Taron tsarin mulki ko sharholiyar shan shayi
Sa’ilin da Shugaba Jonathan ya fayyacewa ‘yan Najeriya aniyarsa ta shirya wani taron tattauna makoman kasar nan a ranar daya ga watan Oktoban bara, don magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da gwamnatocin da suka shude suka kasa yi duk kuwa da kokartawar da suka yi ta irin wannan hanyar ‘yan Najriya sun fahimci […]
Sa’ilin da Shugaba Jonathan ya fayyacewa ‘yan Najeriya aniyarsa ta shirya wani taron tattauna makoman kasar nan a ranar daya ga watan Oktoban bara, don magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da gwamnatocin da suka shude suka kasa yi duk kuwa da kokartawar da suka yi ta irin wannan hanyar ‘yan Najriya sun fahimci cewa tsuguni-tashi ba ta kare ba game da haka. Talakawa na mamakin yadda za a yi haka ganin cewa akwai majalisar tarayya ta kasa wacce babu wata harkar gyaran sha’anin siyasa ko tsara wata sabuwar dokar gudanar da al’amuran mulki za su gagare ta. Shi ya sa jama’a ke ta mamakin hikima ko basirar Shugaba Jonathan ya yi da ya furta kudurinsa na kiran wannan taro a daidai lokacin da majalisar tarayyar kasar ke tsakiyar aiwatar da shirinta na yin gyararraki ga kundin tsarin mulki don a kawar da abubuwan da ke sawa ganin cewa bai dace da tafarkin dimokuradiyya ba domin kuwa sojoji ne suka tsara shi bisa son zukatansu.
To amma bayan Shugaba Jonathan ya kafa kwamitin mutum goma ha uku a karkashin Sanata Femi Okourounmu don shawartarsa game da sunan da za a kira taron da kuma tsara ababuwan da za a tattauna sai ‘yan Najeriya da yawa suka fara zumbura baki, suna guna-guni ganin yadda aka gaggauta yin haka ba tare da yin cikakken tunani ko la’akari da halin da tarurrukan baya suka shiga ba, da kuma yadda batun gyararrakin ya ci tura. Tun kafin akai ko ina sai ga shi nan ana ta tsattsagar manufar kafa wanan kwamitin, suna cewa hanyar da aka bi don kiran taron ba ta dace ba, kuma hakan na iya kawo cikas game da gudanar da shi, ko kuma ma hakan na iya gurgunta shi, a kasa kai ga biyan bukata. A cewar mutanen Kudancin kasar nan wadanda suka fi zakewa game da haka shi ne a tsara taron da ba wata hukuma ko wani mahaluki da zai canja sakamakonsa wanda shi ne kuma zai zamanto kundin tsarin mulkin kasar da za a ci gaba da amfani da shi, amma ba taron je-ka-na yi-ka ba irin na Jonathan.
Ganin yadda jama’a ke ta kumfar baki wajen tozarta makasudin kiran wanan taron don rashin fahimtar alkiblarsa da kuma burin da ake so a cimma, sai Shugaba Jonathan ya ce za a mika sakamakon taron ga majalisar tarayya don hakan ya kasance gudummawar gwamnati ga kokarin da majalisar ke yi a halin yanzu na yin gyararraki ga kundin tsarin mulki bisa shawarwarin da gwamnatin ta aike mata da su da kanta. To idan kuwa haka ne ina amfanin sake kiran wani taron da za a kara aika wa majalisa da sakamakonsa a matsayin shawarwarin yin gyaran da take gudanarwa? Wannan dai, a wajen talakawa da yawa, wani mataki ne don a kawar da hankulan jama’a daga kulle-kullen gwamnati ta yadda za a yaudare su. Wasu kuma cewa suke yi Shugaba Jonathan na bin ra’ayin wasu a ciki da wajen kasar nan don zartar da muguwar manufarsu ta hargitsa wa kasar lissafi.
Ana dara ne sai ga dare ya yi. Jama’a na nuna rashin amincewarsu da wannan taro don rashin kan-gadon masu tsara shi, wanda aka kashe sama da Naira miliyan dubu shida daga 2007-2011 don share fagen afkuwarsa da kuma da kuma wasu miliyan dubu bakwai da za a batar cikin watanni uku masu zuwa don gudanar da shi, sai kuma ga Shugaba Jonathan ya hau turbar jefa taron cikin rijiya mai gaba dari, domin kuwa ya ce wakilan da za su halarci taron har guda 492 ba zabensu za a yi ba kaman yadda aka saba yi a lokutan da ake kokarin yin haka, nannada su za a yi, kuma kansa zai zabi guda 43 sauran kuma kungiyoyi da jam’iyyun siyasa da kuma sauran hukumomi ne za su firfitar da su daidai da adadin yawan wakilan da ya kayyade masu. Hakan ya saba ka’idar dimokuradiyya kuma zai bayar da daman zartar da kudurorin da za a zartar cikin sauki daga kashi saba’in cikin dari na yawan wakilan da za a zazzabo don goyon bayan manufofin gwamnatin Shugaba Jonathan.
Amma duk da haka nan akwai wata babbar tambaya game da wannan taron da jama’a ke gani bai wajabta ba. Shin kundin tsarin mulkin da ake aiki ne da shi ke da kaifi ko masu aiwatar da shi ne ba su san makamarsa ba? Idan har an yi wani sabo fil mala’iku ne daga sama za su sauko don taimakon Shugaba Jonathan aiwatar da shi, ko kuwa ‘yan siyasan asali ne da ke biye son zukatansu maimakamon aikin da doka da oda? Shin ba wadancan shugabanni da ‘yan siyasan da suka hana dukkan tsare-tsaren mulki aramashi ne ba a kasar nan za su sake taruwa don kago wani sabo? To idan har Sarkin Fawa ya mutu ba a bizne shi da wukarsa ba, to dabbobi ba su tsira ba, domin kuwa wukar za ta koma hannun magajinsa.