EFCC ta tsare ’yan canji a Kasuwar WAPA
A safiyar Laraba jami’an Hukumar EFCC suka yi dirar mikiya a kasuwar ta WAPA a wani yunkuri na yaki da ayyukan masu boye Dala.
Hukumar EFCC ta tsare wasu ’yan kasuwa a samamen da jami’anta suka kai kasuwar ’yan canji ta WAPA da ke Jihar Kano ranar Laraba.
A safiyar Laraba jami’an hukumar cikin shigar burtu, suka yi dirar mikiya a kasuwar ta WAPA a wani yunkuri na yaki da ayyukan masu boye Dala.
Wani ganau mai suna Malam Isma’ila Zico, ya ce jami’an na EFCC “Sun nuna kwarewa, sai daga bisani muka gano cewa tun safe suke nan.
“Lokacin da za su fara aikin ne sai muka ga masu jaket dinsu sun shigo, suka yi wa wajen yan canji kawanya.
- ’Yan bindiga sun sace fasinjoji 26 a hanyar Funtua-Gusau
- DSS ta nemi NLC ta janye zanga-zangarta kan tsadar rayuwa
“Ban san ko mutum nawa suka kama ba, amma dai sun tafi da wasu ’yan canjin,” in ji Zico, wanda ya ce an kai samemen ne a yayin da ake tsaka da hadahadar kasuwanci.
EFCC ta kai samemen ne a yayin da ake tsaka da hadahadar kasuwanci, suka yi awon gaba da wasu daga cikin yan kasuwar.
Shugaban ’yan canji na kasuwar, Alhaji Sani Salisu Dada, ya tabbatar kamen na ranar Laraba, wanda ya ce za a binciki wadanda aka yi awon gaban da su na.
A ceawrsa, jami’an EFCC sun kai samamen ne domin shawo kan matsalar masu boye dala da kuma ’yan canji masara lasisi.
Amma ya kara da cewa an ci gaba da harkoki yadda aka saba a kasuwar, kuma a shirye suke su ba da hadin kai ga hukuma.
Hakan na zuwa ne sakamakon ci gaba da tashin gwauron zabo da dalar ke yi a wurin ’yan canji a sassan kasar, inda farashin dalar ya kai N1,900.
A ranar talata gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin tsaro da su dauki matakin kamawa, bincike da kuma hukunta masu wannan dabi’a.
Ko a ranar talata jami’an EFCC sun kai makamancin wannan samame a kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Zone 4 da ke Abuja.
A safiyar Laraba ma rahotanni sun nuna cewa an kai irin wannan samame a kasuwar ’yan canji da ke Unguwar Sabo a garin Ibadan, Jihar Oyo.