Taron tattalin arzikin duniya lokacin rikici
Duk da halin rudani da matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita, ta karbi bakunci ’yan kasashen waje da wakilan Afirka a taron tattalin arzikin duniya (WEF) da ta shirya. Wannan al’amari dai na da matukar wahala hada al’amura a cikin mawuyacin hali. A daidai lokacin da ake gudanar da taron tattalin arzikin duniya […]
Duk da halin rudani da matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita, ta karbi bakunci ’yan kasashen waje da wakilan Afirka a taron tattalin arzikin duniya (WEF) da ta shirya. Wannan al’amari dai na da matukar wahala hada al’amura a cikin mawuyacin hali. A daidai lokacin da ake gudanar da taron tattalin arzikin duniya a Abuja, mai taken “bunkasar da ta hade kowa, don samar da ayyukan yi,” ga kuma taron duniya mai taken “A dawo mana da ’yan matanmu, don a nusar da duniya halin da ake ciki game ’yan matan sakandare fiye da 200 da aka sace a Chibok da ke Jihar Barno, inda maharan ’yan bindiga ke tsare da su kimanin kwana 25 da suka wuce, al’amarin yana da wuya a san wane sakon ya fi jan hankalin ’yan Najeriya. Duk da haka, bai kamata a yi watsi da muhimmancin taron tattalin arziki na kwana uku ba.
Wannan taron tattalin arziki (WEF) na 25, zai tattaro shugabannin kasashe 13 da jiga-jigan mutane fiye da dubu da suka goge a harkokin kasuwanci da siyasa da cibiyoyin bunkasa ci gaban al’umma da kungiyoyin fafutikar hakkin dan Adam, wadanda za su tattauna kan hanyoyin aiwatar da sauye-sauye, ta yadda wannan nahiyar za ta samu bunkasar tattalin arziki wanda zai yi tasirin kyautata rayuwar miliyoyin al’umma da ke cikin wahala.
Don samun ci gaba mai ma’ana da dorewa, kowane tsarin tattalin arziki dole ne a tafiyar da shi kan tafarkin samar da ayyukan yi da yaki da fatara da talauci da cike gibin da ke tsakanin al’umma na rashin daidaito, wanda ke ruruta wutar tashe-tashen hankula; Hadin kai tsakanin kasashen yankin da gyara tsare-tsaren kasa da hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin bincike na Afirka das aka jari wajen samar da kayayyakin kyautata jin dadin rayuwa da bayar da horon kwarewa ga al’umma da tabbatar da tsaro, ta yadda za a yi amfani da dimbin albarkatun Afirka don samun tabbacin bunkasar tattalina arzikin Afirka tare da tasirin kyautata rayuwa da samun walwala.
Ganin cewa kasar nan ta shafe shekara 38 wajen shirya tarurrukan tattaunawa don yi wa tattalina arziki garambawul da tsare-tsaren saka jari, burin da ake son cimmawa da wannan gagarumin taron duniya, shi ne, ya yi tasiri wajen tallafa wa Najeriya, kan tattalin arzikinta da aka tabbatar da bunkasarsa, don ya kauce wa biyan bukatun wasu ’yan tsiraru, sannan ya shigo da wadanda ba a damawa da su, musamman matasa.
Yin wannan taro a daidai lokacin da ake fama da kururuwar satar mata ’yan makaranta, wannan taro na tattalin arzikin duniya (WEF), ya kamata ya zama matashiya kan hadarin da ke tattare da tsarin bunkasa tattali da ake tafiya a kai, bisa la’akari da yawan fatara da talauci da lalacewar hanyoyi da sauran kayan more jin dadin rayuwa da yawan rashin aikin yi. Masu fasalta wa Najeriya tsare-tsarenta, ya kamata su fadada tunaninsu, maimamkon su rika zuwa gaban taron tattalin arzikin duniya suna almubazzaranci, kamata ya yi su duba gazawar gwamnatin kasa, ta yadda za su fito da hanyoyin gyara. Bai kamata a kawar da kai daga kan cin hanci da rashawa da yawan fatara da talauci, matukar ana son samar da ci gaba mai dorewa da makoma mai alfanu.
Yayin da ake ta kwakwazon karuwar kimar tattalin arzikin Najeriya, a matsayin mafi karfi a fadin nahiyar Afirka, mahukuntan Najeriya su dauki darasi kan cewa kimanin biyu bisa uku na al’ummar kasar na fama da talauci, har ta kai ga suna rayuwa a kan kasa da Dala biyu. karancin abin da daidaikun ’yan kasa ke samu bai wuce Dala dubu biyu da 688, sabanin ’yan Afirka ta Kudu da ke samun Dala dubu takwas da 342, duk da cewa Najeriya na da dimbin hamshakan attajirai fiye da sauran kasashen Afirka. Baya ga kasar Sin, Najeriya ce kasa ta biyu da kasuwar manyan jiragen alfarma mallakar daidaikun mutane ke ci a duniya, inda masu dimbin dukiya ke kashe fiye da Naira tiriliyon (biliyan sau dubu) a kan jiragen alfarma cikin shekara biyar da suka wuce. Ya kamata a ce wannan wadata da suka samu an rabata a tsakanin al’umma, don ta ci gaba da yaduwa.
Sannan akwai bukatar ganin wannan gagarumin taro ya samar da mafita, wajen shawo kan matsalolin kayan more jin dadin rayuwa da suka ragwaggwabe, tare da matsanancin talauci, maimakon babatu da burga da ake ta yi. Alal misali, wutar lantarkin Najeriya sai faduwa da sauka take yi, daga karfin megawatt dubu uku zuwa hudu, duk da dimbin biliyoyin Dalar da aka kashe wajen gyaran wutar. Kwananan Najeriya ta sayar da kamfanoninta a karkashin shirin garambawul din gwamnati. Idan aka kwatanta Kamfanin Eskom na Afirka ta Kudu da ke samar da fiye da karfin megawatt dubu 45 ga kasar, wannan na nuni da cewa akwai bukatar a gano dalilan da suka haifar da koma baya, maimkon sayar da kamfanonin kawai.
Abin da kawai ba wai sai an yi ta nanatawa ba, shi ne biyan haraji ga masu hada-hadar kasuwanci na kasashen waje da na cikin gida, sannan a tabbatar suna yaki da cin hanci da rashawa, domin mafi aywan kamfanonin kasashen waje, suna bayar da toshiya don boye kudin da suka shigo wajensu ba bisa ka’ida ba. Dole ne hukumomin Najeriya su tabbatar da cewa, duk da suna bukatar jawo masu saka jari a Najeriya, akwai bukatar taron ya samar wa Najeriya muhimman fa’idojin da za ta karu da su.