Tattaunawa game da yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (1)

A makon jiya ne zakakurin dan jarida kuma malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Malam Kabiru danladi Lawanti ya bude wani tsokaci a turakarsa ta Facebook, inda ya ce: “Ina fatan ganin ranar da malaman addinin Musulunci na dukkan bangarori za su mai da hankali wajen ginin makarantu, asibitoci da wuraren kula da gajiyayyu, maimakon yawace-yawace […]

Tattaunawa game da yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (1)
Tattaunawa game da yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (1)

A makon jiya ne zakakurin dan jarida kuma malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Malam Kabiru danladi Lawanti ya bude wani tsokaci a turakarsa ta Facebook, inda ya ce: “Ina fatan ganin ranar da malaman addinin Musulunci na dukkan bangarori za su mai da hankali wajen ginin makarantu, asibitoci da wuraren kula da gajiyayyu, maimakon yawace-yawace daga jiha zuwa jiha da sunan wa’azin kasa ko mauludin wani shaihi.”
Yana rufe baki sai Muhammad A. Kumo, shi ma ya mara masa baya da cewa: “Mafarkina ke nan kuma ai wannan gallafiri ne da ko bai da amfani ko kuma amfaninsa bai taka kara ya karyaba.”
Shi kuwa Hassan danhaire cewa ya yi: “Nema ake a mai da abin sana’a.”
Daga nan ne kuma sai Kabiru ya dawo, inda ya ce: “Na fi danganta abin da siyasa. Kwanakin baya na ga Mansur Manu Soro shi ma ya yi magana irin wannan. Akalla ana kashe sama da Naira miliyan goma wajen shirya irin wadannan bukukuwa na kasa ko na Afirika, banda irin kudade da ake kashewa na mota don halarta irin wadannan wa’azozi. Kwanakin baya muka kama wata yarinya da ta saci wayar matata a nan Zariya. A cikin irin wannan yanayi, ake ce mana wai babanta ya tafi Legas wa’azin kasa. A nan nake ce wa shi DPO na Zariya, ka ji mutumin da ga wa’azi a gidansa amma wai ya kama hanya ya tafi wa’azin kasa a Legas. Ba abin da ake koyowa a wadannan wurare na wa’azozin kasa. Hasali ma, masu zuwa wadannan wurare sun fi damuwa da yawan jama’a da suka halarci wuraren, ko irin motar da malaminsu ya je da ita ko kayan da ya saka, a kan abin da malaman suka fadi. Amma in kai magana ko ka soki abin, sai a ce ba ka kishin addini. Na tashi daga Zariya zuwa Gombe wancan watan, a kan hanya daga Soba har Gombe, na iske wurare sun kai ashirin a hanya, ba abin da ake nema sai taimakon ginin masallaci, ba inda na tarar ana neman taimakon ginin makaranta ko daya. Ina ji malamai irin su Yasir Ramadan Gwale da sauransu ya kamata su dauki wadannan irin batutuwa da muhimmaci, don canza irin wannan hali, wanda bai kyautata mu’amala ba tsakanin mutane, bayan fiye da shekara talatin ana yi.”
Daga nan ne shi ma Bashir Yahuza Malumfashi ya yunkuro, inda ya ce: “Wallahi kamar ka shiga zuciyata, tuni nake ta kai-kawo da tunanin cewa lallai ya kamata kungiyoyin addinin Musulunci su farga. A ganina, babban abin da ya kamata a maida hankali shi ne gina makarantu da ilimantar da mutane tsintsar koyarwar addini, wanda ya fi tara jama’a da yawa ana wa’azin la’antar juna da shagube ga juna. Ka duba kauyukanmu da karkara, kai har ma da biranen, tsarki ma matsala ne, domin da dama ba mu ma iya tsarkin ba, balle alwala, balle kuma ita kanta Sallar. Attajiranmu ba su da ilimin zakka, balle su fitar da ita yadda ya kamata. Na tabbata ta hanyar karantarwa a makarantu nakwarai, zai rage irin wadannan matsaloli. A yau mun maida addini kamar siyasa, a tara mutane ana… Allah Ya sawwake!”
Malam Kabiru danladi ya sake yin ta’alikin cewa: “Mu, mabiya, ba mu da cikakken ilmin da zai sa mu yin cikakken tsarki, alwala, Sallah da iya zamantakewa da mutane amma malamanmu ba abin da suka sa gaba ban da wa’azin kasa da shirya mauludin shaihinnai.”
Daga nan kuma sai Muhammad Hashim Suleiman ya bayyana cewa: “Abin haushin kuma, yawancin mabiyan ba su da ilmin tsarki, alwala, sallah da zamantakewa. Wallahi na san wanda bai bai wa iyalansa abinci amma ziyara har kasar Nijar yake zuwa! Na kuma san wanda ’ya’yansa ’yan mata biyu har kwana a waje suke amma wa’azin kasa har Legas yake zuwa! Na san wanda ya kasa kawo cikakiyyar Fatiha amma an masa kyautar Aljanna! Gaskiya muna da matsala, shuwagabanninmu su yaudare mu, in mun fado wajen wadanda ya kamata su sanar da mu Allah da manzonSa, su kuma hankalinsu na wajen wa’azin kasa da maulidin shaihunnai!”
Nan take Kabiru ya dawo da cewa: “Bashir Yahuza Malumfashi, wallahi shi ya sa nake girmama malamai irinsu marigayi Auwal Adam, Ja’afar Adam, Bn Uthman, Dokta Ahmad BUK da sauransu. Su sun maida hankali ne wajen koyar da addini a masallatai, ta hanyar saka takardu na ilmi ana karantar da jama’a. Maimakon wa’azin kasa, malamai su rika kiran taron kara wa juna sani, watakila a shekara sau daya ko sau biyu. A duba wasu matsaloli na addini da suka ta so, sannan a ba da fatwa. Ta haka sai ka ga zuciyoyi da bakuna sun hadu wajen kawo ci gaba na addini. Amma irin abin da ake yi yanzu, ba shi da tsari ko kadan.”
Sai kuma Mansur Manu Soro, da ya ce: “Wannan matsala fa tana daga cikin manyan dalilai da suka hana Arewa ci gaba. Malaman sun zama ’yan siyasa, ’yan kasuwa masu yin kasuwanci da mabiyansu. Shehunai su sayar da mabiyansa ga ’yan siyasa su karbi kudi, malaman Izala kuma su yi bikin kaddamar da wani shiri, su sace kudaden. Ana damfarar mutane da sunan addini, jahilai sun kasa ganewa. Shi ya sa ni fa ba ruwana da wani kungiyanci a addini. Ya rage wa ’yan Arewa, ko mu gyara ko al’ummarmu ta ci gaba da rugujewa.”
Haka shi ma Bashir Malumfashi ya dawo, inda ya kara da cewa: “Maganar ke nan, domin manyan malaman duniyar Musulunci da suka shahara, haka suke yi. Misali, marigayi Ahmad Deedat, ga su Shaikh Khalid Yasin, ga su Dokta Bilal Philips, ga su Dokta Zakir Naik da sauransu. Salon karantarwarsu ya fi tasiri, babu hauragiya, babu zage-zage, sai hujja karara. Ta haka ne ma suke jawo hankalin wadanda ba Musulmi ba su amshi Musulunci. Amma a Najeriya, mun tsaya sai fada da la’antar juna. dan Shi’a na zagin dan Izala, dan Izala na zagin dan darika…. Yaushe wani zai yi sha’awar addinin, a haka? Lallai lokaci ya yi da za mu farka!”
Sai Malam Kabiru ya sake dawowa, inda ya ce: “Yau shi ya sa muka samu kanmu a cikin matsalar Boko Haram. Gobe ki ji an ce Kiristoci da Musulmai sun kaure a Zangon-Kataf ko kaura ko Jos ko Bauchi da sauran wurare. Ko dai mu canza wadannan halaye, ko kuma ba abin da muka gani. A kwanakin baya wa’azin kasa da aka yi a Zamfara, kasafin kudi na gudanar da wa’azin da aka bai wa Gwamnan Naira miliyan 60 ne amma daga baya sai Gwamnan ya yi dabara, ya kira wani malami a cikinsu, ya tambaye shi, yana gani kamar nawa za a kashe wajen gudanar da wannan wa’azi. Wannan malami ya ce masa ai in manyan malamai da aka gayyata duk sun halarta, da kudin otel da na man mota da abinci da za a tanada don baki, watakila a kashe Naira miliyan shida. Sai Gwamna ya ba shi Naira miliyan goma, ya ce mai a je a yi wa’azin.”
Za mu ci gaba