Taronmu kan yaki da ta’addanci ya samu nasara –Sheikh Yakubu Musa
Aminiya: Mene ne makasudin shirya wannan taro?Sheikh Yakubu Musa: A’uzu billahi minash shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Da farko dai muna godiya ga Allah da Ya gwada mana aka yi wannan taro lafiya aka tashi lafiya, wannan dace ne daga wajen Allah. Najeriya kasa ce da mafiya rinjayen al’ummarta Musulmi ne haka kasashen da ke […]

Aminiya: Mene ne makasudin shirya wannan taro?
Sheikh Yakubu Musa: A’uzu billahi minash shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Da farko dai muna godiya ga Allah da Ya gwada mana aka yi wannan taro lafiya aka tashi lafiya, wannan dace ne daga wajen Allah. Najeriya kasa ce da mafiya rinjayen al’ummarta Musulmi ne haka kasashen da ke kewaye da ita. Wadannan kasashe da wasu kasashen Musulmi a mataki na duniya baki daya, sun samu kansu a cikin wani hali na jarrabawa sakamakon abin bakin ciki na rashin fahimta ko mummunar fahimta na wasu malamai da suka karkatar da dubbai ko miliyoyin matasanmu a nan Afirka da sauran kasashen Musulmi da sunan jihadi, ba tare da la’akari da kuma kiyaye ka’idoji na ayoyi da Sunnar Manzon Allah (SAW) suka yi bayani a kan abin da ya shafi jihadi ba. Suka kwashi matasa suka jefa su a cikin bala’i na ta’addanci. Wannan abin bakin ciki ne da bata Musulunci da lakaba masa wani al’amari. A Musulunci idan za ka shiga wajen jama’a kamar kasuwa, ba a son ka zare takobi ko daga mashi a sama kana tafiya, sai dai ka yi kasa da shi don kada ka nuna dan uwanka da makami. Musulunci addini ne na rahama yana kuma koyar da tausayawa ba ga Musulmi kawai ba, har ga wadanda ba Musulmi ba, ba ga mutum kadai ba har ga dabbobi. Amma a yau duniya na ganin Musulunci a matsayin addinin zubar da jini da rashin tausayi. To yakar wannan al’amari musamman a kawar da shi daga zukatan jama’a abu ne da gwamnatoci kadai musamman ma a tsarin demokoradiyya ba za su iya ba, wajibi ne ga kungiyoyin da ke da kishin addini su shigo ciki tare da nazarin irin gudunmawar da za su ba da domin a gudu tare a tsira tare. To daga cikin abubuwan da muka yi amfani da su domin fadakarwa a kan al’amarin, akwai huduba a masallatai da kuma wa’azuzzuka a wuraren karantarwa a masallatai da sauransu, haka matasa za su rika shiga lungu da sako don fadakarwa, da kafofin watsa labarai. To sai muka ga cewa wannan a matakin Najeriya ke nan ina ga sauran kasashe makwabta wadanda su ma sun samu kansu a cikin wannan al’amari. To a sakamakon haka sai mu ka yanke shawarar gayyatar shugabannin addinin Musulunci na wadannan kasashe, musamman malamai da limamai domin tattaunawa da su da kuma neman mafita.
Aminiya: Kamar wadanne kasashe ne suka halarci wannan taro?
Sheikh Yakubu Musa: Jigo a cikin kasashe da suka halarci wannan taro ita ce kasar Saudiyya inda mutum wajen sittin da wani abu suka halarci taron. Wannan ya hada da tawagar kungiyar Hadin kan Musulunci ta Duniya wato Rabidatul Alamil Islami ko World Islamic League a Turance, wadda babban jagoranta Sheikh Abdullahi Ibn Abdulmuhsin At-Turki ya jagoranta. Wannan kungiya ita ce uwar dukkan kungiyoyin Musulunci na Sunnah wadda kuma gwamnatocin kasashe na duniya suka sani a wajen mu’amala tare da wakilci a Majalisar dinkin Duniya. Akwai kuma kungiyoyin ’yan Afirka mazauna Saudiyya su ma sun turo wakilansu, ban da wannan a bangaren kasashen Turai mun samu wakilai daga Amurka da Ingila wadanda suka kunshi manyan limamansu da masu wa’azi. A nan Afirka akwai tawaga daga kasashen Libya da Sudan da Mali da Senegal da Kwaddibuwa da Ghana da Togo da Kamaru da Nijar da Chadi da Burkina Faso da Benin. Wasu kasashen wakilai ne kadai suka samu zuwa, wasu kuma har da mabiya da suka halarci wa’azin kasa-da-kasa da aka gudanasr daga baya. Tasirin wannan wakilci nasu shi ne al’ummar Musulmi sun fi sauraron malamai da limamansu fiye da gwamnatocin kasashensu. Makkah da Madina inda a can ne aka sauKar da Alkur’ani da kuma Hadisan nan, kololuwar shugabannin addininsu ita ce dai wannan kungiya ta Rabida. To wadannan malamai sun gabatar da kasidoji da fatawa a kan hukuncin wannan al’amari da kuma irin gudunmawa da malamai da limamai da gwamnatoci ya kamata su bayar a kai. Matsalar ta’addancin nan ta taso ne daga bangaren Saudiyya wanda ta yi amfani da irin wannan salo ta samu nasarar magance ta. To ana sa rai wadanda suka halarci wannan taro idan sun koma za su shirya irin wadannan kwasa-kwasai domin ilimantar da jama’arsu a kan abin da suka koya tare da koyar da wata jama’a horon da aka koyar da su.
Aminiya: A iya cewa kun samu nasarar cimma burin taron ke nan?
Sheikh Yakubu Musa: Alhamdulillahi hakika mun cimma nasara dari bisa dari domin duk abin da muka yi kirdado za mu samu na nasara, tsakani da Allah mun samu. Da farko mun yi fargaba ko watakila saboda irin hali da ake ciki na kukan abin hannu yanzu a kasar nan mu kuma ba kudin ne muke da shi ba a fuskanci gazawa. Amma cikin ikon Allah da ma an shirya taron ne saboda Shi, kuma Shi Mai iko ne a kan komai, dukiya taSa ce, zukatan mutane a hannunSa suke Yana juya su yadda Ya so, sai ga shi a cikin yardarSa an kammala wannan gagarumin taro ba tare da an samu wata matsala ba. Nasara ta farko da muka samu ita ce su kansu malaman da suka gabatar da lacca da su kansu manyan shugabannin a bangaren Musulmi duk sun halarta, saboda mun gayyaci har wadanda ba Musulmi ba kamar tsohon Shugaban kasa (Olusegun) Obasanjo da tsohon Shugaban Majalisar dinkin duniya, Kofi Anan, ba su samu zuwa ba amma sun turo wakilai. A cikin wadanda suka halarci taron a bangaren Musulmi, akwai Kamar Imam Majid, shahararren mai wa’azi ne a duniya an san shi Ba’amurke ne yana da babban masallaci a Amurka, ya samu halartar taron tare da abokansa. To halartar wadannan shugabanni da suka gabatar da lacca ita ce nasara ta farko da muka samu. Halartar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda shi ne babban bako nasara ce, halartar sauran manyan baki kamar sanatoci wajen sama da talatin ciki har da sanatoci Kiristoci goma da Shugaban Majalisarsu Abubakar Bukola Saraki nasara ce. Sannan shugaban majalisar ya je wajen rufe wa’azi, ya je Sallar Juma’a da Babban Sakataren Rabidatul Alamil Islami ya jagoranta a Masallacin kasa na Abuja. Gwamnoni tara sun zo, su kansu wadanda aka shirya wa bitar duk sun halarta har ma da kari. Kafofin watsa labarai na nan gida Najeriya kamar NTA da FRCN da tashoshin FM da kuma na waje kamar MANARA bangaren talabijin da rediyo da tashar talabijin ta Rabida duk sun watsa wannan al’amari kai-tsaye, ga kuma jaridu sun dauka, to wannan ba karamar nasara ba ce, nasara ce gagaruma.
Aminiya: A karshe wane sako za ka aika ga wadanda ba su samu damar halartar taron ba?
Sheikh Yakubu Musa: Akwai faya-faye da ake shiryawa a yanzu haka, insha Allahu nan ba da dadewa ba gidajen rediyo da talabijin na MANARA za su fara sakowa don amfanar duniya baki daya. Kuma mun umarci mahalarta taron musamman a matakin jihohi a nan Najeriya su shirya irin wannan taro tare da gayyatar dukkan Musulmi har ma da wadanda ba Musulmi ba da ke da kaykaywar mu’amala da jama’a su halarci taron, koda yake na ji wasu har sun fara yin suka a kan me ya sa aka gayyaci mata a kan al’amarin. Sun mance da tarihin Musulunci Annabi (SAW) har yaki ya je da su, don haka mun gayyaci kungiyoyin Musulunci gaba daya kamar na Tijjaniyya da kadiriyya, haka mun gayyaci kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN). Muna fata a matakin jihohi ma za a bi wannan salo kuma muna fata hukumomin gwamnatocin jihohi za su taimaka musu.
Aminiya: Sai dai wata babbar fuska da ba a gani ba ita ce ta Sheikh dahiru Bauchi da kuma Sheikh Sani Yahaya Jingir, me za ka ce?
Sheikh Yakubu Musa: Mun gayyace su kuma sun amsa kiran, Khalifan Tijjaniya na Najeriya Sheikh Isiyaka Rabi’u an gayyace shi ya turo wakilansa ciki har da ’ya’yansa kuma har kyauta an mika musu a madadinsa. Haka Sheikh karibullahi (Nasiru Kabara) Shugaban (darikar) kadiriyya ta Afirka shi ma an gayyace shi kuma ya turo wakilansa, Sheikh dahiru Bauchi mun gayyace shi kuma ina kyautata zato ya turo wakilansa. bangaren Sheikh Sani Yahaya Jingir mun gayyace su sai dai ba su samu zuwa ba, kuma ba mu ga wakilansu ba.