Taron yi wa kasa addu’a ya bar baya da kura a Bauchi
Taron addu’ar zaman lafiya da wasu ke zargin na tazarcen Shugaba Jonathan ne da da aka gayyaci malamai 6000 daga ciki da wajen Najeriya da aka gudanar a Bauchi, ya bar baya da kura inda yawancin malaman da suka shiga karatun suka tafi suna guna-guni wasu na la’antar yadda aka sallame su.Malaman sun rika kukan […]

Taron addu’ar zaman lafiya da wasu ke zargin na tazarcen Shugaba Jonathan ne da da aka gayyaci malamai 6000 daga ciki da wajen Najeriya da aka gudanar a Bauchi, ya bar baya da kura inda yawancin malaman da suka shiga karatun suka tafi suna guna-guni wasu na la’antar yadda aka sallame su.
Malaman sun rika kukan cewa an gaza cika alkawarin ba su Naira dubu 10 zuwa dubu 50 a matsayin kudin sallama inda a karshe aka ba su Naira dubu dai-dai.
Wannan korafi na zagayawa a tsakanin masallatai da makarantun da malaman suka fito, inda wakilinmu ya ce an ji wasu malaman na Allah Ya isa a cikin lasifikoki suna cewa an zalunce su.
Babban Daraktan Ilimin Tsangaya na Jihar Bauchi Sayyadi Ali dahiru Usman Bauchi wanda shi ne jagoran addu’ar ya ce samun sabani game da biyan malaman ya sa wasu marasa kishi sun warwashe Alkur’ani sama da dubu daya da tabarmi da katifun da wasu ma aro su aka yi.
Sayyadi Ali ya ce ganin haka ya sa sauran Alkur’anan da suka rage a hannun malaman aka ce kowa ya rike a matsayin kudin sallama musamman ganin yadda ran almajiran ya baci.
Sayyadi Ali ya ce Shugaban kasa ne ya kira a yi taron yi wa kasa addu’a domin samun zaman lafiya. Kuma su ma Kiristoci an kira su an ba su kudin gudanar da wannan aiki na tara fastoci da mabiya sun yi. Don haka ya ce idan an kira Musulmi sun ki amincewa ba a kyauta ba. Amma batun a ce wai an shirya taron yi wa Goodluck Jonathan addu’a domin tazarce ne ba haka ba ne.
Sayyadi Ali ya ce lokacin da Gwamna Isa Yuguda ya je Abuja saboda gudun irin wadannan karairayi, bai karbo komai da sunan wannan aiki ba, cewa ya yi a bari gwamnatinsa za ta dauki nauyin komai kuma za a yi duk abin da ya dace.
Ya ce da aka ga aikin na cin kudin da ba a zata ba, sai Gwamna ya ce a rage wasu bukatu, aka ce wadanda suka fito daga wasu jihohi a ba su Naira dubu 10 wasu Naira dubu 15, wadanda suka fito daga jihar, ba sai an ba su komai ba, saboda suna cikin malamansa na tsangaya da ake ba su Naira dubu biyar duk wata.
Alaramma Shaya’u Abubakar Gwanki na cikin ’yan kwamitin da suka shirya addu’ar ya nuna rashin jin dadi kan abin da ya faru, ya ce kashi biyu cikin uku na wadanda aka samu matsala da su ba masu amsar tallafin gwamnati ba ne. Don haka ya roki Gwamna ya taimaka a biya kowa a huta.
Alaramma Muhammadu Mai Kankat cewa ya yi ba za su yafe abin da aka yi musu ba, har sai an biya su hakkokinsu, “Domin ba mun zo cin abinci ba ne, yadda Gwamna ke zaune a ofis ya yi aiki ya samu kudi, muma wannan shi ne aikinmu na neman abin da za mu ci, don haka ya kamata Gwamna da wadanda suka shirya taron su biya su hakkinsu,” inji shi.
Alaramma Abdulmumini kofar Nasarawa ya ce a karkashinsa mutum 50 aka sa ya tura wurin karatun kuma kowa ya dawo da wannan korafi. Don haka ya ba masu shirya taro shawarar su daina sa yarinta cikin harkar almajirai kuma su kasance masu bayyana gaskiya komai dacinta don magance irin wannan matsala a nan gaba.