Tashin Dala: Gwamnan CBN ya sauka kawai —PDP
Farashin Dala yan ninka sau uku a shubabancin Emefiele a CBN.
Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya sauka daga mukaminsa saboda tashin gwauron zabon farashin Dala da kuma lalacewar tsare-tsaren kudade a Najeriya.
Sakataren Yada Labaran PDP, Kola Olagbondiyan, ya ce shugabancin Emefiele a CBN, a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC shi ne lokacin da tsarin kudaden Najeriya ya fi shiga mawuyacin hali har farashin Dala ya ninku fiye da sau uku.
- Kudaden shiga daga bangaren man fetur sun ja baya
- Ba za mu fallasa masu taimakon ’yan ta’adda ba —Gwamnati
- ’Yan bindiga daga Zamfara da Katsina sun fara kai hari Kano
Ologbondiyan ya ce, “Ya kamata a tuna cewa lokacin da aka nada Emefiele a matsayin Gwamnan CBN a 2014 farashin cajin Dala N164 ne.
“Amma zwau yanzu da CBN a karkashin Emefiele da gwamnain APC, farashin Dala ya kusa kaiwa N600, lamarin da ke neman durkusar da tattalin arzikin Najeriya.
“Abin takaicin shi ne shugabancin Emefiele a CBN ya gaza a babban aikinsa na gudanar da tsare-tsaren tattalin arziki, amma yake ta yada farfaganda sabanin abin da ke faruwa a zahiri a bangaren na tattalin arziki,” inji shi.