Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS

Bunƙasar tattalin arzikin ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.

Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024.

A cewar rahoton da hukumar NBS ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.

Alƙaluman game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma ɗara kaso 3.46 cikin 100 da aka ba da rahoton samu a zango na 4 na 2023.

“Ɓangaren ayyuka ne kan gaba a bunƙasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya ƙaru da kaso 5.37 cikin 100 tare da ba da gudunmawar kaso 57.38 cikin 100 na jimillar tattalin arzikin,” a cewar NBS.

A jimillar ƙididdigar shekarar ta 2024, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka ne da kashi 3.40 idan aka kwatanta da kashi 2.74 a 2023.

Sai dai duk da haka, haɓakar ba ta cimma alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na haɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kashi 6 ba a shekarar ta 2024.

Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu

Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS

An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo