Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi (2)

  Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  Bayan haka, mun kwana a […]

Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi (2)
Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi (2)

 

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Bayan haka, mun kwana a karkashin bayanin nau’in dabbobin Layya, muka ce lallai ne kowace dabbar Layya ta kasance lafiyayya, wadda ba ta da kowace bayyanannar nakasa, to ga ci gaba:
Kodayake Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fadi aibi hudu ne a fili, Jamhurun (mafi rijayen) Malamai, sun tafi a kan ana iya kiyasin wadansu aibobi dangane da rashin lafiya da makamantansa.
Barra’u dan Aazib (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya mike cikinmu ya ce, “Hudun (halaye da kamanni a cikin dabbar Layya) ba su ingantar da Layya. (Wadannan halaye su ne):  Makanta (ko da ta gefe daya ce); rashin lafiya (bayyananne); gurgunta (bayyananna, mai hana tafiya); tsufa (wadda ta tsotse ba maiko da bargo a jikinta).”  Imam Ahmad da wasu hudu (As’habus Sunan) suka ruwaito wannan Hadisi.  Imamu Tirmiziy da Ibnu Hibban da Hakim suka inganta shi.
Ana iya yanka rago dan wata shida lafiyayye, kosasshe, idan ana cikin matsi, saboda haka ke nan wanda ya shekara shi ne wanda ake bukata.  Tunkiya da bunsuru da akuya, dole sai sun cika shekara guda cif da abin da ya wuce haka. Shanu kuwa sai sun kai shekara biyu, sun shiga ta uku. Rakuma sai sun kai shekara biyar sun shiga ta shida. Duk ana yanka su ne bayan an kare Sallar Idi. Wuraren da ba su Sallar Idi, wato mazauna daji, sai su yi hasashen lokacin kammalawa a birane, sannan su yanka. (Muslim, Hadisi na 1,963 da Tirmizi, a cikin littafin Assunan, mujalladi na 4, Hadisi na 194 da Ibnu Abdulbarr a cikin littafin Attamhid, mujalladi na 23, Hadisi na 185 da kuma littafin Almabsud, mujalladi na 12, shafi na 9 da Almudawwana, mujalladi na 2, shafi na 2 da Alhawiy, mujalladi na 19, shafi na 89 da kuma Almughniy, mujalladi na 9, shafi na 348).
Ya fi kyau mutum ya yanka Layyarsa da kansa don koyi da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) saboda shi Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi da kansa ne.
Ana son mutum ya fara ci daga naman Layyarsa, bayan ya dawo daga Sallar Idi, kuma ya yi yankan. An fi so ya raba naman Layya gida uku: ya ci; ya sadaukar; ya yi kyauta ga masu ziyartarsa. Idan ya cinye duka shi da iyalinsa, daidai ne.  dan ya sadaukar duka daidai ne. Allah Shi ne Mafi sani.
Sallar Idi da abin da ya rataya da ita:
An son mutum ya yi wanka, a safiyar Ranar Sallah (wato 10 ga watan Zul-Hajji ke nan), sannan ya sanya tufa sabuwa in da hali. Kuma in babu halin sabuwa, sai a samu wankakkiya mai kyau mai tsabta. Ya sa turare in ya samu. Ya fita daga gida a kafa ko a kan abin hawa kowane iri, alhali yana kabbarbari, har zuwa filin Idin, ya zauna ya jira zuwan liman. Ba zai yi nafila ba, domin ita kanta Sallar Idin a matsayin nafila take. Zai yi ta fadin dayan biyun kabbarbari ko kuma ya rika musanyawa, lokaci bayan lokaci. Yana cewa: “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Ko kuma “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La’ilaha illallah!!! Allahu Akbar! Wallahu Akbar!! Walillahil hamd!!!”  Haka zai yi ta yi, har liman ya zo a tayar da Sallah.
Akwai muhimmanci kwarai a zauna cikin natsuwa a saurari hudubar liman, bayan an kammala sallar, matukar ba wata lalura. Wanda bai samu Sallah cikin jama’a bayan liman ba, yana iya yi shi kadai.  Raka’a biyu ce. Ta farko zai yi kabbara bakwai tare da ta harama; sannan ya karanta Fatiha da Sura. Ta biyu zai yi kabbara shida tare da wadda ya mike, wato in yana tsaye kyam, zai yi kabbara biyar, kafin ya karanta Fatiha da Sura. Ya kammala Sallah, ya yi tahiyya, ya yi sallama.
Bayan wannan ne ake yanka Layya. A ziyarci ’yan uwa da abokan arziki, a taya juna murna da fatar alheri.  
Sannan a ranar ne dai daga Sallar Azahar, a mazhabar Malikiyya, mutum zai ci gaba da yin irin wadancan kabbarbari da suka gabata, a bayan kowace sallar farilla har sai ya samu salloli goma sha biyar. Ke nan zai soma, kamar yadda ya gabata, daga bayan Sallar Azahar ta Ranar Sallah, sannan ya kammala bayan Sallar Asuba ta ranar 13 ga wata. Wato ga 4 na Ranar Sallah; ga 5 ranar 11 ga wata; ga 5 ranar 12 ga wata; sannan sai bayan Sallar Asubar ranar 13 ga wata. Allah Ya karba mana ibadarmu, amin.
Waiwaye:  Da yake yau (Jumu’a 18 ga Satumba, 2015) wuni na hudu ke nan muke ciki, yana da kyau mu kara jan hankalin mai karatu kan muhimmancin yin zikirori a cikin wadannan kwanaki da sadaka da nafilfilin Sallah da yawaita kabbarbari da karatun Alkur’ani da karin kyautata wa iyaye da kokarin sadar da zumunta da dai kyautata wa sauran abokan halitta (mutane da dabbobi da tsuntsaye) da kara wa makwabtaka armashi da sauran kyawawan ayyukan alheri wadanda ba su lissaftuwa a nan.
Wannan ya nuna wanda bai samu damar yin azumi ba, yana da damar samun wasu alherai masu yawa da zai iya yi, idan ya mayar da hankali kan sauran ayyukan alherin da aka jero ko waninsu. Allah Ya ba mu dacewa da duk abin da yake daidai.  
Har wa yau dai sai a yawaita addu’o’in fatar alheri ga kanmu da kasarmu da shugabanninmu masu son kawo gyara cikin al’amuranmu na rayuwa, musamman ma dai a dage kan haka a Ranar Arafa domin Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Mafi alherin addu’a (ita ce) addu’ar Ranar Arafa. Mafi alherin abin da na fada, ni da annabawan da suke gabanina (shi ne) ‘La’ilaha illallahu wahdahu la sharikalahu lahul mulku walahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir.”  Imam Tirmizi ne ya ruwaito shi daga Amru dan Shu’aibu daga babansa daga kakansa, (Allah Ya yarda da su). Imam Malik ma ya fitar da shi a cikin Muwadda dinsa da isnadi mursal.
Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da shi), yakan yi kabbara a cikin kubbarsa a Mina, ta yadda mutanen masallaci za su ji, su ma su amsa, sannan mutanen waje su karba su ma, har ta yadda Minna za ta yi gumji saboda kabbarbarin.
Haka nan dai Umar dan Khaddab da Abu Huraira, (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna zuwa kasuwa su yi kabbara, mutanen kasuwa kuma su amsa da kabbarbari su ma, duk dai a cikin wadannan kwanaki goma. (Al’azkar, shafi na 174).
Za mu takaita a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu da fata Allah Ya sa mu yi Idi da Layya lafiya.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!