Tasirin Abinci Ga Ingancin Ibadar Aure (2)
Assalamu alaikum, marhabin da sake haduwarmu a cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, domin inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin. Abincin karin dandano, Da karfin Sha’awar Ma’aurataDukkanin […]
Assalamu alaikum, marhabin da sake haduwarmu a cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, domin inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Abincin karin dandano, Da karfin Sha’awar Ma’aurata
Dukkanin abincin nan da zan jero, cin su a kai-a kai ne kadai ke tabbatar da samun lafiyayyar sha’awa ba wai a ce sai lokacin da ake so ne kadai za a ci su ba, amfanin su kamar shan ruwa ne, don ka sha yanzu bai hana idan an jima ka sake jin kishirwa, don haka maigida sai ya dage da sayo su, ke kuma uwargida sai ki dage da saka su cikin duk girke-girkenku dai-dai misali, sannan a lura, ba a son a cika masu wuta wajen dahuwa domin sinadaran ciki duk sai su kone, kuma sune suke gina sha’awa ba wai dusar abincin ba, da fatan Allah ya sa a dace amin.
1.Lansir: Wannan ganye yana da matukar alfanu wajen inganta lafiyar sha’awar ma’aurata domin yana dauke da sinadarin androsterone, maza na fitar da shi ta gumin jikinsu, idan uwargida ta shake shi yana sa mata nishadin mijinta a zuci.Wannan zai taimaka wajen motsa mata sha’awarta. Uwargida na iya kwadon ganyen lansir, da kuli da mai da yaji, ko ki sanya shi saman shinkafa ko ma ku ci shi a haka yadda ya ke.
2. ‘Ya’ya kabewa (kadawa, kabushi ko goji): Wannan wani abu ne da zubar da su ma mu ke yi duk lokacin da mu ka yi amfani da kabewa wajen yin miyar taushe cikin rashin sanin cewa sun fi ainihin tsokar kabewar amfani ga lafiyar jikinmu. Kuma musamman suna tsananin inganta ma’aikatar sha’awa. Cike suke da sinadarin Zinc, wanda da shi jiki yake amfani wajen sarrafa sinadarin sha’awa da kuma ruwan maniyyi, kuma shi yake inganta lafiyar Prostate gland, wani tsibirin sinadarai da ke kula da sarrafa ruwan maniyyi da kwayayen halittar da namiji. Sannan yana dauke da dukkanin bitamins masu inganta lafiyar sha’awa irin su C, D, E, K da kuma B mai rassa(B compled). Haka kuma yana dauke da sinadarin myosin da ke inganta lafiyar jijiyoyin ‘yan matanci. Haka kuma yana dauke da sinadaran omega 3 wanda su ma suna inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa. ‘Ya’yan kabushi suna da matukar amfani ga lafiyar jiki duka ba ga sha’awa kadai ba ma. Inda ma’aurata za su iya, to su ci su haka yadda suke cikin kwansansu, sai sun fi ganin alfanunsu. Sun fi dadi in aka gasa su irin gashin da ake yi wa gyada. Amma zafin yakan kone da yawan sinadarai masu alfanun da suke cikinsu. Uwargida na iya gyara su, ta cire kwanson, sai ta watsa su saman abinci in ya kusa dahuwa kamar dai yadda ake watsa tsanwar wake, karas ko kabeji. Sanna tana iya amfani da su wajen hadin salad ko ta nike su ta sanya cikin miyar taushe kamar yadda ake sa gyada, sai dai kada ta bari ya sha wuta sosai.
3. Cakulet: Tana dauke da sinadarin phenyl-ethylamine, wani sinadarin da yake haifar da nishadi da jin dadi cikin ma’aikatar hankali, irin jin dadin da masoya biyu kan ji farkon haduwarsu. Idan ma’aurata suka sha cakulet gab da gabatar da ibadar aure, za su samu karin so da karsashin ibadar auren dukkansu, wanda zai haifar da karin dandano da zakin ibadar auren gare su duka. Sai dai a kula, ba kowacce cakulet ce za a saya ba, sai a nemi wacce kokon (cocoa) da yake ciki ya fi dukkanin kayan da aka hada ta da su yawa. Yawanci wadanda suka fi yawa a kasuwanni da kantuna zaki ne ya fi yawa a cikinsu, wasu kuma sai a cika su da gyada ko wafa. Hanya mafi sauki ta sayen cakulet mai kyau sai mutum ya ce a nuna masa wadanda suka fi tsada, domin dai an ce araha ba ta ado. Sannan sai a sha ta a sannu musamman in mutum mai kiba ne domin tana dauke da sinadaran kara nauyin jiki.
4. kwan Salwa:Yana dauke da muhimman sinadaran gina jiki irin su Phosphorous, Proteins, and bitamin B da D da E, don haka yana matukar inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa.Sinadaran cikinsa suna kula da kuma zaburar da masarrafin maniyyi- Prostate gland. Yana kara karfin motsuwar sha’awa da kuma karin kuzarin sha’awa. Ana sarrafa shi don ci kamar yadda ake sarrafa kwan kaza, amma ya fi alfanu in aka sha shi yadda yake domin ba shi da wani karni ko wari mai sa tashin zuciya.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.