Tattaki don Buhari ya zama tattaka
Tun bayan da matashin nan mai suna, Sulaiman Hashim, ya tako da kafa daga birnin Legas zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja domin taya Janar Muhammadu Buhari murnar nasarar da ya samu a zaben watan Maris, ake ci gaba da samun jama’a wadanda ke bin sawunsa wajen yin tattakin daga garuruwa daban-daban zuwa wadansu domin taya […]

Tun bayan da matashin nan mai suna, Sulaiman Hashim, ya tako da kafa daga birnin Legas zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja domin taya Janar Muhammadu Buhari murnar nasarar da ya samu a zaben watan Maris, ake ci gaba da samun jama’a wadanda ke bin sawunsa wajen yin tattakin daga garuruwa daban-daban zuwa wadansu domin taya Buhari murna ko kuma Shugaba Goodluck Jonathan da wadansu ‘yan siyasa.
Akwai Oladele John Nihi wanda ya sha alwashin takawa da kafa daga Abuja zuwa Otuoke wato kauyen Shugaban kasa Mai barin gado, Goodluck Jonathan da ke Jihar Bayelsa. dan asalin Jihar Kogin ya fara tattakin da ya kai nisan Kilomita 700 ne a ranar Litinin, 4 ga wannan watan da misalin karfe shida na safe domin yaba wa da amsa shan kayin da Shugaba Jonathan ya yi. Ya ce: “Hakan ya ba Jonathan martabar zama gwarzon dimukradiyya.” Amma kwana biyu tsakani, sai Oladele ya samu wata mace wadda ta ce za ta raka shi zuwa kauyen na Otuoke . Matar mai suna Gloria ta fara jerawa da shi ne daga garin Abaji da ke Abuja.
Har ila yau, akwai Abubakar Umar wanda aka fi sani da sunan Duduwalle, shi ya niki gari da kafarsa daga garin Yola na Jihar Adamawa zuwa Abuja domin ya taya Janar Buhari murnar nasarar da ya samu a zabe.
Sai Hajiya Talatu wacce ita ce macen farko da take yi wa Janar din tattaki kuma ta taso ne daga Kaduna, inda take fatan isa Abuja .
Hakazalika, akwai Adamu Abdullahi mai shekara 45, ya fara tafiyarsa ne daga Maiduguri a ranar 30 ga watan jiya zuwa Abuja domin ya taya sabon shugaban murna.
Sai dalibin Jami’ar Bayero ta Kano, wato Haruna wanda ya fara taka sayyada daga Kano zuwa Abuja domin nuna rashin gamsuwarsa da sakamakon zaben Jihar Taraba. Kuma ya ce yana nuna goyon bayansa ne ga ’yar takarar jam’iyyar APC a zaben wato Hajiya Aisha Alhassan wadda ta sha kaye.
Daga garin Funtuwa na Jihar Katsina, an samu Nazifi Lawal da Ibrahim Sani wadanda suke nasu tattakin zuwa garin Yola saboda godiya da tsohon Maitaimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar bisa goyon bayan da ya bayar wajen tabbatar da rashin samun nasarar jam’iyyar PDP a zaben da ya wuce.
Daga nan sai wani matashi marar hannaye mai suna Musa Ibrahim, shi kuma ya yi tattaki ne daga Kaduna zuwa Abuja, inda yake fatan ganawa da Janar Buhari. Ya ce yana hakan ne domin ya isar da sakon nakasassu zuwa ga sabuwar gwamnatin.
Akwai kuma Musa Badawa da ke tattaki daga Jihar Kano zuwa Abuja domin Buhari, sai dai shi ba kamar sauran takwarorinsa ba, ya samu inshorar rai daga kamfanin sadarwa na Airtel.
Har ila yau, daga Jihar Taraba zuwa Bayelsa an samu Paul Tankwa da ke tattaki domin ya gabatar wa Shugaba Jonathan kambun girmamawa saboda amsa shan kaye.
Kodayake, Malam Kabiru Ja’afaru shi tuka kekensa ya yi tun daga Kaduna zuwa Legas domin ya jinjina wa al’ummar Yarabawa kan goyon bayan da suka bai wa Janar Muhammadu Buhari.
Ana cikin haka ne kuma, a ranar Litinin da ta gabata aka samu wasu mutum biyar da suka bayyana aniyyarsu ta isa birnin Makkah na kasar Saudiyya a kafa daga Jihar Bauchi domin godiya ga Ubangiji saboda nasarar da ya bai wa Janar Buhari da kuma yi masa addu’ar samun nasarar sauke nauyin bai wa kasar nan romon dimukradiyya. Mutane biyar din sun hada da: Abubakar Daguma da Abdullahi Hussaini da dahiru Aminu da Kabiru Saleh da kuma Muhammad Inuwa Yawale. Sun dai ce za su fara tafiyar ne kwana guda bayan rantsar da zababben shugaban wato ranar Asabar, 30 ga wannan watan nan.
Tattakin ya saba wa shari’a -Malamai
Aminiya ta tuntubi Sheikh dahiru Bauchi domin jin ta bakinsa game da yunkurin da wadannan matasa suka yin a takawa a kasa zuwa Saudiyya saboda Buhari, inda ya bayyana cewa,’’ na yi matukar farin ciki da wannan tambayar, hakika na samu labarin cewa wadansu za su je Saudiyya a kafa ranar da aka rantsar da Buhari a watau ranar juma’a. Annabi Muhammadu (SAW) ba ya son mutum ya dauki aikin ibada wanda zai wahalar da shi, komai ana son mutum ya yi daidai gwargwado.’’
Akwai wani mutum a zamanin Annabi da ya ce zai yi azumi amma ba zai shiga inuwa ba domin zama, sai Annabi ya ce masa ka ci gaba da yin azumi amma ka je ka zauna a inuwa. Kuma ya kamata a fahimci cewa akwai mota, akwai jirgin sama, saboda haka babu dalilin da zai sa mutum ya tafi da kafa.Tafiya da kafa akwai hadari, domin da yawa daga cikin kasashen Afirka suna fama da rikice-rikice, tun daga kan Sudan har zuwa sama, kuma Jihar Barno ana fama da ‘yan Boko Haram. Allah Ya fada a littafinsa kada mutum ya jefa kansa cikin halaka.
Malamin ya ci gaba da cewa, “Bayan haka akwai wurare da dama da za a binciki mutum wanda yake tafiya da kafa ko a mota, saboda haka ina bada shawara ga wadannan matasa su yi hakuri su fasa wannan tafiya. Kuma idan suka ce dole sai sun tafi da kafa ya ya za su tsallake ruwan Maliya? saboda haka su yi kaffara su fasa tafiyar.’’
Shehin ya kuma yi fatan idan Buhari ya kama aiki zai cika alkawuran da ya dauka na samar da zaman lafiya da murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram. ‘Labarin da muke samu ana cigaba da kai musu hare-hare a dajin Sambisa da ke Jihar Barno. Kuma muna fata sabuwar gwamnati za ta kawo karshen matsalar sace-sacen shanun Fulani da ake yi a sassa daban-daban na kudancin Najeriya har da wadansu jihohin Arewa maso gabas.’
Haka kuma Aminiya ta tuntubi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir, Mataimakin shugaban Majalisar Malamai na kasa na biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, inda ya bayyana cewa tafiye-tafiyen da wadansu suke yi don nuna murnar cin zaben Janar Buhari ya saba wa shari’a, yana mai nuni da cewa maimakon haka addu’a ya kamata al’ummar kasar nan su yi wa Janar Buhari.
Malamin ya ci gaba da cewa, ‘’Mun gode wa Allah da Ya kawo karshen wannan hali da muke ciki. Kuma mun gode maSa da Ya kaddare mu muka zabi Janar Muhammad Buhari. Lokacin da Janar Buhari ya samu wannan nasara, shugaban Majalisar Malamai na kasa na wannan kungiya, wato shugabanmu, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir kiran taron walima ya yi, ya yanka dabobi da kaji, ya sayo kayan marmari, jama’a suka taru aka ci aka sha. Shi da sauran malaman da suka halarci walimar aka yi jawaban godiya ga Allah tare da rokar wa Janar Buhari nasara. Irin wannan ya kamata al’ummar musulmi su yi, domin musulunci ya nuna cewa idan aka samu abin farin ciki a yi walima ne.’’
“Amma irin wannan tafiya da wadansu mutane suke yi daga wannan wuri zuwa wancan wuri za mu iya cewa kamar an shigo da siyasa ce ko neman kudi ne, ko kuma neman suna. Idan mutum na farko ya yi babu manufa, sauran da suka biyo baya za a iya cewa akwai manufa. Don watakila na farkon nan da ya yi, kamar yadda labari ya ishe mu, an yi masa bajinta. Watakila wannan bajinta da aka yi masa ita ce ta sanya wadansu suka ce bari su ma su yi. Wai a ce wannan tafiya da kafa har da mata ma? Kina mace ki tako da kafa a wannan hali da ake ciki a Nijeriya, ga ‘yan fade, ga barayi, ga ‘yan fashi da makami, ga masu tukin ganganci a kan hanyoyi.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’Ai idan kana son Janar Buhari walima ya kamata ka shirya. Idan ba ka da karfin shirya walima sai ka yi azumi ko ka yi Sallah ka roki Allah Ya bai wa Janar Buhari nasara, wannan shi ne ya dace.’’
Da Aminiya ta tambaye shi ko irin wannan tafiyar da ake yi don murnar cin zaben Janar Buhari ya saba wa shari’a? Sai ya ce,’Wannan ya saba wa shari’a, don babu wanda ake koyi da shi a musulunci wajen gudanar da irin wadannan tafiye-tafiye.’
Sheikh Sa’idu Jangir sai ya shawarci mutane su taimaka Buhari ya samu nasara ta hanyar yin gaskiya da rike amana da son juna. ‘’Ai shi Janar Buhari ya yi suna ne saboda gaskiyarsa, kowa ya san abubuwan da Janar Buhari ya yi a kasar nan. Wadannan abubuwa da Janar Buhari ya yi shi ne ya sanya a duk kasar nan, gabas da yamma da kudu da Arewa kowa yake cewa sai Janar Buhari.’’
A karshe, Sheikh Sa’idu ya shawarci Buhari ‘’ya fara duba matsalar tsaron da take damun kasar nan. Kuma ya mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa. Haka kuma ya yi kokari ya hada kan kasar nan. Hakazalika ya yi kokari ya gyara masana’antun da aka rurrufe a kasar nan. Kuma ya zabi mashawarta nagari.’’
“Wato zaben Janar Buhari alheri ne a Nijeriya, domin zabensa ya hada kan al’ummar kudanci da arewacin Nijeriya. Dalilin zaben nan an samu fahimtar juna a tsakanin arewaci da kudancin kasar nan.’’
Akwai amfani da kuma matsala -Likita
Aminiya ta kuma tuntubi Dokta Rilwan Muhammad wanda shi ne Sakataren gudanarwa na Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko a yankin birnin Tarayya Abuja, inda aka tambaye shi ko akwai wani illa da irin wannan tattakin ke jawowa? Sai ya ce,“Kasancewar yawancin masu wannan tafiyar matasa ne, to tamkar motsa jiki su ke yi, motsa jiki kuma abu ne mai kyau ga lafiyar mutum, kasancewar yana sanya jini ya rika gudana a kan tsari, ya magance kamuwa da ciwon zuciya, ya kuma kara wa mutum kuzari. Sai dai ga wanada bai saba motsa jiki ba sannan a lokaci guda ya ce zai fuskanci tafiya irin wannan, to zai ji jiki.’
Ya kara da cewa, “a cikin jiki akwai wani sinadari da ake kira Lactic Acid, wanda yake digowa a gabobin mutum idan ya motsa jiki a karo na farko ba wanda ke yi akai-akai ba, hakan zai jawo masa kasala ya ji jikinsa ya yi nauyi har ya ji bai sha’awar ci gaba da tafiya. A bangaren illolinta kuwa tafiya irin wannan idan zafin rana ya yi yawa, mutum zai iya fuskantar suma, haka nan idan sanyi ya yi yawa ko ruwan sama ya buge shi, to zai iya fuskantar cutar namoniya, idan ko iska ce mai dauke da kura zai iya kai shi ga cutar Asma. idan kuwa cizon sauro ne ka ga zai kai shi ga zazzabin Maleriya, ga kuma barazanar kamuwa da cututtuka masu yaduwa idan ya samu haduwa da masu cutar,” inji shi.