Tasirin Abinci Ga Ingancin Ibadar Aure (3)

Assalamu Alaikum, marhabin da sake haduwar mu a cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, domin inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin. 5. Waken suya: Da duk wani […]

Tasirin Abinci Ga Ingancin Ibadar Aure (3)
Tasirin Abinci Ga Ingancin Ibadar Aure (3)

Assalamu Alaikum, marhabin da sake haduwar mu a cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, domin inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

5. Waken suya: Da duk wani abin da aka hada da shi, irin su awara, madarar waken suya, da sauransu na inganta ma’aikatar sha’awar ‘ya mace musamman wajen tabbatar da isashhiyar lema a ‘yan matancinta domin yana dauke da sinadarin ‘Phytoestrogen’ wanda yake yanayi da sinadarin ‘yan matanci ‘estrogen’. Ga uwargidan da take fama da matsalar isasshiyar lema, sai ta rika shan kofi daya na madarar waken suya sau daya a rana, amma banda mai matsalar cutar daji domin akwai yuwuwar sinadaran cikin waken suyan ya sake dawo mata da ciwon. Maigida ya guji cin waken suya ko duk wani abu da aka hada da shi, sai dai in yana son rage sha’awarsa ne, domin wannan sinadari ‘phyto-estrogen’ yana dakile karfi da yalwar sinadarin mazantaka da sha’awa, watau ‘testosterone’.
6. Alayyahu: Yana dauke da sinadarin ‘Magnesium’ wanda yake taimakawa wajen bayar da lafiyayyar iska ga jijiyoyin al’aura, kuma yana saukar da natsuwa ga mata, musamman lokacin ibadar aure. Hakan nan kuma alayyahu da kabeji da ganyayyaki ire-irensu na dauke da sinadarin ‘indole-3’ wanda yake rage yawan sinadarin ‘oestrogen’ ga maza don haka sai ‘testosteron’ ya samu karuwa, kuma suna kara yawan ‘oestrogen’ ga mata.
7. Ayaba: Tana da yalwar sinadarin ‘potassium’ da kuma bitamin B mai rassa da kuma sinadarin ‘bromelain’ wadanda duk suna taimakawa wajen inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa da kara mata gudu.
8. baure: Yana cike da sinadaran ‘amino acid’wanda suke da alfanu wajen kara motsuwar sha’awa da kara mata karfi ga duka maza da mata.
9.Tafarnuwa: Tana dauke da sinadarin‘Allicin’ wanda yake taimakawa wajen malalar da jini ga jijiyoyin al’aura, ta fi alfanu in aka hadiye ta danyarta, amma sai a san lokaci mafi dacewa na cinta domin tana sa warin jiki da na baki, idan mutum na warin tafarnuwa ko albasa kuwa, mala’ikun rahama ba sa kusantarsa.
10. Alkama: Idan aka barza ta da kwansonta, aka yi fate-fate ko kunun ta, ita ma tana kara karfin sha’awa, domin tana dauke da sinadarin ‘L-arginine’ wanda yake zaburar da samar da sinadarin ‘Nitric Odide’ wanda yake kula da zagayawar jini a cikin jiki.Kuma yana sa jijiyoyin ibadar aure su bude su cika da jini sosai. Wannan yana tabbatar da ingancin ibadar auren. Yazawa ma tana dauke da wannan sinadari mai alfanu.
11. Hatsi: Irin su masara, gero, dawa da sauransu idan aka sarrafa su da kwansonsu, suna kunshe da sinadaran kara lafiyar sha’awa da ma lafiyar jiki duka. Don haka tuwom datsa ya fi tuwon surfaffiyar masara kara lafiya da inganta sha’awa.Haka ma shinkafa ‘yar gida ta Hausa ta fi shinkafar Bature ko shinkafar tuwo, domin tana dauke da sinadarin ‘zinc’, daya daga cikin sinadarai masu alfanu ga ma’aikatar sha’awa.
12. Barkono: Yana dauke da sinadarin ‘capsaicin’ wanda yake dumama jini don haka sai ya rika malala nan da nan cikin jini. Haka kuma wannan sinadari yana sa kwakwalwa ta saki sinadaran nishadi (endorphins) cikin jini.
13. Zogale: Binciken kimiyya ya tabbatar ba wani abinci da yake inganta lafiyar jikin dan adam da kuma bayar da waraka ga cututtuka daban-daban irin zogale, akwai matukar mamaki ga irin sinadaran karin lafiya da kuzarin da ke tattare da wannan ganye wanda zano su a nan zai dauki lokaci, don haka sai dai in ce da ma’aurata a durfafi cin zogale ka’in da na’in don samun lafiyayyar sha’awa, lafiyayyen jiki da lafiyayyen kuzari. Uwargida ta busar da danyen zogale, ta daka ta tankade sai ta rika barbada shi ga duk abinci har da na yara.Ana iya gauraya shi da zuma a sha, ko da madara, koko ko nono da ma duk kowane irin abinci. Sannan a nemi man sa a rika amfani da shi dai-dai bukata. Don karin karfin kuzari da motsuwar sha’awa kuwa, uwargida sai ta sami barankacen ‘ya’yan zogalen hade da furensa, sai ta dan yi farfesunsu sama-sama, kar su sha wuta sosai, sai ku ci tare da maigida, tare da shanye romon duka.
Sauran wasu nau’ukan abincin masu kara sha’awa sun hada da citta da zuma da madara da dabino da aya da karas da dukkan kayan marmari da ganyayyaki.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.