Tattaunawa da ’yan bindaga ne mafita rashin tsaro a Arewa – Sarkin Fulanin Legas  

Sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado ya bayyana cewa mafita ga rashin tsaro da ke addabar al’ummar wasu yankunan Arewa ita ce tattaunawa da ’yan bindigar tare da samar wa matasa ayyukan yi. Sarkin Fulani Bambado ya ce matakin da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, ya dauka na tattaunawa da ’yan bindigar ya […]

Tattaunawa da ’yan bindaga ne mafita rashin tsaro a Arewa – Sarkin Fulanin Legas  

Sarkin Fulanin Jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado ya bayyana cewa mafita ga rashin tsaro da ke addabar al’ummar wasu yankunan Arewa ita ce tattaunawa da ’yan bindigar tare da samar wa matasa ayyukan yi.

Sarkin Fulani Bambado ya ce matakin da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, ya dauka na tattaunawa da ’yan bindigar ya yi tasiri, don haka ya kamata ragowar gwamnonin Arewa da ke fama da irin wdaannan matsaloli a jihohinsu su yi koyi da shi.

Sarkin Fulanin Legas ya bayyana haka ne lokacin da matasan Majalisar Kungiyar Sa Ahmadu Bello ta Kasa suka ziyarce shi a karshen makon jiya. Matasa wadanda suka koka da rashin tsaro da ke addabar al’ummar Arewa sun ce matasa da mata ne  suka fi shan wahala don haka shugabannin gargajiya na da gudunmawar da za su bayar domin magance matsalar.

Matasan a karkashin jagorancin Malam Yahaya Yakubu Domain, sun karrama Sarkin Fulanin na Legas Alhaji Muhammadu Bambado da lambar girmamawa ta Jakadan Zaman Lafiya inda suka bukaci taimakonsa wajen ba da shawarwari domin ci gaban mata da matasa da wanzuwar tsaro.