Taron Shugaba Jonathan da gwamnonin sabuwar PDP ya gagara
Taron sulhu tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da gwamnonin sabuwar PDP bakwai ya gagara, bayan da aka dage zaman sulhun a ranar Litinin da ta gabata sai bayan dawowa daga aikin Hajji da ziyarar Kiristoci a Urshalima.Gwamnoni hudu daga cikin gwamnoni ‘masu tawaye’ bakwai ne suka halarci zaman da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa a […]
Taron sulhu tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da gwamnonin sabuwar PDP bakwai ya gagara, bayan da aka dage zaman sulhun a ranar Litinin da ta gabata sai bayan dawowa daga aikin Hajji da ziyarar Kiristoci a Urshalima.
Gwamnoni hudu daga cikin gwamnoni ‘masu tawaye’ bakwai ne suka halarci zaman da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa a ranar wadanda suka hada da Mu’azu Babangida Aliyu (Neja) da Abdulfatahi Ahmed (Kwara) da Rotimi Amaechi (Ribas) da Rabi’u Musa Kwankwaso (Kano).
Sauran wadanda suka halarci taron wanda aka fara da karfe 12:00 na rana ya kare da karfe 1:30 na rana sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Mohammed Namadi Sambo da Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP Cif Tony Anenih da gwamonin da suka hada da Idris Wada (Kogi) da Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da Ibrahim Shema (Katsina) da Liyel Imoke (Kuros Riba).
Lokacin da yake karanta takardar bayan taro Gwamna Imoke ya ce, Gwamna Lamido da Nyako da kuma Wamako ba su halarci taron ba ne saboda sun tafi aikin Hajji. Don haka an yanke shawarar sake kiran taron bayan kammala aikin Hajjin bana da kuma ziyarar mabiya addinin Kirista.
Gwamna Imoke ya kara da cewa taron ya amince a dauki matakan aiwatar da matsayar da aka cimma a tarukan baya. Ya ce, “Sakamakon taron da aka yi ranar 15 ga Satumba, kuma bisa yarjejeniyar da aka cimma a taron, gwamnonin sun gana da Shugaban kasa da Mataimakinsa da Shugaban Kwamitin Dattawa (na PDP) tare da sakon rashin halarta daga gwamnonin Jigawa da Sakkwato da Adamawa wadanda suka tafi aikin Hajji. Taron ya gudana cikin annashuwa kuma ya yanke shawarar cewa duk da abubuwa marasa dadi da suka biyo bayan taron 15 ga Satumba, bangarorin za su ci gaba da aiki da yarjejeniyoyin da aka cimma. Kuma taron ya amince ya dauki matakan aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a tarukan baya.”
Ya kara da cewa, “Bisa wannan dalili an yanke shawarar cewa za a sake kiran taro da zarar Musulmi sun dawo daga aikin Hajjin bana, su ma Kiristoci sun dawo daga aikin ziyara.”