Tattalin arziki: Ma’adanai za su iya maye gurbin man fetur – Minista
Ministan Tama da karama Musa Mohammed Sada y ace ma’adanai za sum aye gurbin mai wajen samar da kudin shiga ga kasar nan, musamman idan aka yi la’akari da cewa akwai ma’adanai zube birjik a ko’ina a kasar nan. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi yayin taron masu hakar ma’adanai […]
Ministan Tama da karama Musa Mohammed Sada y ace ma’adanai za sum aye gurbin mai wajen samar da kudin shiga ga kasar nan, musamman idan aka yi la’akari da cewa akwai ma’adanai zube birjik a ko’ina a kasar nan.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi yayin taron masu hakar ma’adanai a Jos a ranar Talata.
Ministan wanda Darakta a ma’aikatar ma’adanai ta tarayya Mista Patrick Ojeka ya wakilta ya ce: “Wannan taron da kuma horarwa suna daga cikin ayyukan bunkasa tattalin arzikin kasar nan da Shugaba Goodluck Jonathan ya sanya a gaba, wato a bunkasa tattalin arziki ta hanyar kirkiro sababbin hanyoyi daban-daban.”
“Ma’adanai za su bada babbar gudunmuwa wajen bunkasa tattalin arziki, kai idan aka ba su muhimmanci za su iya maye gurbin mai, wannan shi ne babban dalilin da ya sa aka shirya wannan horarwar da kuma taron. A yanzu tattalin arzikin kasar nan ya shiga cikin mawuyacin hali, ya zama dole a samar da wata hanya da za ta ceto shi.”