Tasiri da sauyin da Najeriya ta samu a ɓangaren noma
A daidai lokacin da muka shiga sabuwar shekara, mu ka ga dacewar biyayar nasarori da kalubalan da harkokin noma suka fuskanta a shekarun baya, tun bayan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kudiri aniyar kawo sauyi a bangaren. Wannan wani nazari ne da Dakta Aliyu Tilde ya yi, sannan gidan rediyon BBC ya wallafa a kwanakin […]
A daidai lokacin da muka shiga sabuwar shekara, mu ka ga dacewar biyayar nasarori da kalubalan da harkokin noma suka fuskanta a shekarun baya, tun bayan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kudiri aniyar kawo sauyi a bangaren. Wannan wani nazari ne da Dakta Aliyu Tilde ya yi, sannan gidan rediyon BBC ya wallafa a kwanakin baya, inda masanin ya dubi irin tasirin hana shigar da shinkafa Najeriya ta tudu ya yi da kuma janye tallafi a kan takin zamani da kuma irin sauyin Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo a harkar noma da sauransu kamar haka:
Benezuela da Najeriya ƙasashe ne biyu da gwamnatocinsu suka dogara kan man fetur wajen samun kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje. Yau shekara uku ke nan tun da farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwannin duniya, inda ya sauko daga dala 120 a shekarar 2012 har zuwa dala 30 a 2015. Sai dai tasirin faɗuwar man fetur a kasashen biyu ya bambanta. Duk da cewa akwai ƙarin matsin rayuwa a ƙasashen biyu, a Benezuela muhimman abubuwan rayuwa kamar magunguna da abinci sun gagara.
A Najeriya, inda akasarin mutanen ƙasar manoma ne, an ci gaba da noma abinci kamar yadda aka saba. Hasali ma a 2016 an samu amfanin gona wanda an jima ba a samu irinsa ba saboda albarkar damuna. Duk da matsin rayuwa a Najeriya a yau, akwai magunguna da sauran muhimman abubuwan rayuwa da mutane za su saya ba kamar a Benezuela ba.
Wannan bambanci tsakanin ƙasashen biyu wajen tasirin faɗuwar farashin man fetur a kan rayuwar jama’a ya samo asali ne daga cewa yayin da tattalin arziƙin Benezuela da mutanenta suka dogara kacokam a kan man fetur wanda da kudinsa ake shigo da abinci da sauran muhimman abubuwan more rayuwa daga kasashen waje, a Najeriya noman cikin gida ne yake taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da mutanen ƙasar. Tun shekarar 1984, noma yake ba da wajen kashi 40 na arizikin mutanen kasar (GDP).
To amma duk da samun abinci a ƙasarsu, jama’ar Najeriya na matuƙar kokawa da tsadarsa, har ta kai talakawa da yawa ba sa iya sayensa isasshe. Alal misali, buhun shinkafa mai kilo 25, ya ninka kuɗinsa daga dubu 8 a 2015 zuwa dubu 19 a 2016; masara – wadda ita ce talakawa suka dogara da ita – buhunta ya ninka sau uku daga dubu 5 zuwa dubu 150; suga shi ma daga dubu 6 zuwa dubu 19 da sauransu.
Da kakar bara, an samu sauƙin kayan kaɗan, a inda ƙaramin buhun shinkafa ya sauko zuwa dubu 15 har tsawon wata daya, amma a watan Afirilun bara farashin kayayyakin sun fara tashi kuma. A kasuwar Jos misali, bayan sauƙi da aka samu kwanan baya, a yanzu ana sayar da buhun suga a naira dubu 18; buhun masara a dubu 14; na shinkafa a dubu 18. Ana kuma tsoron farashin zai ci gaba da ƙaruwa musammam idan damuna ta yi nisa.
Abubuwa biyu ne suka kawo tsadar abinci a Najeriya: Hana shigo da shinkafa ta iyakokin tudu da kuma janye kowanne irin tallafi na aikin noma har da na takin zamani da sabuwar gwamnatin ta yi – matakai biyu wadanda ba wata gwamnati a baya da ta taɓa ɗauka a ƙasar. Duk da koke-koken da ‘yan ƙasa da shugabanninsu da Majalisar Dattijai suka yi a kan wadannan matakan, gwamnatin ta yi mirsisi ta tsaya a kan bakanta don ta yi imani cewa ta haka ne kaɗai ƙasar za ta zama mai dogaro da kanta. A wannan shekarar ta 2017, hana shigo da shinkafa zai haɗa har da ta teku.
Alal haƙiƙa, an samu haɓakar noman shinkafa da alkama a Najeriya, kuma tsadar abincin ya sa mutane da yawa da suka ga uwar-bari sun koma noma amfanin ciyar da gida musammam hatsi.
To amma tsadar kayan abinci a ƙasar za ta ci gaba da sanya talaka tagumi, musammam mai karɓar albashi wanda a yanzu abin da ake biyan shi ba zai saya masa rabin abin da yake saya masa ba shekara biyu da suka wuce, kuma ga shi gwamnati da kamfanoni sun ƙi ƙara albashi balle ma’aikatan su samu sa’ida.
A nan, ana iya tambaya: Mene ne manufofin gwamnatin a aikin noma da kiwo kuma ina ta kai wajen cim ma waɗannan manufofi?
Idan ana batun manufofin gwamnatin siyasa a duniya, ma’auni na farko shi ne a duba alƙawuran da ta yi wa mutane lokacin zaɓe sannan a haɗa da waɗanda ta yi bayan ta hau mulki. Cikin alƙawurran da ta yi, nawa ta cika? A kundin manufofi na jam’iyya mai ci a Najeriya APC – akwai alƙawari 19 da jam’iyyar ta ce za ta cika idan ‘yan Najeriya suka zaɓe ta a shekarar 2015.
A wajen bibiyar ina aka kwana game da waɗannan alƙawurran, wata gamayyar kungiya uku – watau CDD da OSSIWA da BudgIT – sun kirkiro shafin intanet na musamman mai suna Buharimeter. A ciki, ƙungiyoyin sun nuna cewa alƙawari uku ne kacal gwamnati mai ci yanzu take wani abu a kan su cikin 19 da ta yi lokacin zabe a fannin noma.
Waɗannan su ne batun canza aikin gona daga na masu ƙaramin ƙarfi zuwa noman kasuwanci na zamani, da inganta yaɗa dabarun noma, da inganta bankunan ci gaba kamarsu Bankin Noma da Bankin Masana’antu, amma ƙungiyoyin ba su da abin cewa a kan ragowar alƙawari 16 da jam’iyyar APC din ta yi yau fiye da shekara biyu kenan bayan ta hau mulki.
Wannan ba ya nufin cewa gwamnatin ba ta yi komai ba a fannin noma. Alal misali, ta samar da tsari na bai wa manoman shinkafa bashi wanda aka aiwatar a wasu jahohi ta hanyar ba da bashin kayan aiki ga manoma. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da aka samu bunƙasar noman shinkafa a Jihar Kebbi misali, inda gwamnatin jihar take ikirarin an noma sama da tan miliyan guda na shinkafa a bara.
Akwai kuma batun yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta cim ma tsakaninta da ƙasar Sin. A cikin wannan yarjejeniya, ƙasar Sin za ta samar wa Najeriya na’urorin noma da kiwo iri daban-daban da kuɗinsu ya kai dala biliyon 4 a matsayin bashi don bunƙasa aikin noma da kiwo. Wannan shiri ya yi nisa, a inda ake tsammanin isowar wasu daga cikin kayan kowane lokaci daga yanzu.
Haka kuma akwai yarjejeniya da kasar Morocco a kan samar da takin zamani wadda ita ma ta fara aiki, inda ita kasar Morocco din take tallafawa masana’antun taki na cikin gida wajen samar da wadataccen taki ga manoma a farashi mai rahusa.
Har ila yau, an samu nasarar mayar da duk jami’o’in ayyukan noma ƙarƙashin Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara don tabbatar da ganin makarantun suna taka rawar da ta kamata wajen wanzar da ilmin aikin noma da bincikensa a ƙasar.
Ministan Aikin Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh, ya yi batun samar wa makiyaya matsuguni na dindindin a jihohi daban-daban na kasar inda har a shekarar 2016 ya ba da tabbacin cewa ba saniyar da za ta yi yawo nan da wata 18. Wannan wa’adi ya wuce amma har yanzu ba a ma ƙare gardamar zartar da dokar ba a Majalisa kuma wasu jihohi da ƙungiyoyin al’ummu sun kyamaci shirin inda suke cewa ba su da dazukan da za su ware wa makiyaya. Aikin da kamar wuya don Gwamnatin ita ma ta ce ba za ta tilasta wa kowa bayar da filinsa don shirin ba.
A ƙarshe Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya ta fito da shirin wannan gwamnati na bunƙasa aikin gona kwanan nan wanda ta yi wa laƙabi da Tsarin Bunƙasa Aikin Noma na 2017-2020 – wato Agriculture Promotion Policy. Manufar shirin, kamar na gwamnatocin baya da suka wuce, shi ne ƙasar ta zama mai ci da kanta a shekarar 2020.
Najeriya kasa ce da ke cike da duk abin da ake buƙata na bunƙasa noma: Akwai filin noma wadatacce, da ruwan sama da koguna da madatsun ruwa, da ɗumbin manoma da makiyaya. Abin da kawai ya gaza shi ne tsarin hukuma da zai tattara waɗannan abubuwa waje daya ta yadda noma da kiwo za su bunƙasa ba tare da an bar komai a hannun talakan manomi ba, ba kuma da an bar masu hannu-da-shuni sun shiga harkar sun yi kaka-gida ba.
Tabbas Najeriya ba Benezuela ba ce, saboda waɗannan ni’imomi da Allah Ya yi mata. Amma manazarta da yawa na tababar himmar wannan gwamnati da waɗanda suka shude a kan noma. Farfesa Ango Abdullahi na cewa zai yi wuya gwamnati ta iya bunƙasa noma da kashi 1.2 kacal da ta warewa harkokin aikin gona a kasafin kuɗinta na 2016 ko kashi 1.6 a cikin kasafin shekara ta 2017, alhali noma ne ke bai wa ‘yan ƙasa kashi 40 na arziƙinsu.
Manazartan na cewa muddin Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta ci gaba da manufarta na janye tallafi da rashin zuba jari a harkar noma ta bar talaka kowa tasa ta fisshe shi, to fa tsadar abinci a ƙasar ba za ta ƙare ba kuma ga akasarin yan ƙasar, wata miyar, sai dai su ji ta a maƙwabta.