Tattara dukiyar Jihar Sakkwato a asusu daya ya samar da gagarumar nasara – Kwamishina
Alhaji Sa’idu Umar Kwamishinan Kudi na Jihar Sakkwato, tsohon ma’aikacin banki ne masanin harkokin tattalin noma da zuba jari. Aminiya ta zanta da shi kan tsare-tsaren gwamnatin Jihar Sakkwato, kasancewarsa dan Majalisar Zartarwar Jihar: Aminiya: Wane hali ne ka samu sha’anin kudi a Jihar Sakkwato a matsayinka na Kwamishinan Kudi, kuma yaya kake ganin za […]
Alhaji Sa’idu Umar Kwamishinan Kudi na Jihar Sakkwato, tsohon ma’aikacin banki ne masanin harkokin tattalin noma da zuba jari. Aminiya ta zanta da shi kan tsare-tsaren gwamnatin Jihar Sakkwato, kasancewarsa dan Majalisar Zartarwar Jihar:
Aminiya: Wane hali ne ka samu sha’anin kudi a Jihar Sakkwato a matsayinka na Kwamishinan Kudi, kuma yaya kake ganin za a tafiyar da aikin gwamnati ganin mafi yawan ayyukanka ka yi su ne a hukumomin da ba na gwamnati ba?
Kwamshina: Ba wata matsala gaskiya, babu bashin da ya fi karfinmu, ban ga wata almundahana ko sama da fadi da aka yi ba. Don haka zan ce harkokin kudin jiharmu lafiya lau suke ba mu da matsala. Maganar shigata gwamnati kuma ba wannan ne farko ba, na yi aiki da Kamfanin Sanya Hannun Jari na Jihar Sakkwato shekara shida a lokacin na shiga harkokin hada-hadar kasuwanci manya da matsakaita da kanana domin samar da tallafin da ya dace. Ayyukkan da na yi a baya sun taimaka min sosai, don da fara aikina ne muka tattara duk wani asusun ajiya na gwamnati muka mayar da shi wuri daya don mu habaka tsarin tafiyar da gwamnatimu, wasu asusun ajiyar ma an rufe su na wucin-gadi, wasu ne kawai ke bude sai kawai muka tattara su wuri daya ka ga duk wasu kudin shiga da jihar nan za ta samu a hukumomi da daidaikin mutane za su shiga asusun ajiya daya ke nan, ku,a hakan zai taimaki tafiyar da gwamnati a harkokinta na yau da kullum.
Aminiya: Bayan asusun ajiya guda daya da kuke da shi ko wata hukuma ko ma’aikata na iya bude wani asusun ajiya daban, kuma wannan tsarin ba zai kawo cikas ga hukumomin da ke tara kudin shiga na jiha ba?
Kwamshina: Wannan asusun ba wani abu mai matsala ba ne akwai wasu ma’aikatu da lamuransu ke tasowa jefi-jefi da ke bukatar gaggawa mun ba su damar bude wasu asusun ajiya amma fa wannan ba wani abu ba ne illa kokarin kawo ci gaba mai dorewa ga tsarin tafiyar da gwamnati. Babu wata matsala ga tafiyar da gwamnati abin da muka gada wurin biyan albashin ma’aikata har yanzu haka muke yin sa daga Ma’aikatar Kudi ta Jiha ne muke tura wa duk ma’aikatanmu kudinsu a asusun ajiyarsu na bankuna. Tsarinmu na asusu daya yana tafiya tare da hukumomin tara kudin shigarmu, duk wasu kudi da za ka biya a wurin wata hukuma lambar asusu daya za a ba ka ka sanya su, ma’aikatar ta gwamnati ce, shi ma asusun nata ne to me zai kawo cikas a nan?
Aminiya: Akwai hukumomin da ba su cikin tsarin biyan albashinku, yaya kuke biyan albashinsu a yanzu da kuka fito da tsarin asusu daya kuma wane alfanu ya samar?
Kwamshina: Wadannan ma’aikata muna biyan su ne bisa wani tsari na musamman da muke tambayar kowace hukuma ta kawo mana yawan kudin da take hadawa da yawan kudin da take kashewa mukan biya su albashi ne daidai kudin shigar da suke kawo mana. Ka ga ba wani mutum da muka rike yana jiran tsammani hasali ma hukumomin ne muka sanya wa kaimi don su samar da kudin shigar tafiyar da ofishinsu, shi ya sanya da zarar hukuma ta cika ka’idojinmu mukan sallame ta ba tare da wani bata lokaci ba. Nasarorinmu kuwa su ne kafin mu fara wannan tsari wane ne ya san akwai Naira biliyan daya da rabi a wasu asusun da ba kowa ne ya san suna aiki ba? Na biyu kowace ma’aikata da hukuma da ke jihar nan ta san gwamnati ta san duk kudin shigar da suke samu. Domin da sun sanya kudin za su fada cikin asusun daya na gwamnati, tun lokacin da aka fara wannan tsari an samu gagarumar ci gaba da fahimtar juna wurin sanin kudin jama’a a tsakanin bankuna da gwamnati wanda hakan ya samar da raguwar kura-karai kan hakikanin kudin da ke cikin asusun ajiyar gwamnati. Kada ka manta hakan ya sanya gwamnati bibiyar kudin ajiyarta don tabbatar da kare su da kuma hana barnatar da su, tsarin na taimakawa matuka wurin aiwatar da kasafin kudin bana.
Aminiya: Tsofaffin ma’aikata na bin bashin garatuti, wace hobbasa kuke yi don biya su musamman malaman firamare?
Kwamshina: Mun fara shiri kwakkwara don ganin mun biya su dukkan kudin da suke binmu tun daga wannan biyan da muka fara na sama da Naira biliyan 2 da miliyan 600, za mu yi kamar yadda muke yi kan kudin albashi da fansho, kafin wata ya kare za mu rika duba wadanda za mu biya su don samun karin mutane a kowane wata. Mun zage damtse sosai daga nan zuwa karshen bana ya zamo ba zancen fansho ko garatuti ko albashi da ake bin mu. Malaman firamare da ma’aikatan kananan hukumomi za mu biya su nan ba da jimawa ba, kamar yadda muka yi wa jiha. A yanzu mun kafa kwamitin da zai tantance su ya tabbatar da wadanda ke da hakki kadai ne za su amfana, mun gina tsarin tantancewar ne ta hanyar Ma’aikatar Shari’a don haka ba mu da matsala insha Allah.
Aminiya: Hanyoyin samar da kudin shiga a jihar sun yi kasa wane shiri kuke da shi na ganin kun zaburar da su?
Kwamshina: Na farko dai za mu share kurar da ke saman dokar samar da kudin shiga ta jiha, za mu nemi Majalisar Dokokin ta Jiha ta yi bitar dokar da yi mata gyarar fuska ta yadda za ta da ce da halin da ake ciki yanzu. Yanayin karbar haraji da muke da shi zai canja, za mu fadada hanyoyin irin na can baya kuma za mu tuntubi wadanda lamarin ya shafa don cimma bukatarmu. Tun daga wurin kasafinmu na bana ba mu yi wasa ko kyale kowane bangare na haraji ba.