Taron Tattalin Arziki na Duniya: Makarantu 500 na Arewa za su amfana
A makon jiya ne aka kammala taron Tattalin Arziki na Duniya a kan Afirka karo na 24 a Najeriya. Daraktan kungiyar Tattali Arziki na Duniya a Afirka Elsie S. Kanza ya ce sakamakon taron ya nuna za a zuba hannun jarin Naira Tiriliyan 9.2 a Afirka.“Sakamakon taron ya nuna a yanzu Afirka za ta amfana […]

A makon jiya ne aka kammala taron Tattalin Arziki na Duniya a kan Afirka karo na 24 a Najeriya.
Daraktan kungiyar Tattali Arziki na Duniya a Afirka Elsie S. Kanza ya ce sakamakon taron ya nuna za a zuba hannun jarin Naira Tiriliyan 9.2 a Afirka.
“Sakamakon taron ya nuna a yanzu Afirka za ta amfana da hannun jari na Naira biliyan 59 (daidai da Naira Tiriliyan 9.2), wanda hakan zai samar da guraben ayyuka kamar dubu 230, zai kuma taimaka wa makaratun areacin Najeriya kimanin 500.’ Inji Kanza.
Ya ce ’yan kasuwani daga sassan duniya da kuma gwamnatocin kasashen duniya ne za su zuba wannan hannun jarin a Afrika don bunkasa tattalin arzikin Afirka.
A cikin ’yan kasuwar da za su zuba hannun jarinsu akwai Alhaji Aliko Dangote, wanda ya yi alkawarin zai zuba hannun jarin Dala biliyan 16 a Najeriya, zai kuma zuba wannan kudin a bangaren kayayyakin da ake samu daga mai.
kasar China kuma za ta zuba jarin Dala biliyan 12, inda sauran ’yan kasuwa daga Najeriya za su ba da gudunmuwar Dala biliyan 20 don taimaka wa Shirin Bunkasa Makarantu.
Wannan shirin na hadaka ne tsakanin gwamnati da ’yan jarida da jama’a da matasa da iyaye da kuma malamai don bunkasa makaratu 500 a Arewacin Najeriya.