Tattalin arzikin Najeriya ya karye – NBS

Wasu alkaluma da Hukumar kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, (NBS) ta fitar sun nuna cewa kasar nan ta samu koma-baya a tattalin arzikinta.Alkaluman da hukumar ta saki sun nuna an samu tawayar kaso biyu cikin 100 na arzikin kasar nan da mutanenta, a watanni ukun da suka gabata.Hakan dai na nuni da […]

Tattalin arzikin Najeriya ya karye – NBS
Tattalin arzikin Najeriya ya karye – NBS

Wasu alkaluma da Hukumar kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, (NBS) ta fitar sun nuna cewa kasar nan ta samu koma-baya a tattalin arzikinta.
Alkaluman da hukumar ta saki sun nuna an samu tawayar kaso biyu cikin 100 na arzikin kasar nan da mutanenta, a watanni ukun da suka gabata.
Hakan dai na nuni da cewa, Najeriya ta fada cikin kangin tattalin arzikin da ya fi kowanne a tsawon shekara 10, kamar yadda BBC ta bayyana.
Da man ko a watanni ukun farko na bana, tattalin arzikin ya samu komada da kaso 1.70 ne kawai.
Sai dai kuma alkaluman sun nuna cewa komadar ta wannan lokacin ba ta kai ta watanni ukun farko na mulkin Shugaba Buhari ba, a shekarar 2015.
Hukumar ta kididdiga dai ta ce kasar ta samu tawayar arziki da kaso 2.35.
Wannan dai bai zo wa ‘yan kasar da mamaki ba bisa la’akari da irin mawuyacin halin da jama’a ke ciki ta fuskar tattalin arziki.