tushen taron da masu dauki nauyin mutum 30,000, mahaddata da masu zayyanar kalmomin Al-Kur’ani.
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), wadda aka fi sani da Izala, ce ke jagorantar shirya taron, amma ta ce kai-tsaye ba za a ayyana sunan mai ɗaukar nauyinsa ba, duk da cewa ba a san nawa gudanar da taron zai ci ba, haka ma yawan mutanen da suka yi rijista.
Sai dai kuma malaman Izala da dama na zargin taron wanda ake kira ‘Qur’anic Convention’ a Ingilishi, wani yunkurin ne amfani da addini don cimma wata manufar siyasa.
Muna da ƙarfin ɗaukar nauyinsa — Sheikh Bala Lau
Amma Shugaban JIBWIS na Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce babu bukatar kananan maganganu domin ko masallatan da ke karkashin kungiyar za su iya kaukar nauuyin taron.
Ya ce “Muna da masallatai sama da 15,000 a Nijeriya, ka ƙaddara idan muka ce kowane masallaci ya ba mu tallaffin N10,000 a kowane sati, nawa za mu tara?
“Kuma akwai jama’ar Musulmi da su ma a shirye suke su ba da gudummuwa saboda Allah musmaman ga irin wannan taro.”
Asalin taron
Wasu rahotanni sun nuna cewa Shugaban Kamfanin mai na Kasa (NNPC), Malam Mele Kyari, ne ya fara kawo tunanin yin taron, kamar yadda Shugaban Majalisar Malaman JIBWIS, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana, inda ya kara da cewa har wasu kungoyin Musulunci ma suna cikin wannan tsari.
Ya ce, “Duk wanda ya san Mele Kyari ya san mutumin kirki ne, kuma ya fito daga gidan mutunci, babu yadda za a yi wannan abu a siyasantar da shi.
“Burinsa bai wuce ganin ya kafa wani abu da zai zama gadon gidansu ba, domin shi ma almajirin Al-Kur’ani ne. Muna addu’a Allah Ya masa albarka da wannan tunani.” Jalo Jalingo ya bayyana haka ne a wani taron lacca da JIBWIS ta kira domin kore shakku ga masu zargin amfani da su domin cimma manufar siyasa.
Mun tuntuɓi Jami’in Hulda da Jama’a na NNPC, Femi Soneye, domin jin matsayar shugaban kamfanin a taro, amma ya shaida mana cewa Mele Kyari ba shi da alaka da taron.
“Duk abin da ya shafi addini, idan zai yi shi, yakan yi ne bisa ra’ayin kansa, amma in dai a kan wannan batu ne, ba shi da wata alaka da wadannan kungiyoyi” in ji Soneye.
Duk da haka wasu ke ganin malaman sun kasa kawo kwararan dalilai don kare taron, inda wasu ke kallon sa matsayin bidi’a da malaman Izalar ke yaka, amma suuka bige kirkiro wata.
Yadda taron ya raba kan malamai
Tun da JIBWIS ta sanar da shirya taron ake ta kace-na-ce tsakanin malamai a Arewacin Nijeriya, inda akasari ke nuna damuwarsu kan ingancinsa a Musulunci da kuma wanda zai dauki nauyisa, musamman yadda ake alakanta shi da siyasa.
Amma jagororin taron sun nesanta shi da siyasa — cewa manufarsa ita ce hada kan Musulmi da kuma nuna mu’ujizar Al-kur’ani tare da yi wa kasa addu’a.
Sheikh Bala Lau ya ce taron zai gudana ne karkashin kulawar Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci wadda Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ke jagoranta.
Amma wani abin da ya kara jan hankula shi ne zargin da Shugaban Majalisar Malaman Izala ta Izala Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi game da nagartar masu shirya taron da kuma matsayinsa Musulunci.
Sheikh Jingir, wanda ya sha bugun kirji kan alakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya nesanta shugaban kasan da da taron.
A wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta, Sheikh Jingir ya ce: “Na san ba Tinubu zai ba su wannan aikin ba. Muna zargin suna son yin amfani da Al-Kur’ani ne wajen yin tsafi da sabon Allah.”
Yadda lamarin ya faro
A ranar 14 ga watan Junairu, 2025, Sheikh Bala Lau ya bayyana aniyarsu ta tara akalla mmahaddata da marubuta marubuta Al-Kur’ani 30,000 a fadin Nijeriya a a Abuja.
Bayan sanarwar ne wani mai yin bidiyoyin barkwanci, Bello Galadanci (Dan Bello) ya yi zargin cewa za a tara mutane ne da sunan Al-Kur’ani domin yi wa Shugaba Tinubu yakin neman zaben 2027.
Zargin nasa ne ya haddasa zazzafar muhawara tsakanin masu shirya taron da wasu malamai, wadanda suka bukaci a soke shi.
Yawancinsu irin su Dakta Ahmad Gumi da Sheikh Ibrahim Khalil da Dakta Sani Umar Rijiyar Lemu da Sheikh Abubakar Salihu Zariya, sun kafa hujja da wasu muhimman abubuwa guda uku.
Na farko shi ne kalmar turanci ta ‘Festival’ da aka yi amfani da ita ta wajen siffanta taron.
A ra’ayinsa, wani malamin Darikar Tijjaniya, Sheikh Muhammad Auwal Sharif Zariya, ya ce kalmar na nuna taron sharholiya ne.
Wani malamin Izala, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, ya ce yana ganin kimar Sheikh Bala Lau amma duk da haka ba sa goyon bayan taron saboda ba shi da gurbi a Sunnah.
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce amfani kalamar “festival” zai sa wau su fahimce shi a matsayin taron sheke aya.
Duk da cewa daga baya an sauya kalmar zuwa “convention”, wasu malaman sun nace a kan cewa yin taron da sunan Al-Kur’ani Bidi’a ce kuma suna zargin ana so a yi amfani da shi ne don cimma manufar siyasa.
A wata lacca ta Sheikh Muhammad Auwal Sharif Zariya, ya yi ikirarin samu labarin cewa an hana a gayyace su saboda an san da wuya su bayar da hadin kai.
Ya kuma lissafo wasu malamai tara da ake ganin za su yi tutsu, wadanda aka haramta wa gayyatar.
Ya yi zargin wadanda suka halarci taron “za a ba su Naira 50,000 kowannensu ko kuma makamancin haka”
Sai dai tuni Sheikh Kabiru Haruna Gombe wanda shi ne Sakataren Kungiyar JIBWIS na Kasa ya mayar da martani da cewa wadanda Sheikh Shari ya ambata tare da su ake gudanar da komai har ya nuna daya daga cikinsu a wani bidiyon da suka gudanar a wajen lacca.
Ya ce “’Yan siyasa sun dade suna amfani da malamai wajen cimma muradunsu, kuma ya kamata malami su yi hankali su kula zuwa yanzu,” amma ya ce kai-tsaye ba za a ce taron haramun ba ne, amma wasa da sunan Al-Kur’ani ne.
Shi ma Farfesa Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya ce taron salon bidi’a ne shi da ire-irensa domin ba su da gurbi a Musulunci da sunnah.
Hakazalika Dakta Ahmad Gumi, a yayin karatu a majalisinsa da ke Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya ce taron ya ci karo da koyarwar Musulunci.
Ya yi zargin an kwafo shi ne daga wasu kasashe, aka yanke shawarar amfani da malaman Izala domin cimma wata manufa.
Gumi ya shawarci masu taron su maida hankali wajen koyar da al’umma yadda za su yi ibada da gane Musulunci yadda ya kamata maimakon irin wadannan taruka, domin, “Yanzu ba zamanin da za a ce a rika kwaikwayon wasu ba ne, wannan abin bidi’a ne, kuma ba ya cikin addinin Musulunci.
“Mun san cewa Kur’ani ba ya bukatar wani biki, kullum muna karanta shi.”
Tijjaniyya da Kadiriyya sun yi maraba da shi
Yayin da taron ya raba kawunan malaman Izala, su kuwa malaman Darikar Tijjaniya da Dadiriyya tuni suka yi kira ga almajiransu su shiga ciki a dama da su.
A cikin wani bidiyo, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, babban dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda jigo ne a Darikar Tijjaniya yana shaida wa mabiyansu cewa taron abin sam barka ne kuma “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa muna maraba da taron Alkur’ani da za a yi a Abuja. Kuma za mu yi wa kasar nan addu’a.
Har ila yau, Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi in shaida wa mabiya cewa muna goyon bayan wannan taron domin duk wani abu da ya shafi Al-Kur’ani muna maraba da.”
Shi ma Shugaban Darikar Kadiriyya a Afirka, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, a cikin wani bidiyo ya buƙaci magoya bayansa su yi rijistar halartar taron domin suna goyon baya.
Ba shi alaƙa da siyasa — JIBWIS
Shugabannin JIBWIS dai sun dage cewa shi da kowace irin alaka da siyasa ballanta har gwamnati ta dauki nauyinsa domin amfani da addini wajen a cimma nasarar zaben 2027.
A jawabinsa a laccar da suka shirya a hedikwatar JIBWIS da ke Abuja, Sheikh Abdullahi Bala ya ce ba su kadai suka yanke shawarar taron ba domin akwai kungiyoyin addini da dama a ciki irinsu Darikar Tijjaniya da Kadiriyya, amma dai malaman Izala ne suke jagorantar taron shi ya sa ake ganin hannunsu dumu-dumu wajen assasa shi.
Ya yi zargin cewa masu adawa da taron suna yi ne saboda ba su suke jagorantar shi ba, wasu kuma da ma can suna jin haushinsa ne shi ya sa suke surutai.
Ya kuma yi zargin cewa wasu malaman suna ta zuga gwamnati ta soke taron.
A jawabinsa, bayan taron laccar, ya ce “Al’ummar Musulmi za su iya daukar nauyin wannan taro ba tare da sa hannun gwmanati ba, ko mu a kungiyar Izala muna da karfin da za mu iya daukar nayin.”
Ya ce dalilinsu na gayyatar Shugaba Tinubu shi ne a matsayin shi na shugaban kasa ya zama wajibi ya sanya wa taron albarka, kuma hakan zai ba su dama su gaya wa gwamnati inda ta yi kuskure domin ta gyara.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce “Wallahi idan har batun siyasa za a yi a wajen wannan taron, ko yi wa wani dan siyasa kamfen ba zan halarce shi ba, da ni da Shugaba (Bala Lau)”.
Ya ce ba Izala ce kadai ke daukar nauyin taron ba, ya kuma soki malaman da ke neman kawar da hankalin al’umma kan ingancinsa da kalamai marasa tushe.
Ya ce, “Wasu ne kawai ke da haushin Izala suke ganin tunda ita ta shirya taron, to ga dama ta samu da za su ɓata mata suna. Kuma ina rantsuwa da Allah wannan taron ba shi da wata alaka ta siyasa,” in ji Kabiru Gombe.
A jawabin Sheikh Jalo Jalingo, ya ce irin wannnan taron da an sha yin shi a ƙasashe irinsu Saudiyya da Senegal har ma da Birtaniya, kuma zai kara haɗa kan Musulmi mahaddata Al-ƙur’ani a faɗin ƙasar da ma Afirka.