Tartsatsin wutar murnar sabuwar shekara ya raunata mutum 260 a Filifins
Hukumomi a kasar Filifins sun ce fiye da mutum 260 suka samu raunuka daga tartsatsin wutar murnar sabuwar shekara da kuma harsashin bindiga da ya kauce hanya.Wadanda suka jikkata a bikin sabuwar shekarar, sun hada da wnai yaro dan shekara takwas da ke tsakiyar birnin Cebu, wanda ya rasa hannunsa na dama, saboda karfin tartsatsin […]

Hukumomi a kasar Filifins sun ce fiye da mutum 260 suka samu raunuka daga tartsatsin wutar murnar sabuwar shekara da kuma harsashin bindiga da ya kauce hanya.
Wadanda suka jikkata a bikin sabuwar shekarar, sun hada da wnai yaro dan shekara takwas da ke tsakiyar birnin Cebu, wanda ya rasa hannunsa na dama, saboda karfin tartsatsin wutar da ya shafe shi; da kuma wata mata ’yar shekara 40 da ke birnin Manila, wadda harsashin bindiga ya saki hanya, ya sameta, inda ta samu mummunan rauni.
Jami’an Lafiya a kasar sun bayyana cewa, tartsatsin wutar ya jikkata amutum 253 ne, sannan mutum takwas kuwa harsashuin bindiga ne ya kauce hanya ya samesu, don haka suka yi gartgadin za a samu karuwar wadanda suka jikkata, kai har ma yawan mace-mace na iya karuwa, a wannan kasa da ke da yawan al’umma mutum miliyan 100. Mai magana da yawun hukumar, Eric Tayag, ya ce, za a samu karuwa mutum 50 zuwa 80 masu raunukan tartsatsin wuta a kowace sa’a, tun daga safe har duwa tsakar dare.
Mafi yawan kasashen da ke bin darikar Katolika, suna da tabbacin cewa a kowace sabuwar shekara za su iya korar shaidan, da miyagun iskokai, sannan su samar da sa’a da kyakkyawan yanakin rayuwa ta hanyar tartsatsi da rugugin karar wuta. Don haka wadanda suka kai makura a irin wannan imani, har bindiga suke harbawa sama, duk da cewa gwamnati ta haramta amfani da kayan tartsatsin wuta.
A bara, yara biyu harsashin bindiga da ya kauce hanya ya halaka, inda mutum fiye da 400 suka samu raunuka.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwato cewa ana zagaye bishiya a Filifins da abin rugugin wuta mai siffar maciji, a daidai lokacin da ya rage mintuna kadan sabuwar shekara ta kama.