Tattaunawa kan yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (3)

Jama’a, har yanzu dai muna ci gaba da tattaunawa game da yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya kuma da ikon Allah mun shiga mako na uku:   Bari mu fara da kalaman Shehu Mustapha Chaji, wanda ya ce: “Bashir Yahuza Malumfashi, abin da nake so mu gane bai wuce cewa layin wa’azozi da mauludai […]

Tattaunawa kan yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (3)

Jama’a, har yanzu dai muna ci gaba da tattaunawa game da yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya kuma da ikon Allah mun shiga mako na uku:

 

Bari mu fara da kalaman Shehu Mustapha Chaji, wanda ya ce: “Bashir Yahuza Malumfashi, abin da nake so mu gane bai wuce cewa layin wa’azozi da mauludai daban, sannan gina makarantu da sauransu, su ma layinsu daban. Da ni da kai za mu iya rajistar kungiyar addini don samar da kudade don biyan malaman Islamiyya albashi ko taimaka wa tsangayoyi da magunguna. Mu daina tunanin cewa lallai sai su Sheikh ne kawai za su yi wa al’umma hidima.”

Nan take shi kuma Malumfashi ya kara haske da cewa: “Chaji, a’a, ban amince da haka ba. Kullum ta inda aka hau, ta nan ake sauka kuma da na gaba ake gane zurfin ruwa. Kowace kwarya akwai abokiyar burminta. Maganar addini kullum tana hannun malamai, maganar kungiyar raya al’umma kuma daban, irin ta ce ni da kai za mu iya hadawa, amma ba ta addini ba. Za mu iya taimakon addini da irinta. Lallai ne, ni a ganina, malamanmu na addini su sauya alkibla, su yi koyi da malaman duniyar zamani wajen tafiyar da da’awa. Ni dai na tabbata muddin muka ci gaba da haka, babu inda za mu kai al’ummarmu a addinance sai hallaka, al’umma ba za su fahimci tsantsar koyarwar addinin ba. Idan Sheikh Dahiru Bauchi ya yi gabas, Sheikh Zakzaky ya yi yamma, Sheikh Bala Lau ko Sheikh Jingir suka yi kudu, sannan suka shagaltu da tara tarurrukan yawace-yawace, alhali mabiyansu wadansu ko tsarki ba su iya ba. Don Allah yaushe za a samu ci gaba, yaushe za a samu fahimta ta ainihi a addinance, yaushe za mu gane cewa addinin Allah igiya daya ce, kuma so ake a kama ta jimlatan baki daya ba tare da rarrabuwa ba? Malam Chaji, mu sake tunani, muna da babban aiki!”

An nan ne Kabiru Danladi Lawanti ya dawo, inda ya ce: “Sannan shekara talatin ana abu guda, sannan mun wayi gari a wannan hali? Sannan mu ce wai wa’azin kasa, taron mauludi, ko tattaki zuwa Zariya shi ne zai kawo mana maslaha? Akwai bukatar canja tunaninmu, mu bar yaudarar juna don Allah. In kungiyoyin raya al’umma daban suke da na addini, to ai sai mu watsar da addinin mu yi ta kafa kungiyoyi.”

Chaji ya sake dawowa da wani kalubale, inda ya ce: “Na lura akwai hassada a maganganun wadansu! Duk da haka a ci gaba da ba da shawarwari ko za a yi kwaskwarima a wasu abubuwan. Amma zancen wai a daina wa’azin kasa ko mauludi ko tattaki, mutum har ya bar duniya ba za a daina ba! Shin su wane ne ke yawon da’awa a garuruwan maguzawa da Kudancin kasan nan? Masu yi wa ke biyan su? Kai da ka ce ba su iya ba, yaushe za ka fara naka?”

Daga nan sai Manzo Bappari ya shigo da cewa: “Da kowa zai gane da mun warke wallahi.”

Malumfashi kuma ya tarbi Chaji da cewa: “Chaji, Hahahahahahaha! Wallahi ka ba ni dariya, hassada fa ka ce, kamar yaya? Babu wanda ya ce a daina maulidi, babu wanda ya ce a daina wa’azi, amma mun ce ne mu canja taku da tafiyar da su yadda za su dace da manufa da samun nasara gamsasshiya. Ka sani sarai cewa ba kowa ne Allah Ya ce ya yi wa’azi ba, sai masani kuma mai hikima da fasahar yin haka. Na san ka fahimci batun Danladi Lawanti da manufarsa, amma da gangan kana son karkatar da batun zuwa wani abu can daban. Lallai ne mu duba, mu dauki abin da ya fi amfani ba tare da baddala manufa ba.”

Ganin haka sai ga Ibrahim Lawal Kaya Idasu ya shigo da addu’a, inda ya ce: “Allah Ya hada kan Musulmai baki daya, mu kuma kasance masu yi wa junanmu adalci, domin mutum tara yake bai cika goma ba.”

Shi kuwa Basheer Mukhtar Yusuf Zariya cewa ya yi: “Dokta Kabir Lawanti, kwarai wannan haka yake. Malaman addinin Musulunci daga dukan wadannan bangarori sun fi bayar da hankali ko nuna muhimmanci ga yin wa’azin kasa ko maulidin sheihi amma kuma a zahirin gaskiya ba abin da ya kamata a bai wa muhimmaci ba ke nan. Hada kan al’umma shi ne kan gaba a wannan lokaci sannan samar da makarantun Islamiyya da bayar da tallafi ga gajiyayyu da makamantan haka.”

Daga nan sai ga Muhammad Iliyasu Kurfi ya shigo da cewa: “Wannan ne ya sa nake jinjina wa almajiran Malam Ibrhim Elzakzaky.”

Ibrahim Musa Gwammaja ya yi addu’ar cewa: “Allah Ya sa mu dace.”

Haka shi ma Sani Bula, ya yi addu’ar cewa: “Allah Ya sa sun ji kuma su yi aiki da wannan shawara.”

Hassan Danhaire kuma ya bijiro da cewa: “Fahimtata, wannan tattaunawa ta yadda za mu gyara halayenmu da na malamanmu ce da shi kansa addinin. In kuwa har ba a fahimci juna ba, ya alla da gangan ko ana sane; son zuciya ce, to hakika ba inda za a je. Dole sai an daure in ana son ci gaba.”

Sai Ilyasu Shu’aibu Ahmad, wanda ya ce: “Kowa da tasa fahimtar. Wa’azin kasa wajen wadansu suna ganin ba ya da amfani. Ke nan wa’azin ba shi da amfani? To ku sani wa’azin da ake yawo birni da kauye ake yi, shi ya kawo har Musulmai suka tashi tsaye wajen neman ilmin addini da zamani har suke tutiya da shi a yanzu. Da ba wa’azi da ko an gina makarantar ko asibiti ba za mu samu kwararru da za su rike wadannan wurare ba. Kuma alhamdu lillahi, a kara bincike a cikin kungiyoyin Musulmi; akwai masu abubuwan da ka ambata ko ba duka ba. Misalin wanda na sani sosai, kungiyar Izala. Akwai asibitoci akwai makarantu tun daga na raino har Diploma da NCE, Digiri ma na nan tafe ana kan shirye-shirye. Allah Ya kara hada kan Musulmi.”

Kabiru Danladi Lawanti ya dawo, yana cewa: “Ilyasu Shu’aibu Ahmad ka fahimci makalar da kyau.”

Shi ma Sunusi Sani Dala, bayan ya karanta wannan tattaunawa sai ya aiko da sakon cewa: “Wannan lokaci, muna bukatar hadin kai. Wadansu malaman suna daukar kansu kamar wadansu sababbin manzanni. Idan ba ka bi su ba sai su rika ganin kamar kai ba Musulmi ba ne. Gizago da sauran masu kyakkyawar fahimta, a ci gaba da nasiha. Allah Ya yi mana maganin dukan masifu.”

Za mu ci gaba