Tarzoma ta barke a Bangladesh kan hukuncin rataye wani dan siyasa

Wata kotu mai shari’ar manyan laifuffuka a kasar Bangladesh ta yanke wa wani jigon dan siyasa a kasar hukuncin rataya, bayan ta same shi da aikata manyan laifuffuka a lokacin yakin neman ’yancin kasar a shekarar 1971, hukuncin da yanzu ya haifar da tarzoma. Tarzomar ta barke a harabar kotun ne bayan kotun da ke […]

Tarzoma ta barke a Bangladesh kan hukuncin rataye wani dan siyasa
Tarzoma ta barke a Bangladesh kan hukuncin rataye wani dan siyasa

Wata kotu mai shari’ar manyan laifuffuka a kasar Bangladesh ta yanke wa wani jigon dan siyasa a kasar hukuncin rataya, bayan ta same shi da aikata manyan laifuffuka a lokacin yakin neman ’yancin kasar a shekarar 1971, hukuncin da yanzu ya haifar da tarzoma.

Tarzomar ta barke a harabar kotun ne bayan kotun da ke yankin Dhaka ta Tsakiya a kasar ta yanke wa Abdus Subhan mataimakin shugaban jami’iyyar adawa mai suna Jamaat-Islami hukuncin rataya, bayan ta kama shi da aikata laifin kisan gilla da kuma azabtarwa.
Masu sharhi a kasar sun ce wannan al’amari zai ci gaba da haifar da tashe-tashen hankula a kasar, musamman ma da sauran jam’iyyun adawa suka goya wa jam’iyyar Jamaat din baya, don ganin ta kwace mulki daga Firayi Ministan kasar Sheikh Hasina.
A yanzu an kiyasta mutum 87 suka mutu tun bayan da shugaban jam’iyyar adawa BNP ya bukaci magoya bayan jam’iyyarsa su rufe titunan mota da hanyar jirgin kasa don a tilasta wa Hasina shirya zabe.
Alkalin kotun a kasar Obaidul Hassan ne yanke wannan hukuncin, inda ya ce za a rataye mai laifin har sai ya mutu.
“An same shi da aikita laifuffuka shida a cikin 9 da aka tuhume shi. A matsayinsa na shugaban jam’iyyar Jamaat an same shi da hada kai da sojojin kasar Pakistan inda suka rika gudanar da ayyukan assha da sunan Musulunci.”
Subhan shi ne mutum na 17 da kotun ta yi wa shari’a tun bayan da aka samar da ita a kasar.
Alkalin ya bayyana Subhan ya hada kai da sojojin Pakistan inda suka kashe daruruwan fararen hula ’yan kauyuka, wadanda akasarinsu tsirari ne a kasar, wato ’yan kabilar Hindu cikin shekarar 1971, lokacin da rikici ya barke a Gabashin Pakistan.
Lauyoyin Subhan sun ce za su daukaka kara saboda duk laifuffukan da aka ce ya aikata ba su da tushe ballantana makama.