Tarzoma ta barke a lokacin gudanar da zaben Malawi

An girke sojoji a babban birnin Malawi, Blantyre bayan da wasu masu kada kuri’a suka fusata da yadda zaben shugaban kasar ya gudana, masu zanga-zanagar sun cinnawa kayayyakin zabe huta da kuma sanya shingaye don tare wasu manyan hanyoyin birnin. Rahotanni sun bayyana cewa rashin bude rumfunar zabe da wuri ne ya jefa shakku a […]

Tarzoma ta barke a lokacin gudanar da zaben Malawi
Tarzoma ta barke a lokacin gudanar da zaben Malawi

An girke sojoji a babban birnin Malawi, Blantyre bayan da wasu masu kada kuri’a suka fusata da yadda zaben shugaban kasar ya gudana, masu zanga-zanagar sun cinnawa kayayyakin zabe huta da kuma sanya shingaye don tare wasu manyan hanyoyin birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa rashin bude rumfunar zabe da wuri ne ya jefa shakku a zukatan jama’an, wanda daga nan suka fara yada jita-jita cewa gwamnati na shirin gudanar da magudi ne. Hakan ya sa gungun jama’a bazama kan titunan birnin. A wata rumfar zabe da ke babban birnin kasar, wasu gungun jama’a sun kona kayayyakin zabe bayan da suka isa rumfar a makare. A wasu mazabu kuma matasa ne suka rufe hanyoyi da manyan duwatsu inda daga baya kuma ’yan sanda suka fatattakesu. A tsakiyar birnin kuma wasu matasa sun jagoranci wata karamar zanga-zanga inda sukai ta fadin kalaman kin jinin gwamnati.
Shugaban Hukumar Zaben kasar, Madon Mbendera ya nemi afuwa kan fara zaben a makare, kuma ya baiwa ’yan kasar tabbacin cewa jami’an tsaro sun shawo kan tarzomar.
Wasu daga cikin ’yan takarar da ke kalubalantar Shugabar Mai ci, Joyce Banda sun fara bayyana kokensu, inda suke zargin gwamnati da aringizon kuri’u. Sai dai kuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa Misis Banda ce ke kan gaba saboda irin farin jinin da take da shi tsakankanin jama’ar da ke zaune a yankunan karkara wanda ta gudanar masu da ayyukan ci gaba.
Misis Banda ta dare karagar mulki ne shekara biyu da suka wuce bayan mutuwar Shugaba Bingu wa Mutharika. kanin marigayin Peter Mutharika shi ma dan takara ne a zaben a karkashin inuwar jam’iyyar Democratic Progressibe Party (DPP). Amma tafi fuskantar kalubale daga dan takarar jam’iyyar Congress wato Lazarus Chakwera.