Tashar NTA ta yaba wa NCC game da bunkasa harkokin wasanni
Tashar talabijin ta kasa (NTA) ta yaba da kokarin da Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) take yi game da bunkasa harkokin wasanni a sassan kasar nan. Manajin Darakta na Tashar talabijin ta NTA Tb Enterprises wacce daya ce daga cikin tasoshin talabijin da ke karkashin NTA Mista Madwell Loko ne ya bayyana haka a lokacin […]

Tashar talabijin ta kasa (NTA) ta yaba da kokarin da Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) take yi game da bunkasa harkokin wasanni a sassan kasar nan.
Manajin Darakta na Tashar talabijin ta NTA Tb Enterprises wacce daya ce daga cikin tasoshin talabijin da ke karkashin NTA Mista Madwell Loko ne ya bayyana haka a lokacin da suka kai wa Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umaru dambatta ziyara a ofishinsa da ke Abuja a ranar Larabar da ta wuce.
Ya ce Tashar talabijin ta NTA ta dade tana bibibiyar yadda Hukumar NCC take daukar nauyin gudanar da wasanni daban-daban a kasar nan a kan haka ne ya yaba wa NCC game da sauke daya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyanta ga al’umma wato (Corporate Social Responsibility, CRS).
Daga nan sai ya nemi hadin kan hukumar a game da yunkurin da tashar NTA take yi na kaddamar da kundin littafi a kan irin nasarorin da Najeriya ta samu a bangaren wasanni (Nigeri’as Delegation Sports Book of Record) wanda ake sa ran amfani da kudin da za a samu yayin kaddamarwar wajen daukar nauyin matasa maza da mata da ke rungumar harkar wasanni a bangarori daban-daban don ganin su yi fice a ciki da kuma a wajen kasar nan.
“Gaskiya dole ne mu yaba wa Hukumar NCC a game da bunkasa harkokin wasanni. Na dade ina bibiyar yadda NCC take daukar nauyin harkokin wasanni a kasar nan don haka zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga sauran hukumomin gwamnati su yi koyi da NCC a game da bunkasa harkokin wasanni. Ya kara da cewa wannan ziyara da muka kawo wa NCC za ta bude wata kafa na karfafa dankon zumunci, kuma wata hanya ce da za mu rika sanar da duniya irin dawainiyar da hukumar ke yi wajen bunkasa harkokin wasanni a littafin da muke da niyyar kaddamarwa.
Ya ce kasancewar NCC wata kafa ce ta sadarwa, tana daga cikin hukumomin da za mu yi amfani da su wajen watsawa duniya a lokaci da kuma bayan kaddamarwar. Ya ce “ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen sanar da duniya cewa NCC tana daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawa game da kaddamar da wannan littafi, don haka muke bukatar ku kasance daya daga cikin wadanda za su dauki nauyin kaddamar da wannan littafi”.
“ Littafin zai kunshi ’yan wasan da suka yi fice ne maza da mata da ke zaune a sassan duniya, ba ga wadanda ke cikin Najeriya kadai ba”. “Sannan za mu yi amfani da wannan dama wajen karfafa dankon zumunci a game da bunkasa harkokin wasanni a kasar nan”.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NCC Farfesa dambatta wanda ya samu wakilci daga Manajan hulda da ’yan jaridu na hukumar NCC Mista Sonny Aragba-Akpore ya ce NCC ta dukufa wajen bunkasa harkokin wasanni a kasar nan duk da yake ba shi ne aikinta na ainihi ba. Ya ce hukumar tana yin haka ne don daukaka martabar matasan da ke kasar nan.
Ya ce a lokacin da hukumar ta fara daukar nauyin gasar kwallon tennis kimanin shekaru uku da suka gabata, jama’a da dama sun dauka abin ba zai daure ba, sai ga shi kawo yanzu shirin sai bunkasa yake yi a kowace shekara. Misali a gasar tennis da NCC ta dauki nauyi a bana (2017) wadanda suka samu nasara a gasar sun lashe kyautar Naira miliyan 17 ne.
Sannan ya ce hukumar tana karfafa wa ma’aikatanta gwiwa wajen rungumar harkar wasanni. Ya ce a game da hakan yanzu haka Hukumar NCC ta tura tawagar ’yan wasanta zuwa Jihar Bauchi don halartar Gasar Wasanni ta kasa da Ma’aikatar Kula da Hukumomin Sadarwa ta Najeriya (Federal Ministry of Communication) ta dauki nauyi. Sannan hukumar NCC takan shirya wa ma’aikatanta yin balaguro a kowane wata uku don su rika samun kuzari wajen yin tafiya mai nisa da kafa.
Daga nan ne ya shaida wa tawagar NTA cewa zai gabatar da bukatar da suka kawo don bayar da gudunmawa wajen kaddamar da littafin ga Shugaban Hukumar Farfesa dambatta wanda ba ya nan a lokacin da suka kai ziyarar.
Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Hukumar NCC take daukar nauyin kaddamar da wani littafi ba, musamman idan aka yi la’akari da cewa shugaban tsohon malamin jami’a ne wanda ya san muhimmancin daukar nauyin kaddamar da wani littafi.
Ya ce “ina tabbatar muku da cewa Shugaban NCC yana da sha’awa a game da bunkasa harkokin wasanni don haka zai yaba da wannan shawarar da kuka kawo masa”. Za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun hada kai da ku don ganin an ci gaba da bunkasa harkokin wasanni a kasar nan”.