Tasirin tambaya da amsa a rayuwa 1
Allah cikin ikonSa, yau ma Ya kara ba mu dama mun kawo wannan lokaci, kuma da karfin ikonSa marar iyaka, Ya nufe mu da sake saduwa cikin wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Dama Shi ne mai kaga rayuwa kuma Yake mata adadin iyakarta. Da ikonSa ne kuma muke sarrafa rayuwar tamu domin ta amfane […]
Allah cikin ikonSa, yau ma Ya kara ba mu dama mun kawo wannan lokaci, kuma da karfin ikonSa marar iyaka, Ya nufe mu da sake saduwa cikin wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Dama Shi ne mai kaga rayuwa kuma Yake mata adadin iyakarta. Da ikonSa ne kuma muke sarrafa rayuwar tamu domin ta amfane mu a nan duniya, ga mai yawan rabo, kuma ta amfane shi a gobe kiyama. Allah Ya sanya muna cikin masu dacewa da gwabin rayuwa a nan da can, amin. Ina yi maku sallama, Assalamu alaikum!
Yau kuma ga mu da wani sabon maudu’in, wanda zai caza mana kwakwalwa, domin mu sake daidaituwa bisa neman kyautata rayuwarmu.
Tambaya, tambaya, tambaya… abin da ya kamata mu koyi yi wa kawunanmu ke nan, sannan kuma mu koyi azama da kokari wajen nemo amsoshinsu.
Misali, ni kuwa ai dan Adam ne, to me ya sanya ma na zo nan duniyar? Tambaya ta daya ke nan, to yi kokarin gano amsarta, idan ka gano sai ka sanya sakamakon cikin rayuwarka. Idan ka gano dalilin halittarka da kuma dalilin zuwan ka duniya, to sai ka bi wannan dalili ba tare da ka karkace hanya ba. Har kullum idan mutum ya san dalilin gudanar da wani abu, wannan zai ba shi damar maida hankali kansa ko kuma ya wulakantar da shi.
Na wayi gari, tun ina yaro ake maganar ilimi, ilimi, ilimi, me ya sanya zan nemi ilimi, kuma wane irin ilimi ya kamata in nema? Idan ma na samu ilimin me zan yi da shi? Wadannan tambayoyi ma suna da muhimmanci, musamman idan ka yi kokarin gano amsoshinsu daya bayan daya. Akwai bukatar lallai mutum ya gane cewa ilimin nan dai shi ne mutum, kuma shi ne rayuwar duniya da kuma ta gobe. Idan mutum ya yi wasa da shi, to babu shakka zai zama titibiri duk iyakar rayuwarsa ta yau da kullum.
Neman abinci, cin abinci, maganar ke nan har kullum. To wane irin abinci ya kamata in nema, kuma yaya zan yi amfani da shi? Tambayoyi ne da ya kamata mu rika yi wa kawunanmu, sannan kuma mu amsa su. Nan za mu gane hanyoyin da suka dace mu bi domin neman abincin da kuma yadda za mu ci, idan mun samo. Abin sani ne cewa, duk rayuwar dan Adam na zagaye ne wajen neman abinci, don haka kowa ka gani, yaro da babba, mace da namiji, alkiblarsa ke nan. Wannan dalili ne ya sanya ake samun karo ko kuma cudedeniya da juna wajen nemansa. Inda za a samu sauki shi ne, idan mutum ya koyi ilimin neman abincin, kuma ya nemi hanyoyin da suka dace ya same shi, babu shakka zai samu wanyewa lafiya da sauran jama’a da su ma suke kokowar neman nasu abincin. Sanin ilimin neman abincin kuma zai ba mutum damar sanin iyakar lokacin da ya kamata ya tsaya ko ya huta. Haka za ta ba shi damar daina yin hadama da handama da babakere. In ba haka ba, me ke kawo karo da fada, sai hadamar wasu da ke babbake da wawure abincin mutum dubu su kadai. Ga dubbai na jin yunwa, kai kadai ka mallake abincin miliyoyin mutane, ko kuma ka sanya kandagarki ga wasu don kada su isa ga abincinsu. Ina ganin idan mutum ya amsa wadannan tambayoyi na sama, to zai iya sanin dalilinsa na neman abincin da kuma abin da ya kamata ya ci. Idan ya samu rara kuma, amsoshin tambayoyinsa za su ba shi ilimin sanin abin da ya kamata ya yi da shi.
Na wayi gari na gan ni ina rayuwa cikin mutane, maza da mata, yara da manya da tsararrakina. To me ya sanya ba na rayuwa ni kadai? Da wa ya kamata in zauna, kuma wace irin alaka ko dangantaka ya kamata in yi da wane ko wance? Duk wadannan tambayoyi abin tambaya ne kuma mu yi kokarin gano amsoshinsu. Akwai sirrin rayuwa mai yawa ga mutum idan ya tambayi kansa wadannan tambayoyi, musamman kuma idan ya gano amsoshinsu kamar yadda na ba da shawara a sama. Idan ka san matsayin mutum a kanka, kuma ka san alakarka da shi ko da ita, sannan ka san abin da ya kamata ka yi da shi ko ita. Wannan zai ba ka damar gudanar da rayuwarka ta yin taka-tsan-tsan da duk wani taku na wani ko wata. Wannan kuma zai ba ka damar kauce wa da-na-sani cikin al’amuranka na rayuwa. Domin babu abin da ya kai mutum wahalar fahimta, duk kuwa da cewa ana zaune tattare. Mafi yawan lokaci kuma, irin wannan shu’umanci
na dan Adam ne ke jawo rashin fahimta da sabani da juna; wanda babu shakka haka ke kawo hatsaniya da rashin kwanciyar hankali cikin al’umma. Idan haka ta faru kuwa, sai ka ga an samu rashin sukuni da rashin natsuwa a rayuwar mutum ta yau da kullum. Don haka mu yi wa kanmu tambayoyi kan rayuwa, sai mu gano inda za mu da inda muka dawo.
Siyasa, mulki, sarauta, na dade ina jin wadannan kalmomi, har kuma na zo na fara gane tasirinsu da yadda ake samun su. To, mu tambayi kawunanmu, mece ce siyasa, mene ne mulki ko mukami, kuma ta yaya ake samun su su tabbata? Wane ne da wane ne ya kamata su mulke mu, kuma saboda me? Idan sun mulke mu din, me ya kamata su rika yi, ni kuma a matsayina na mabiyi, me ya kamata in rika yi don kare muradin rayuwata da ta ta’allaka da mulkin ko mai mulkin? Yin wadannan tambayoyi da amsa su, za su sake canzawa da kaifafa mana tunani, sannan kuma su ba mu damar gane abin da muke ciki a rayuwa, kamar kuma yadda za mu gane abin da zai amfane mu ta fuskar mulki da mai mulkin. Idan kowa ya san wannan, dada babu sauran ka-ce-na-ce ke nan, sai kowa ya fuskanci abin da ya kamata da shi. Mai mulki ya tsaya kan mulkinsa kamar yadda ya san abin da ya dace ya aiwatar, talaka, sai ya tsaya a matsayinsa na talaka, kuma ya gudanar da rayuwarsa kamar yadda ya dace. Idan haka ta samu, an samu damar ba kowa hakkinsa ke nan ta wannan fuska. Kuma haka za ta sanya kowa zai tsaya matsayinsa, ba tare da ya shiga hakkin wani ko wata ba.
Babbar fa’idar da muke son nunawa a nan ita ce, kada mu zauna haka nan sasakai a rayuwa, mu koyi cusa wa kawunanmu tambayoyi kan dukkan al’amuran rayuwa. Domin kuwa babu wani abu da ya kasance a duniyar nan ba tare da wani dalili ba. Sanin wannan dalili gare ka shi ne ilimi, kuma da shi za ka yi amfani domin girbar ribar wani al’amari, ko kuma ka guje masa idan mai cutar da kai ne. Idan ba ka san haka ba fa, lallai za ka kasance cikin duhun rayuwa. Duhu kuwa jahilci ne, bata ne kuma talauci ne. Don haka mu yi tambaya, tambaya, tambaya!
Dausayin kauna
kalubale, matsala ko cikas da muke fuskanta a harkar soyayya (2)
A mako na biyu da shiga sabon maudu’inmu, za mu fara ne da sakon Hafsat C. Ahmad Bungudu, 08140234726 da ke cewa: “Ina maku gaisuwa tare da fatan alheri. A hakikanin gaskiya ni ma na fuskanci matsalar soyayya a rayuwa, lokacin da aka hana ni auren wanda nake so. A karo na biyu na tsinci kaina a cikin soyayyar wanda bai ma san ina yi ba. Lallai sai a lokacin na san cewa ana fuskantar matsalar soyayya a rayuwa.”
Haka ne Hafsatu, lallai kam ana fuskantar matsalolin soyayya, doming a shi ke ma kin zama shaida. Allah Ya huwace, amin. – FDk.
Sai kuma sakon S. Kulele Zone5 Abuja, 08029148415: “Dausayin kauna FDk, kun sosa mani inda yake mani kaikai, don haka ba zan manta da wata yarinya da ta ci amanata ba saboda ta yaudare ni, ta ce ba wanda za ta aura sai ni. Sai da muka yi wata uku da ita muna soyayya da ita sai wata kawarta ta ce: ‘mani saura mako daya aurenta, da ma ba sonka take ba, abin hannunka take so.’ Don haka ba zan manta da wannan lokacin ba. FDk don Allah a fada wa masu halin nan da su ji tsoron gamuwarsu da Allah, su daina.”
Sako daga Abubakar Pele Sheka Kano, 08114677776 yana cewa: “FDk, na samu matsala sosai. Na kasance ina da budurwa, mun kai shekara uku muna tare har iyayena sun je sun yi magana a gidansu. Akwai wata da muke tare da ita a makaranta, ita kuma babu wanda take so sai ni. Na gaya mata akwai wadda muka yi maganar aure da ita, ta ce ita babu ruwanta, ta yi mani rantsuwa cewa babu wani namiji da za ta iya aura sai ni. Ta kara yi mani rantsuwa da cewa idan ban aure ta ba, ba za ta taba bari na na yi aure ba kuma za ta bar gidansu kuma idan ta bar gidan daga ni har iyayenta ba za mu kara ganin ta ba. Ta ce duniya za ta shiga.”
Laifi yana wurinka, domin ka san za ka auri wata kuma ka shiga soyayya da wata a makaranta? Ta ce wai za ta bar gidansu, to ta yaya za ta hana ka auren ke nan, kamar yadda ta ce da farko? Ina kira ga yarinyar nan da ta yi hakuri da kai, domin ko ta aure ka ba za ta samu farin ciki ba, tun da ba son ta kake da gaskiya ba, kasancewar ka shirya aure da wata ba ita ba.” FDk.
Ita kuwa Aisha Abubakar Jos, 08132897515 tana cewa: “Assalamu alaikum FDk da fatan kana lafiya. Ni dai ina tare da masoyina muna soyayya, wata rana sai ya zo wai yana so mu rabu. Na ce saboda me? Ya ce haka kawai, sai na ce Allah Ya sa haka shi ne mafi alheri. Kwana kadan sai na ji ya kai sadakin kawata Shafa’atu. Ashe Allah ne Ya kare ni da sharrinsa, sai ji na yi ya yi mata ciki ya karbi sadakinsa. Dayake mahaukaci ne sai ya dawo gare ni, ni kuma lokacin na nuna kamar ban san yana yi ba saboda na samu wanda ya fi shi. To, maza ku ji tsoron Allah, ku sani cewa zina bibiya take yi; in ka yi wa na wani, za a yi wa naka.”
Daga Yusuf Ali Garba, 08067766767, yana cewa: “Mata mayaudara ne, mata akwai zamba cikin aminci; ba su da tunani. Islamiyyar da suke zuwa ba ta amfanar da su komai. Na so in gaya wa filin Dausayin kauna abin da ya faru da ni amma da na fara tunanin sai na ji hawaye na zubar mini tare da kunar zuciya. Nan gaba idan na samu sassauci a zuciyata, idan kuma FDk ya sake fidda irin wannan maudu’in, zan fada muku amma me ya sa mata suke son sa maza mawuyacin hali ne?”
Sai kuma Alhajin Dubai, Sardaunan Matasan Dala, 07038605362 da yake cewa: “FDk, ina fatan kana lafiya. Hakika na hadu da irin wadannan matsalolin da ka lissafa gaba dayansu. Sai da ta kai cewa na kauce wa soyyaya gaba daya. Yarinya ta karshe da muka rabu, ta zo mini da zancen cewa zan bar ta ta ci gaba da karatu, idan na yarda da hakan sai na turo a yi maganar aure, idan ban yarda ba to na rabu da ita. Bayan mun yi haka sai na kaurace mata, na ce ta je ta yi shawara, ni ma zanyi shawara a kan maganar da ta gaya mini. Koda na nemi shawarar, kowa cewa yake na rabu da ita. Bayan da na koma wurinta na tambaye ta, ko ta hakura da karatun? Ta ce ta hakura amma daga ba ya sai ta ce tana kan bakanta, idan ba zan yarda ba na zabi daya. Na ce na zabi rabuwa da ita. Bayan na kaurace wa soyyaya gaba daya, kwatsam sai na hadu da wata ’yar Aljanna. Cikin kwanaki 13 muka daidaita da ita, aka sa mana rana da ita. Sai na kai wa tsohuwar budurwar tawa ziyara don na ba ta katin sanya ranar nawa. Ina ba ta na juya na tafi, ban tsaya jin wata magana ba daga bakint. Bayan kwanaki sai na samu labarin kawarta ce take zuga ta a kan ta nemi cewa za ta yi karatu saboda a tunaninta ba zan iya rabuwa da ita ba kuma ta san cewa ina da tsananin kishi, wanda shi zai sa na hana ta karatun. Wai ma bayan karatun har aiki za ta nema. Yanzu maganar da take wai ni na bata mata lokaci. Na tabbata yanzu idan ta samu saurayi ba zata kuma tayin karatu ba.”
Sakon Aminu Fifa Jega, 08185890052 yana cewa: “FDk, ina neman makaranta Dausayi su taya ni addu’a, Allah Ya ba dan uwana lafiya. Dalili kuwa shi ne, wata yarinya ce ta ci amanarsa bayan ta yi alkawarin aurensa in har ya jira ta kare makaranta. Shi kuwa sai ya tsaya jiran sai da ta kare. Bayan ta kare yake mata maganar aure sai ta ce ita ba aure ne gabanta ba, ita sai wani lokaci in ba zai hakuri ba ya zo ga kayansa; ita yanzu gaskiya ba ta son sa, ga shi kuma shekarar su uku tare. A haka suka rabu, son ta da tunani suka yi masa yawa har ciwo ya kama shi.”