Tattalin arzikin Afirka ta Kudu zai zarce na Najeriya a 2024 – IMF

Sai dai IMF ya ce Najeriya za ta koma matsayinta a 2026

Tattalin arzikin Afirka ta Kudu zai zarce na Najeriya a 2024 – IMF

Shugabar IMF, Christalina Georgieva

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), ya yi hasashen tattalin arzikin Afirka ta Kudu zai zarce na Najeriya a matsayin wanda ya fi kowanne haɓaka a nahiyar Afirka a shekara ta 2024.

A cewar wani rahoto na asusun, ana hasashen tattalin arzikin na Afirka ta Kudu, wacce ɗaya ce daga cikin mafiya girman shi a Afirka, zai kai Dala biliyan 401 nan da 2024.

To sai dai wasu alkaluma na cibiyar Kididdiga ta Britton Wood, sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai kai Dala biliyan 395, na kasar Masar kuma zai kai Dala biliyan 358.

Asusun na IMF dai ya ce tattalin arzikin na Najeriya zai dan zarce na Najeriya, wacce ita ce ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, kafin daga bisani ya fado, Najeriyar ta sake komawa kan matsayinta.

Kazalika, asusun ya yi hasashen tattalin arzikin na Afirka ta Kudu zai iya faduwa ta koma matsayi na uku a bayan kasar Masar nan da shekara ta 2026.

Ana ganin manufofin Shugaban Kasa Bola Tinubu da dama dai sun taimaka wajen jefa tattalin arzikin Najeriya cikin halin ni-’ya-su.

Daga cikin wadanda suka fi tasiri a ciki su ne janye tallafin mai da kuma karya darajar Naira.

Masana dai na ganin su a matsayin wadanda suka zo a lokacin da bai dace ba saboda za su kawo wa tattalin arzikin kasar koma baya.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda