Tashe-tashen hankali a Najeriya: Abin da ya ba ka tsoro…
Malam Aliyu Ibrahim Shariff Gashu’a, Jihar Yobe (08136153181) ya yi mana tsokaci ne game da al’amuran tashin hankali da suka addabi al’umma, musamman ma yankin Arewa maso gabas. Ga abin da yake cewa: Ganin yadda talakawan kasata Najeriya suka shafe fiye da shekaru goma sha hudu a mulkin babbar jam’iyya ta kasa, wato PDP, nake […]
Malam Aliyu Ibrahim Shariff Gashu’a, Jihar Yobe (08136153181) ya yi mana tsokaci ne game da al’amuran tashin hankali da suka addabi al’umma, musamman ma yankin Arewa maso gabas. Ga abin da yake cewa:
Ganin yadda talakawan kasata Najeriya suka shafe fiye da shekaru goma sha hudu a mulkin babbar jam’iyya ta kasa, wato PDP, nake so na yi amfani da wannan dama na yi tsokaci game da yadda sabuwar jam’iyyar adawa ta APC ke da alamar share mana hawaye baki daya.
Sanin kowa ne kasarmu Najeriya Allah Ya albarkace ta da dimbin arziki, wanda kusan fadin nahiyarmu ta Afirika babu kasa mai arzikinta. Sai dai kash, babu wani ci gaba ga rayuwar talakan Najeriya, wanda haka ya janyo matsaloli kamar rashin ingantaccen ilimi, rashin wutar lantarki, rashin samar da tsaro ga ’yan kasa, rashin ruwa, rashin samar da aikin yi ga matasa, da dai sauran matsaloli da dama, wadanda duk sun ta’allaka ne ga jagorori masu mulkinmu, mu talakawa kama daga kan Gwamnatin Tarayya har ya zuwa na kananan hukumomi.
Don haka, nake shawartar talakawa ’yan uwana da su dage wajen ganin mun samar wa kawunanmu ’yanci a wannan zaben da ke karatowa na badi; ganin wata hukuma mai zaman kanta da ake kira ‘Transparency International’ ta fidda wani rahoto da ke cewa talakawan Najeriya, kashi saba’in da biyar na al’ummar Najeriya na rayuwar wuni guda a kasa da dalar Amurka guda (kwatankwacin Naira dari da tamanin). Haka na faruwa ne dalilin gazawar jagororinmu da Allah Ya ba su amanar mulkinmu kuma suka rantse da Alkur`ani da kuma Baibul a kan za su yi aiki da adalci. Nake kuma kara jaddada wa talakawa da mu kasa-mu-tsare-mu-raka-mu-jira-a-fada, don tabbatar da kuri`unmu, sannan mu dage da addu`ar Allah Ya dora mana shugaba mai kishin talakawa baki daya.
Daga karshe nake jinjina wa ’yan jam`iyyar APC baki daya, bisa ga namijin kokarin da suke yi na ganin cewa sun fidda Najeriya daga cikin mugun halin da ta samu kanta a ciki saboda rashin jagora da ta yi, wanda hakan bai taba faruwa kamar na want ton lokacin ba. Haka kuma nake kara addu`ar Allah Ya taimaki Janar Muhammadu Buhari, a duk wasu al`amuransa da ya sa gaba, don ci gaban rayuwar galaka. Nake kuma addu`ar Allah Ya kawo mana karshen fitintinu a yankinmu na Arewa maso gabas, Najeriya, Afirika da ma duniya baki daya. Amin. Wassalam.
Janar Buhari: Babban kalubalen da ke gaban ’yan Najeriya
Shi kuwa KWAMARED BISHIR DAUDA SABUWAR UNGUWA KATSINA (08165270879), ya nusar da al’umma ne irin kalubalen da ke gabansu, musamman game da neman canjin shugabanci da suke hankoron yi. Ya ja hankali game da Janar Muhammadu Buhari. Ga abin da yake cewa:
Lokacin da talakawan Arewacin Najeriya da wasu a sauran sassa na kasar suka samu labarin cewa Janar Buhari ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyarsa ta APC, shagulgula sun barke ciki har da garin Zariya kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
To sai dai ba nan gizo ke sakar ba, mutane da yawa na son canji a Najeriya, to amma canji na tattare da kalubalen da sai kowa ya sadaukar da komi nasa, sannan za a iya samun canji mai ma’ana. Duk mai tunanin Buhari kawai shi daya zai samar da canji, to yana mafarki ne kawai. Kazalika, duk mutumen da ke tunanin cewa da an kawar da gwamnatin PDP a matakin Tarayya, rashawa za ta kau, talauci zai zama tarihi, yunwa za ta bace, za a yi adabo da jahilci, rashin tsaro da rashin imani, to shi ma bai nakalci matsalar kasar nan ba.
Tabbas a Najeriya ana bukatar shugabanci nagari kuma tabbas mutane da yawa sun yarda Buhari mutum ne mai akida, mai kamanta gaskiya, mai rikon amana, to amma duk wannan na Buhari ne kadai. Tambaya, ni da kai da ke da su, me ke gare mu? Muna da gaskiya? Muna da amana? Muna da cika alkawari? Muna girmama lokaci? Idan ba mu da wadannan dabi’un, to Buhari muke jira ya zo ya koya mana su? Kada mu manta, Buhari zai yi bakin iyawarsa, to amma haka ba zai isa ba sai mutane sun sauya halinsu na son zuciya. Buhari na da tarihin ba-sani-ba-sabo ga masu izgilanci da yi wa doka Karen-tsaye. Talaka shi ne kan gaba wajen son Buhari, to Buhari fa ba zai kyale a yi sakarci ba. Karya dokokin hanya kamar guje-guje da abin hawa, dauko mutane fiye da ka’ida, kin bin danja, duk hukunci ne mai tsanani. Masu zuwa layin ATM su yi kutse da masu kin bin layi a banki, idan Buhari ya ci, duk za su gaya wa aya zakinta. Masu ciye-ciye kan titi suna zubar da shara da masu zubar da shara daga cikin mota, duk za su san lallai Buhari ne ke mulki. Ma’aikata masu ha’inci, a je aiki yau gobe a ki zuwa, masu wulakanta jama’a a wurin aiki, ma’aikatan bogi duka za su gane ko me ake nufi da canji.
Da yawa na da jahilcin cewa Buhari zai doki manya ne kawai, a’a, Buharin da muka sani babu ruwansa da bambanci, talaka da mai kudi, dan sarki da dan sarka duk wanda yai sakarci to doka za ta fyadai.
Sannan masu tunanin da Bahari ya hau komi zai dawo daidai, su ma su sani cewa al’ammura sun lalace sosai a Najeriya. Wasu na hasashen cewa zai dauki shekaru kamar hamsin kafin a gyara Najeriya. Shekaru Hamsin rabin karni ne ke nan. Muna tsammanin Buhari shekaru hudu zai yi kamar yadda ya yi alkawari saboda haka,Buhari ba zai iya gyara Najeriya cikin shekaru hudu kacal ba. Shugabanci abu ne mai matukar wahala, don haka talaka ya shirya fuskantar lokaci mafi wahala idan Buhari ya ci zabe, domin dole sai an sake lale; sai kowa ya yi aiki tukuru kuma kowa ya ba da hadin kai kafin Buhari ya iya samar da canjin da talaka ke so. Talaka dole ya yi hakuri mai tsawo kuma dole kowa ya daidaita sahunsa da na iyalansa, domin Buhari kadai ba zai iya daidaita sahun kowane mutum a Najeriya ba. Kuma amfani da karfi kawai, ba zai iya sauya halayyar dan Adam ba.
Lallai Buhari zai karbi Najeriya a lokaci mafi hadari, lokacin da kabilanci, addinanci, bangaranci da son zuciya suka wa kasar katutu; lokacin da rashin aminci da yadda ya kazanta tsakanin ’yan kasar, lokacin da cin hanci da rashawa ya shiga jini da bargon ’yan Najeriya. Lallai ba karamin jarumi ne zai iya tafiyar da kasar ta yadda kowane sashe na kasar zai gamsu ba. Don haka, kamata ya yi ’yan Najeriya mu yi ta addu’a, Allah Ya fidda Buhari kunyar ’yan Najeriya.
Wani abin dubawa shi ne, ga shekaru sun hau Buhari, ga wahalar yakin neman zabe, sannan ya dawo ya fuskanci tulin aikin shugabantar Najeriya. Lallai duk mai hankali, addu’a ya kamata ya yi wa Buhari ba murna ba.