Taron ’yan Arewa na Bond FM ya tashi da korafi
A karshen makon da ya gabata ne gidan rediyon Bond FM ya shirya taron biki na ’yan Arewa, wanda yabar baya da kura, a sakamakon korafe-korafen da jama’ ar da mahalarta bikin suka yi ta yi.A cewar mataimakin shugaban jam’iyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya kadu kwarai da aka kai masa goron gayyata, […]
A karshen makon da ya gabata ne gidan rediyon Bond FM ya shirya taron biki na ’yan Arewa, wanda yabar baya da kura, a sakamakon korafe-korafen da jama’ ar da mahalarta bikin suka yi ta yi.
A cewar mataimakin shugaban jam’iyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya kadu kwarai da aka kai masa goron gayyata, aka ce masa taron na ’yan Arewa ne. “Nan take na tambayi cewa na ’yan Arewa kadai ne ba sauran kabilu? Sai aka sanar da ni cewa, ai an yi na Yarabawa da na Ibo a kwanakin baya a lokuta daban-daban. Ka ga da hade dukkanin manyan kabilun kasar aka yi bikin nasu a tare da ya fi armashi, da kuma ya isar wa duniya sakon hadin kan al’ ummar kasar.” Inji Bode George.
Alhaji Bashir jara, wani dan jarida ne da ya halarci taron. Ya bayyana shi da abin sha’awa duba da yadda ya hado mutane daban-daban a wuri guda. Sai dai ya yi korafin gazawar wadanda suka shirya taron wajen samar da isassun na’urori masu kai sauti nesa tamkar yadda takwaranu Yarabawa suka yi.
Shugaban kungiyar matasan Arewa a cikin garin Legas, Alhaji Sani Zarewa ya shaida wa Aminiya cewa su 45 suka halarci taron bayan kowannensu ya biya Naira 500 kafin ya shiga sai dai yawancin ’yan kungiyar ba su samu wajen zama ba; haka suka yi ta tsayuwa cikin rana.
“Rashin tsarin taron ne ya sanya daidaikun ’yan sandan gaza tankwara taron mutanen, har sai da ya kai ga ’yan sandan na ta korar jama’a; suna bugun su, ha rta kai ga sun buga wa mahalartar taron barkonon tsohuwa. Abin da sam bai dace ba, sai dai daga baya an yi ta baiwa jama’a hakuri, ana cewa kuskure ’yan sandan suka yi suka, da suka buga barakonon tsohuwar da ya sanya jama’a hawaye. Muna fatan za su lura da kura-kuran da aka tafka domin yin gyara nan gaba,” inji shi.