Tattalin arzikin Najeriya ya karu a rubu’i na biyu na 2021 —NBS
Ana ci gaba da samun bunkasar tattalin arzikin tun daga karshen shekarar 2020.
Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2021, inda ya bunkasa daga kashi 0.51 da aka samu a rubu’in farko na bana.
Rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa, wannan shi ne kaso mafi girma na bunkasar tattalin arziki da kasar ta samu tun daga rubu’in karshe na shekarar 2014 kawo yanzu.
- ‘Dalilin da Najeriya za ta mallaki hannun jari a Matatar Dangote’
- Matsalar Tsaro: A kafa dokar ta-baci a Arewa —Matawalle
Sabuwar kididdigar ta nuna cewa, tagomashin da tattalin arzikin ya samu ya dara wanda aka samu idan aka kwatanta da makamancin wannan lokaci a 2020, da ma habakar da aka samu a watanni ukun farko na wannan shekarar.
NBS ta bayyana cewa, ci gaban da aka samu a cikin rubu’in farko da na biyu a bana, ya nuna sau uku a jere tattalin arzikin na bunkasa bisa la’akari koma bayan da aka samu a rubu’i na biyu da na uku na bara.
Rahoton ya ce, “Wannan alamu ne da ke nuni da ci gaba da dawowar harkokin kasuwanci da tattalin arziki bayan mawuyacin halin da aka shiga sakamakon kuncin da annobar Coronavirus ta jefa duniya a ciki.
“Ana ci gaba da samun bunkasar tattalin arzikin tun daga karshen shekarar 2020, sakamakon dawowar harkokin kasuwanci sannu a hankali gami da tafiye-tafiye na cikin gida da na waje.
“Tabbas wannan su ne sabubban da suka janyo murmurewar tattalin arzikin idan aka kwatanta da yanayin da kasar ta tsinci kanta a cikin zango na biyu na shekarar 2020 lokacin da aka shiga dokar kullen annobar Coronavirus.
Kazalika, rahoton na NBS ya nuna cewa bangaren da ba na mai ba ya samu tagomashi da kashi 6.74 cikin dari a cikin watanni shidan farko na 2021, sakamakon bunkasar harkokin kasuwanci a bangaren fasahar sadarwa, sufuri da sauransu.
A shekarar 2016 tattalin arzikin Najeriya ya shiga mawuyacin hali da kuma rubu’i na uku na shekarar 2020 kamar yadda alkaluman na NBS suka tabbatar.