Tattaunawa kan yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (4)

A wannan makon, insha Allahu za mu karkare wannan tattaunawa, wacce muka faro makonni uku da suka gabata. Bari mu ci gaba da jona zaren tattaunawar, kamar haka:  Malam Ilyasu ya dawo kan Bashir Yahuza, ya ce masa: “Malumfashi, don Allah ka kula wajen magana, ka daina kiran zuwa taron wa’azi da sunan yawace-yawace. Ayoyin […]

Tattaunawa kan yadda ake gudanar da Musulunci a Najeriya (4)

Ayarin Gizagawa, a yayin da suka ziyarci Kabir Sakaina a Malumfashi, Jihar Katsina

A wannan makon, insha Allahu za mu karkare wannan tattaunawa, wacce muka faro makonni uku da suka gabata. Bari mu ci gaba da jona zaren tattaunawar, kamar haka: 

Malam Ilyasu ya dawo kan Bashir Yahuza, ya ce masa: “Malumfashi, don Allah ka kula wajen magana, ka daina kiran zuwa taron wa’azi da sunan yawace-yawace. Ayoyin Allah da Hadisan Manzon Allah (SAW) ake karantarwa a wajen.”

Ganin yadda malamin ke son shafa wa Bashir Yahuza kashin kaji, sai shi kuma ya yi masa gyara da cewa: “Ilyasu, lallai ba ka karanta zaren bayanan da aka faro ba tun farko, shi ya sa za ka saka mini magana a bakina, alhali ba abin da ka fada nake nufi ba. Ai ko giyar wake na sha babu yadda zan kira wa’azi da sunan yawace-yawace, kuma kada ka sake ka karkatar mini da ma’ana, idan ba ka fahimci bayani ba, kada ka kakaba mini kakabau! Ehe!”

Har yanzu dai Ilyasun ya dawo kan Kabiru Lawanti da cewa: “Kabiru, kalmarka ta cewa “yawace-yawace,” ita ta sa ba a fahimce ka ba. Da cewa ka yi a kara a kan wa’azin da ake yi, da ya fi. Amma wannan kalmar ta juya ma’anar manufarka, domin tana nuna kamar wa’azin da ake yi a wurare daban-daban ba ya da amfani ke nan. Kai Lakcara ne kuma HOD, idan ba na manta ba, don kana karantar da matata.”

Daga nan ne kuma ya bar Kabir, ya karkato zuwa ga Malumfashi da cewa: “Malumfashi, ka koma bayananka na sama ka ga abin da ka rubuta. Ni gyara na yi maka dan uwa, gudun kada ka fada hadari, amma in gyaran bai yi maka ba, to ka yi hakuri amma ka fadi yawace-yawace.”

Shi kuwa Kabiru Danladi sai ya fito ya ce: “Ni ba na goyon bayan wadannan wa’azozin kasa.”

Ilyasun dai sai ya sake dawowa kan Bashir, ya ce: “Malumfashi, ga kalmar da ka fada, na rage ne ma: “maimakon yawace-yawacen terere da la’antar juna.”

Bashir bai kyale shi ba, shi ma sai ya shaida masa cewa: “Ilyasu, na san abin da na rubuta kuma na san mutane sun fahimce ni, don haka babu wani hadari da na fada ko zan fada da fadar haka. Idan ba ka fahimce ni ba, bai kamata ka yanke mini hukunci ba, ka tura ni rami, alhali ina kan tudu!”

Muhammad Hashim Suleiman, ya shigo cikin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: Ba wanda zai ki wa’azi da yabon Manzon Allah, amma a inda aka makale da sunan wadannan abubuwan ana karbar taro da sisi wajen ’yan siyasa, wannan ba wa’azi ba ne kuma ba yabon Manzon Allah ba ne! Yanzu ma abin ya wuce nan, kowa kokarinsa a ce mabiyansa sun cika gari, sun hana walwala; domin hakan zai ba shi damar fadin cewa shi ya fi mabiya, domin ’yan siyasa su ji da shi! Har ma fadi ake cewa, in zabe ya zo ba za mu zabi wane ko wane ba, ko kuma a rika shagube, ana fadin da ku zabi dan kaza da kaza, gara wanda ba addininku daya ba. A haka kuma mu kira wannan wa’azin kasa ko maulidin sheihunnai? Akwai gyara.”

Ilyasu Shu’aibu bai kyale Malam Kabir Danladi ba, ya sake shaida masa cewa: “Kabiru, wannan ra’ayi ne, kana da ’yancin fadar haka, watakila don ba ka zuwa wuraren sai ’yan kadan. Amma damuwata a wannan magana shi ne, kiransa da sunan ‘yawace-yawace.’ A Musulunci har maganganunmu suna da linzami, komai Musulmi zai fada sai ya auna da ma’aunin Musulunci.”

Sai kuma ya karkato kan Bashir, ya ce: “Malumfashi, babu damuwa wallahi. Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi.”

Kabiru kuma ya dawo da cewa: “To, ai sai mu koma ma’auni na Musuluncin mu gani.”

A nan ne Malumfashi ya jawo hankalin Kabir cewa: “Lawanti, ina ganin kada mu kai ga wannan janibi, domin babu abin da hakan zai haifar sai hairani da gardaddamin da za su ma bata maka rai. Ba ma’aunin fahimta wadansu za su sa ba. Mu dai mun fahimci bayaninka tun farko, kuma gaskiyar ke nan tsantsa, mai daci. Allah sa mu dace, amin!”

Shi kuwa ya amsa da cewa: “Amin, Bashir Yahuza Malumfashi. Allah Ya nuna mana gaskiya, Ya ba mu ikon bin ta.”

Abdulmalik Nuhu Makeri, shi ma ya shigo da nasa tsokacin, ya ce: “Gaskiya kam wa’azin kasa shi ne mafita, ba yawon ziyarar wani shehi ba. Amma dukansu a tsaya a karantar da al’umma karatu na hakika ya fi a yi ma wa’azi sau daya a shekara ko a wata amma insha Allahu mu ’yan Izala za mu gyara, domin na tabbata mu ne da gaskiya ba makida ba.”

Shi kuwa Muhammad Muhammad Lumbi, ya juya kan Kabir Lawanti ne, ya ce masa: “Malam Kabir, gaskiya ba ka fahimci abin da yake damun mutane ba. Babban abin da yake damun mutane shi ne jahilci, addinin son zuciya, da yi ba don Allah ba amma tabbas rashin wa’azi shi ne babbar masifa a kasar nan. Kuma a bincika dukan abin da ka kirga, babu abin da Izala ba ta mallaka ba; musamman kwanan nan an bude sababbin asibitoci biyu a Jos, a Gombe na san akwai Sunnah Hospital, makarantun firamare sun fi hamsin, makarantun sakandare 27, Diploma, NCE da sauransu; ana kokarin digiri duka a Gombe kawai.”

Kabir ya ba shi amsa da cewa: “Ba wanda fa ya ce kada a yi wa’azi amma irin wadannan wa’azozi da ake tafiya gari-gari shi ne na ce a sake masa manufa. A kafa majalisu na karatu a kowane gari, a rika koyar da mutane addini, sannan kowane bayan wata uku a shirya taron malamai, na kara wa juna sani. Wadannan tarurruka su ne za su rika ba da fatawoyi na wasu matsaloli da wasu malamai ba su iya warwarewa ba a majalisinsu. Ta haka za a yi maganin jahilci sannan in matsala ta taso sai malamai sun yi munakasha a kanta, su tace, su gaya wa mutane abin da za su yi. Amma ina nan a kan bakata cewa, wadannan tarurruka na wa’azi da mauludai, in ma sun yi amfani a da, to a yanzu an wuce wannan; duniyar ilimi ta yi gaba ta bar mu.”

Ya kara da cewa: “Malami zai iya yana sana’arsa yana kuma koyarwa, ko wadanda yake koyarwa su dauki nauyinsa, ba irin wannan mummunan dogaro da ake yi da ’yan siyasa ba.”

Muhammad Saleh Akko ya goyi bayansa da cewa: “Shawararka ta yi mini, wallahi amma sai a hankali!”

Haka Muhammad Kabir Ibrahim ya ce: “Haka ne wannan, Allah Ya ganar da mu, amin.”

Kabiru kuma ya kara haske da cewa: “Wallahi Muhammad Saleh Akko, na duba irin halin da muka samu kanmu a yau ne na tabarbarewar tarbiyya da labarai marasa dadin ji game da dabi’un wadansu malamai. Sai na lura da irin hadarin da muka samu kanmu. Za mu ci gaba da wannan kamfe insha Allah.”

Daga nan ne Muhammad ya rufe da addu’ar cewa: “Allah Ya taimake mu. Koda irin mummunar gabar da ake yadawa a tsakanin Musulmi za ta ragu. Na biyu, irin wadannan tarurrukan sun fi kama da farfaganda a kan karin ilimi. Dalili, za ka samu mutum ya zaga jihohin kasar nan kaf a zuwa wa’azi, har wajen kasar nan amma ba zai kirga ma farillan alwala ba.”