Tattakin Zariya: Ya zama dole a jajanta da tausaya majinyata da wadanda suka rasu
Lallai zuwa yanzu an yi addu’ar uku ga wadanda tashin hankalin bam ya tafi da rayukansu a ranar Juma’ar da ta gabata yayin tattaki zuwa Zariya. Maza, an jima da binne su. Mata an bar su da takaici da bakin cikin wannan rashi da aka yi musu. ’Ya’ya, an bar su da marainiyar zuciya […]
Lallai zuwa yanzu an yi addu’ar uku ga wadanda tashin hankalin bam ya tafi da rayukansu a ranar Juma’ar da ta gabata yayin tattaki zuwa Zariya. Maza, an jima da binne su. Mata an bar su da takaici da bakin cikin wannan rashi da aka yi musu. ’Ya’ya, an bar su da marainiyar zuciya mai suranta murmushin da ke fuskokin ubanninsu a lokacin suna raye. Abokai, an bar su cikin alhinin rashin aminan hira da shawarwari.Allah Ya jikansu, Ya yi musu rahama, Ya tallafa wa abin da suka bari.
Haka kuma wannan bam ya bar wasu a asibitoci kwankwance, suna jinyar radadin raunuka. Wasu karairayewa suka yi, wasu munanan raunuka suka ji; wasu sassan jiki suka rasa. Allah Ya ba su lafiya, Ya ganar da su.
Wannan mummunan harin ta’addanci ya nuna mana wani bangare da mu ’yan Adam ba mu cika kula da shi ba, yayin da muke gardandami a tsakaninmu, wato bangaren tausayi. Wannan tausayi ne ya sa akasarinmu, a nan duniyar Facebook muka yi ta yi wa juna jaje da ta’aziyya. Dukkanmu ba tare da la’akari da bambancin gari ko mazhaba ko akida ko kungiya ba, sai muka yi ta nuna alhini kan wannan aiki na ta’addanci ga wadanda abin ya rutsa da su.
Ashe ke nan, idan zafin kanmu da son gardandaminmu ba su hada kawunanmu don ci gabanmu ba, ashe dai tausayin juna irin na dan adamtaka zai iya. To kuwa madalla da haka!
A bayan wannan matashiya, wacce manufarta ke iya zama rufaffiya ga mai karatu zuwa yanzu, to kuma, in har ba a gaji ba, akwai bukatar kai hankula zuwa ga nazarin wasu shawarwari da wasu masu jaje da ta’aziyyar nan suka bayar. Yayin wannan nazari, kada a damu da salo ko sigar da aka bi wurin ba da shawarwarin, a kalli shawarwarin kawai da idanuwa na basira don ganin cewa ko akwai abin dauka a ciki.
Yawancin masu ba da shawara suna kallon cewa tattakin nan zuwa Zariya, koda ya kasance aikin lada ne a fahimtar masu yi, to fa bai kai matsayin wajibi ba. To kuma dukkan mazhabobi da akidun Musulunci sun yi tarayya a kan cewa, koda aiki ya zama wajibi a cikin addini, amma kuma sai ya zama akwai tunanin rayuka ko dukiyoyi za su salwanta yayin aikata shi, to lallai bai kamata a aikatan ba. Bare kuma wanda akwai kokwanton samun ladarsa a kashin kansa. Na’am, a Shi’a, akwai wasu ayyuka da Maraji’ai za su iya hana bin wannan ka’ida ta ‘Laa dharara walaa dhiraara’ saboda wata natija da su kadai ne ke iya hango hakan. To a nan, koda akwai barazanar salwantar rayuka, kamar tattakin da ake yi Karbala, za su ce a ci gaba da yi. Game da tattakin Zariya, sanannen abu ne cewa babu wannan sam-sam.
Tun kafin a kawo wannan lokaci na tattaki, Shugaban Harkatul Islamiyya Fee Najeriya, Sheikh Ibrahim Ya’akub Zakzaky, ya shaida wa duniya cewa za a kai wa mutanensa hari yayin tattakin. Mutane da dama, sun zaci Shehin Malamin zai hana mutanen nasa fitowa saboda wannan ilimi da ya zo masa tun da wuri, musamman da yake cewa shi ne kadai zai iya hana su, su hanu a cikin wannan duniyar. Amma ba a san dalilinsa ba, sai bai hana su din ba. Kuma cikin rashin sa’a, sai kuwa bam ya tashi kamar yadda ya fada. Rayuka 21 suka salwanta, yayin da kuma adadi mai yawa na matasa suka ji raunika. Sannan aka ci gaba da gudanar da wannan tattaki (aikin da ba Wajibi ba, ba Mustahabbi ba a cikin akidar Shi’a), tamkar ba jinane ne suka zuzzuba ba. Anya, an aminta hankali ya yi jagoranci a nan kuwa!?
Irin wannan kumaji da jin zabura don addini a aikin da a ita kanta akidar ta Shi’ar bai kai haddin mustahabbanci a cikinta ba, wani hankalin na ganin cewa, ina ma a ce, maimakon sanya wadannan matasa yin sa, me zai hana, a yi amfani da wannan jin kumaji da zabura tasu wurin sanya su, a misalance, su tattara koda Naira dari bibbiyu ne. Idan adadin masu tattakin ya kai mutum miliyan daya (wanda kuma ana tunanin ma sun zarce haka), to, sai a ce musu maimakon kudin guzurinku na tattaki, a wannan karon ku zauna a gida babu tattakin, amma ku kakkawo gudunmowar Naira dari bibbiyu cikin kudin guzurinku. Naira dari biyu sau miliyan daya zai ba da Naira miliyan dari biyu!
Sheikh Ibrahim Zakzaky zai iya amfani da wannan kudi wurin gina asibitin talakawa a Zariya, wanda zai dan taimaka wurin rage wahalar da mutanen Zariya da kewaye ke fuskanta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika. Sai ya sanya wa asibitin suna ASIBITIN HUSAIN (AS). Na tabbata, hakan zai fi soyuwa a zukatan akasarin mabiyansa da mutanen gari, kuma zai fi zama abin alfahari a wurin Imam Husain (AS). Kazalika shi ne zai zama karbabbe a wurin Allah da yardarSa.
In kuma tattakin ne dai dole ake bukatar yi, to maimakon wannan da ke da hadurra kuma bai da lada, to, a yi wanda akwai hujjar da za a kai gaban Allah mana. Wato a tattara kudi, a ba wasu kalilan don su je ziyarar inda kabarin Imam Husain (AS) yake. Sai a yi tarayya a cikin samun ladan.
Wannan dai, duk domin albarkacin zaman tare ne, cewa dukkanmu masu nasiha ne ga junanmu a kan abin da zai amfane mu a lahirarmu da kuma duniyarmu.
Allah Ya ba mu ikon aikata abin da Shi Yake so, ba wanda mu muke so ba.