Tattalin arziki yana cikin matsala

Tsada ta karu, kudin shiga ya ragu Farashin shinkafa da sukari sun yi tashin gwauron zabo kwararru sun fadi mafita Muna bakin kokarinmu- Gwamnati Tattalin arzikin Najeriya ya fada cikin matsala sakamakon yadda karfin arzikin kasar (GDP) ya yi kasa da kashi 2 da digo 06 a rubu’i na biyu na shekarar 2016.Ana jingina shiga […]

Tattalin arziki yana cikin matsala
Tattalin arziki yana cikin matsala

  • Tsada ta karu, kudin shiga ya ragu
  • Farashin shinkafa da sukari sun yi tashin gwauron zabo
  • kwararru sun fadi mafita
  • Muna bakin kokarinmu- Gwamnati

Tattalin arzikin Najeriya ya fada cikin matsala sakamakon yadda karfin arzikin kasar (GDP) ya yi kasa da kashi 2 da digo 06 a rubu’i na biyu na shekarar 2016.
Ana jingina shiga matsalar kan ci gaba da faduwar darajar farashin man fetur a kasuwar duniya da yadda hare-haren da ake kai wa bututun mai a yankin Neja-Delta suke kawo cikas ga samar da man a kasar nan.
Farashin mai ya fado kasa warwas daga Dala 100 kan kowace ganga a shekarar 2014 zuwa kasa da Dala 50 a yanzu, yayin da ’yan ta’addana Neja-Delta suka jawo hako man ya yi kasa daga ganga miliyan 2 da dubu 400 zuwa ganga miliyan 1 da dubu 600 a kullum.
Rahoton kudin shiga na kasa na rubu’i na biyu na bana da Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a shekaranjiya Laraba, ya nuna cewa kudin shigar kasa ya yi fadi da kashi 1 da maki 70 na bunkasar da yake yi na kasha 0.36 da aka samu a farkon watanni ukun bana.
Idan aka nazarci nazarin za a ga cewa an samu koma-baya zuwa kashi 2 da maki 32 a rubu’i na biyu na wannan shekara wanda ya gaza kashi 4 da maki 41 na bunkasar da aka samu ta kashi 2 da digo 35 a irin wannan lokaci a bara.
Rahoton na Hukumar NBS ya ce idan aka auna farashin kaya da kudin shigar kasar nan na Naira tiriliyan 23 da biliyan 480 a rubu’i na biyu na bana, za a ga ya cira sama daga Naira tiriliyan 22 da biliyan 300 a wannan rubu’in, alhali hakikanin kudin shiga yana Naira tiriliyan 16 da biliyan 100, wanda shi ma ya cira sama daga Naira tiriliyan 15 da biliyan 900 idan aka kwatanta da rubu’in farko na shekarar.
A cewar wani farfesan tattalin arziki kuma Darakta Janar na Cibiyar Kula da Kudi da Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma da ke Legas, Farfesa Akpan Hogan Ekpo, hanya mafi sauri da za a fice daga wannan matsala ita ce a zuba kudi a cikin tsarin.
 Ya ce, Shugaban kasa yana da zabin karbo bashin kudi daga ciki da wajen kasar nan ko ya zuba kudaden da aka kwato a cikin harkokin tattalin arziki kafin matsalar ta kai magaryar tukewa.
Farfesa Ekpo wanda yake cikin kwararrun da fadar Shugaban kasa ta gayata a kwanakin baya domin tsara hanyar fita daga wannan hali ya ce: Hanya daya da za a bi a farfado da tattalin arzikin it ace a sako kudi domin gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma manyan ayyuka kuma a yi wani tsari na tallafa wa jihohi su biya albashin da ma’aikata suke bin su bashi.”
Ya kara da cewa wannan nau’i na matsalar tattalin arziki ya yi muni ne saboda manyan sassa kamar na ayyuka da masana’antu suna macewa sosai, don haka akwai bukatar gwamnati ta yi dukkan abin da za ta iya yi wajen samar da yanayin da za a magance matsalar wutar lantarki da samar da basussuka masu sauki ga kamfanonin da suke bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.
Kuma ya bukaci Babban Bankin Najeriya ya hanzarta yin gyara ga tsarin bayar da bashi wajen rage kudin ruwan da ake cajar masu masana’antu domin su rika samun basussukan cikin sauki.
Game da tsarin kudi Farfesa Ekpo ya ce a daina kara kudin haraji a kan talakawa, maimakon haka gwamnati ta kara haraji ga masu hannu da shuni ta hanyar fito da harajin kayayyakin jin dadi da na alatu kuma ta dakile shigo da irin wadannan kayayyaki daga kasashen waje, domin a adana kudaden musayar da kasar nan ke samu.
Shi ma wani Malami a sashin Ilimin Tsimi Da Tanadi a Jami’ar Jihar Kaduna, Dokta Aminu Usman ya ce, rahoton baya-bayan nan na nuna cewa tattalin arzikin yana fuskantar wasu matsaloli a sakamakon faduwar farashin danyen mai da kuma hako shi.
Dokta Usman ya shaida wa Aminiya cewa, faduwar farashin man ya kamata a ce ya taimaka wa Najeriya ta juya akalar tattalin arzikinta zuwa wasu bangarorin da za su habaka shi amma maimakon haka sai ga shi yana kara tabarbarewa; wanda haka ke nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan gaugawar ceto shi fiye da matakan da take dauka a yanzu.
Da ya juya kan yadda ake ta samun hauhawar farashin kayan masarufi kuwa, Dokta Usman ya ce al’amarin yana da ban takaici, musamman kuma ganin cewa akwai karancin kudi a hannun mutane. “Hauhawar farashin kaya ya karya darajar kudin da mutane ke samu, a bangare daya kuma ga rashin aikin yi, wanda ke kara haifar da karancin saye-da-sayarwa tsakanin al’umma.” Inji shi.
Ya bayyana cewa yadda ake ta rufe kamfanoni, shi ya ta’azzara yawan rashin aikin yi a kasar nan. Don haka ya shawarci gwamnati da ta fito da dabarun da za su karfafa da habaka tattalin arzikin cikin kasa. “Wani mataki da ya kamata a dauka shi ne, gwamnati ta fara biyan bashin ’yan kwangila na gida sannan ta fara fitar da sabbin ayyukan bunkasa karkara domin a farfado da tattalin arzikin karkara, wanda shi zai samar da kasuwa ga manoma da kuma kayan da kamfanonin gida ke sarrafawa. Biyan bashin ’yan kwangilar waje, zai kara matsalar da ta shafi canjin kudi ne kawai.” Inji masanin.
Shi kuwa jami’in gudanar da cibiyar bin kadin al’amuran tattalin arziki a Afirika ta yamma (OSIWA), Joseph Idahosa Amenaghawon, ya bayyana wa Aminiya cewa, wannan rahoto da aka fitar dangane da tattalin arzikin Najeriya na nufin cewa lallai kasar na cikin matsalar tattalin arziki.
“Ga dukkan alamu dai muna ci gaba da kokari domin ganin an samo dubaru da hanyoyin shawo kan matsin tattalin arzikin da muke fuskanta.” Inji shi.
Shi ma Daraktan gudanarwa na Cibiyar tsara kyakyawan shugabanci da cigaba, Dakta Otibe Igbuzor, ya bayyana cewa halin da aka shiga na tattalin arziki ya tabbatar da cewa lallai Najeriya ta fada matsala kuma tattalin arzikinta na kara tabarbarewa.
 ‘’A ganina,abubuwa biyu ne muhimmai wannan rahoton ya nuna,na farko shi ne cewa lallai muna cikin matsala, na biyu, ya nuna cewa tattalin arziki ya shiga cikin wani mawuyacion hali ta yadda ake samun karuwar hauhawar farashi da kuma rashin ci gaban tattalin arziki.’’
Igbuzor ya bayyana wa Aminiya cewa,lallai tattalin arzikin Najeriya na kara tabarbarewa kuma hakan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da abin da yake faruwa a kullum.
Muna iyakar kokarinmu  – Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa tana da sauran aiki da yawa wurin magance tattalin arziki.
Ministan kudi, Kemi Adeosun ce ta sanar wa manema labarai hakan bayan taron majalisar ministoci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Ministar ta ce wannan shi ne lokaci mafi tsanani ga wannan kasar, sannan ta ce gwamnatin tarayya ba za ta yaudari kanta ba wurin cewa komai na tafiya yadda ya kamata.
Sai dai ta tabbatar da cewa, duk da cewa lokacin ya zo da rudani da yawa, gwamnati a shirye take wurin magance duk wata matsala da ke faruwa.
Ministar ta kara da cewa, idan ‘yan Najeriya suk ayi hakuri har wannan lokacin ya wuce, kasar nan za ta gyaru kuma kowa zai ji dadi.
Ta ce, tattalin arzikin Najeriya ba zai cigaba ba matukar Najeriya ta cigaba da dogaro da man fetur, domin kuwa farashin man da kuma hako shi yana kara zuwa kasa ne, sannan ta ce ya kamata ne a bunkasa wadansu bangarorin.
Da take amsa tambayoyi game da bayanan da hukumar bayanan da Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar inda ta ce tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali, Adeosun ta ce, “ wannan shi ne lokaci mafi wahala, amma za mu yi maganin matsalar. Yadda za mu yi shi ne, na daya za mu canja yanayin tattalin arzikin ta hanyar bunkasa wadansu bangarorin tatalin arziki, sannan zas mu rage dogaro da man fetur. Mun san abin da muke fitarwa, rikicin tsagerun Neja Delta ya jawo mana koma-baya a harkar kudin shiga na kasa baki daya domin dogaron da muka yi da bangaren man fetur, duk da cewa kashi 87 na kudin shigarmu yanzu ba daga man fetur ba ne, don haka ya kamata ne mu bunkkasa wadannan bangaren mu rage dogaro da bangaren man fetur.“  Ba a rude muke ba, duk da cewa lokacin na da rudarwa sosai, za mu magance matsalar, idan har muka yi hakuri wannan matsalar za ta wuce, sannan kuma kasa za ta yi kyau. Idan muka cigaba da dogaro da man fetur ba za mu cigaba a haka ba, don haka dole mu bunkasa wadansu bangarorin.
Ta kara da cewa, “ muna da sauran aiki da yawa a gabanmu, ba mu rude ba kuma bama yaudarar kanmu, wannan lokaci ne mai wahalar gaske, amma Najeriya na hannun na kwarai, idan muka tsaya a kan tsare-tsarenmu sannan muka yi wadansu gyare-gyare za mu samu nasara. Ina tunanin za muyi wadansu gyare-gyare a bangaren tsare-tsaren kudade, muna aiki a kan wannan. Za mu nemo yadda za mu taimaka wa masana’antu.’’
“Muna cikin wani yanayi ne na hauhawar farashin kayayyaki, sannan duk lokacin da aka samu irin wannan yanayin, zai yi wahala tsare-tsare su yi daidai. Don haka dole mu lura da abin da ya jawo tashin farashin.