Tasiri da muhimmancin taimako a rayuwa (2)
Jama’a, ina yi maku sallama, assalamu alaikum! A yau kuma za mu karkare wannan tsokaci da muka faro a makon jiya, inda muke duba muhimmanci, tasiri da kuma dinbin sinadaran da ke tattare da taimako ga rayuwarmu ta yau da kullum, a matsayinmu na mutane.Haka dai za a ci gaba, har yaro ya ci gaba […]
Jama’a, ina yi maku sallama, assalamu alaikum!
A yau kuma za mu karkare wannan tsokaci da muka faro a makon jiya, inda muke duba muhimmanci, tasiri da kuma dinbin sinadaran da ke tattare da taimako ga rayuwarmu ta yau da kullum, a matsayinmu na mutane.
Haka dai za a ci gaba, har yaro ya ci gaba da girma, sannan a ci gaba da ba shi abinci da abin sha da sutura. Sannan kuma a yi ta taimaka masa da hudubobi da shawarwari, sannan ma har a sanya shi makaranta, duk dai domin ya samu cikakken hankali da halayen kwarai, ta yadda zai zama mai dogaro da kansa. Wannan duk wasu nau’ukan taimako ne da ake masa, wadanda idan ba a yi masa su ba, babu yadda za a yi ya samu sa’idar rayuwa cikin dadi.
Idan kuma ya girma, ba shi ke da dubarar samun aiki ko sana’ar da ya samu ba. Sai da ya shiga hannun wani ko wata, sannan ya koya, ya iya. Sai da aka tallafa masa, aka taimaka masa, aka dauke shi aiki, ko kuma aka taimaka masa da jari, sannan ya samu duk wani abu da ya samu a ma’aikatar ko kuma a wurin sana’ar tasa. Ashe lallai mutum ya samu tallafi da taimakon wasu, kafin ya samu nasara a rayuwa.
Ina fatan yanzu dai duk an gane misalaina, kuma an ankara da dalilan da ke nuna cewa mutum, ko shi wane ne, yana bukatar taimako. Babu shakka na san yanzu an gane da haka. Idan mutum na ganin yanzu ya zama attajiri, to lallai yana bukatar taimako ta bangarori da dama. Dole sai an tallafa masa kafin ya samu damar watayawa, domin kuwa akwai abubuwa da yawa da ba zai iya aiwatarwa ba da kansa. Ko da biya zai yi a yi masa da kudi, taimako ne dai, domin wani dan Adam din ne zai aikata masa.
A lokacin da muka kasance attajirai, muna jin cewa lallai dukiya ba matsala ba ce a rayuwarmu. To, mu waiwaya baya mu taimaki wadanda ba su da shi, domin mu ma an taimaka mana a lokacin da ba mu da shi. kwarai kuwa, domin kuwa idan mun tuna, mu ma an taimaka mana a lokacin da muka zo duniya a matsayin tsirara, ba tare da komai ba a hannunmu ko a jikinmu. Idan mulki ne Allah Ya ba ka, lallai akwai bukatar ka yi amfani da wannan mulki domin taimakon dan uwanka mutum mai rauni, domin kai ma an taimaka maka kuma akwai ranar da za ka dawo kan dole ka nemi taimakon mutane. Idan ilimi ne Allah Ya wadata ka da shi, sai ka yi himma ka taimaka wa jahilai domin su samu wannan ilimi, domin akwai lokacin da kai ma ba ka da shi, sai da wani ya taimaka maka. Domin a lokacin da kake jahili, wani kuwa yana da dinbin ilimi, sai ya taimaka maka ya koya maka wani bangare na iliminsa, wanda dalili ke nan ya sanya ka zama malami a yanzu. Ke nan, kwaryar da ta je, kamata ya yi ta dawo.
Idan mun lura da hikimar da ke cikin wannan rayuwar, abin ya kasance dai kamar cude-ni-in-cide-ka. Haka kuma rayuwa ta kasance tana zagayawa. Mai shi ya tallafa wa mara shi har ya zama mai shi, wanda nan gaba shi ma ya tallafa wa wani, wanda zai zama mai shi. Haka lamarin yake a kowa ne zamani.
Sai dai a rayuwarmu ta yau, muna ji muna gani, mun kekasar da zukatanmu, ba mu son taimako da tallafa wa juna. Wannan dalilin ne ya sanya muke cikin rudu da tashin hankali. Idan mai dukiya ya rike dukiyarsa, alhali yana ganin ’ya’yan talakawa na gararamba babu karatu, babu abin yi. Babu shakka hankalinsa ba zai kwanta ba, domin kuwa su ne za su rika tare masa hanya suna yi masa kwace kuma suna razanar da iyalansa. Idan mai mulki ya ki amfani da mulkinsa wajen taimakawa da adalci, babu shakka shi da iyalansa da danginsa ba su tsira ba, domin dai yana zaune ne cikin mutanen da yake wa rashin adalcin.
Abin da wannan tsokaci na yau ke nuna mana shi ne, kowa na bukatar taimako. Taimakon wani kamar taimakon kai ne. kin taimakon wani, alhali kana da halin taimakawa, kamar ka sayi wuka ne kuma ka burma wa cikinka. Hausawa ma dai sun ce, alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza. Don haka sai mu kasance cikin taimakon juna a kowane lokaci!