Tattaunawa da ‘yan bindiga ne mafitar rashin tsaro a Arewa- Sarkin fulanin Legas

Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya bukaci gwamnonin Jihohin Arewa su yi amfani da irin matakin Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, da ya dauka wajen sasantawa da ‘yan bindigar Jihohin su. Sarkin ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron da ke addabar al’ummar jihar Legas shi ne rashin tattaunawa da ‘yan bindiga tare […]

Tattaunawa da ‘yan bindiga ne mafitar rashin tsaro a Arewa- Sarkin fulanin Legas

Sarkin Fulanin jihar Legas Alhaji Muhammadu Bambado, ya bukaci gwamnonin Jihohin Arewa su yi amfani da irin matakin Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, da ya dauka wajen sasantawa da ‘yan bindigar Jihohin su.

Sarkin ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron da ke addabar al’ummar jihar Legas shi ne rashin tattaunawa da ‘yan bindiga tare da sanarwa matasa madafun ayyukan yi Yace matakin da gwamnan jihar Zamfara, ya yi tasiri sossai dan haka ya kamata ragowar gwamnonin Arewa da ke fama da irin wannan matsaloli a jihohin su su yi koyi.

Sarkin fulanin na Legas ya bayyana haka ne a sa’ilin da matasan majalisar kungiyar Sir Ahmadu Bello ta kasa suka ziyarce shi a karshen makon jiya, wadanda suka koka da rashin tsaro da ke addabar al’ummar Arewa inda suka ce matasa da mata su kafi shan wahala dan haka shugabannin gargajiya nada rawar da zasu taka domin magance matsalar Matasan, sun kuma karramma sarkin fulanin Legas Alhaji Muhammadu Bambado da lambar girmamawa ta jakadan zaman lafiya.