Tattaunawa ta musamman a kan littafin Alfu Laila Wa Laila (Dare Dubu Da daya) (2)

A ci gaba da tattaunawar dam asana suka yi game da mashahurin littafin labarum dauri na Dare Dubu Da daya, ga abin da Farfesa Malumfashi Ibrahim y ace, a taken sharhinsa day a yi wa take da: ‘karin Haske Game Da Littafin Alfu Laila Wa Laila.’ Inda y ace:“Yanzu na tsinci wannan tattaunawar, da yake […]

Tattaunawa ta musamman a kan littafin Alfu Laila Wa Laila (Dare Dubu Da daya) (2)

A ci gaba da tattaunawar dam asana suka yi game da mashahurin littafin labarum dauri na Dare Dubu Da daya, ga abin da Farfesa Malumfashi Ibrahim y ace, a taken sharhinsa day a yi wa take da: ‘karin Haske Game Da Littafin Alfu Laila Wa Laila.’ Inda y ace:
“Yanzu na tsinci wannan tattaunawar, da yake kuma ta ilimi ce na dan bi na ga bayanai masu burgewa. Abin da zan yi a nan shi ne tsoma baki a wuri biyu kurum, asalin ‘Alfu Layla’ da yadda masu fasaha ke samun haske game da fasaharsa, kila ta haka mu fahimci abin da ya sa kowanenmu yake kasancewa ‘barawo’ a duniyar fasaha. Bari na soma da asalin ‘Alfu Layla’ tukuna.
Ya zuwa yau, babu wata takamaimiyar matsaya dangane da ko a wane wuri ne aka tsara ko aka wallafa littafin ‘Alfu Laila.’ Zamani da lokaci da kuma shekarar da aka yi wannan aiki ba tabbatattu ne ba. Ta’allake da wannan kuma ba a tabbatar da wanda ya wallafa ko ya tattara ko tace littafin ba. Shi dai littafin ‘Alfu Laila’ yana kunshe ne da tatsuniyoyi da labaran ban dariya da na soyyayya, bayanai kan rayuwar gaskiya ko tarihi da tsunduma a cikin duniyar aljanu da maridai da ifiritai da sauran su.
Rashin tantance hakikanin wadannan muhimman abubuwa dangane da littafin ‘Alfu Laila’ bai zama abin mamaki ba, domin in an duba za a ga cewa litttafi ne wanda tun farkon tsara shi har ya zuwa lokacin da ya bunkasa, ya yi bulaguro zuwa kasashe da dama kuma ya ratso zamunna daban-daban. Ya fada hannun editoci da masu sake masa kama bilahaddin. Wannan matsayi nasa ya sa Turawa da dadewa suka kasance cikin rudu dangane da wannan littafi, suna cewa:
Abin mamaki ne a ce aikin talifi kamar wannan da aka san shi a Turai da dadewa, aka kuma yi sama da shekaru 200 ana nazarinsa amma ba a san masomarsa ba. Sa’annan kuma ba a san sirrin da aka yi amfani da shi wajen tsara shi ba (Burton; 1894; 9:53).
Daga binciken da aka gudanar, an sami rukuni biyu na masana kuma mabambanta dangane da asalin wannan littafi. Akwai masu cewa daga kasar Farisa ya fito da kuma masu cewa tsittsigensa na kasar Larabawa ne. Masu ra’ayin cewa daga kasar Larabawa ya fito sun fi kafa hujja ta nuna cewa ba wani littafin ‘Alfu Laila’ a wani harshe da ya fi na Larabci dadewa a halin yanzu, haka kuma yawancin labaran da ake da su a cikin littafin a kasashen Larabawa aka tsara su ko kuma suna dauke da sunayen Musulunci ko masu tasiri da addinin Musulunci. Haka ma wasu labaran da aka gina na cikin littafin za a ga cewa ko da an yi dace da wasu wadanda ba na Musulunci ba, ko kuma ma an tsara labarin kafin zuwan Musulunci za a sami birbishin Musulunci a cikinsu. Misali, labarin kamarzaman da Gimbiya Badura (Imam II, 1970:138), a Sin aka nuna an tada labarin amma uban Badura Musulmi ne, uwarsa, sunanta Fatima, jama’r kasar ma Musulmai ne, da makamantan wadannan da dama.
Su kuma wadanda suka danganta ‘Alfu Laila’ da kasar Farisa, sun yi haka ne ganin matsayin yankin a fagen raya adabin dauri, musamman yadda ake sane da cewa daga Farisa da Indiya ne aka bubbugo da rubuce-rubuce irin na ‘Alfu Laila.’ Wannan ne ya sa ake jin cewa ainihin littafin da Farisanci aka yi shi, Larabawa kuma suka dauka suka fassara shi, domin kuwa akwai wani dadadden littafi mai kama da ‘Alfu Laila’ na Larabci da harshen Farisanci. Burton ya karfafa irin wannan ra’ayi da cewa: Wannan littafi shi ne ‘Hazar Afsanah’ ko kuma ‘Labarai Dubu,’ wanda jama’a daga baya suka sani da ‘Alfu Laila’ (Burton, 1884:9:65).
Ba wani abu ya sa wasu suka amince da wannan hujja ba, sai ganin cewa labarin Sarki Shahriman da wazirinsa da ‘ya’yan wazirin biyu, mata, Shirzad da Dinarzad da labarin tafiye-tafiyen Sindibad, duk akwai su a cikin ‘Hazar Afsanah’ da kuma a cikin ‘Alfu Laila.’
In aka koma kan batun shekara ko lokacin da aka wallafa litttafin, nan ma ra’ayi ya bambanta. Abin da aka fi yarda a kai shi ne, an wallafa littafin ne a tsakanin karni na 10 zuwa na 16, Miladiyya. An gano haka ne ta bin diddigin ginuwar wasu labarai da wakokin da ke ciki da al’adu da tadojin jama’ar da labaran ke magana kansu da wasu abubuwa da suka hada da kayan kida da yake-yake. Daga kumshiyar wasu wakokin aka fahimci akwai labaran zamanin jahiliyya da kuma na zamanin wasu halifofi, kamar Haruna Rashid da kuma labaran da suka wanzu daga karni na 15 zuwa na 16. Wasu al’adun kamar shan giya da taba duk sun auku ne kafin karni na 15. Inda aka yi maganar bindiga da alburushi kuwa ana maganar zamanin karni na 16 da 17, lokacin da Turawa suka kirkiro su, har aka samar da su ga sauran al’ummu.
Ita kuwa maganar da ta shafi wanda ya rubuta littafin har yau sai dai hasashe ake yi, ba wata hujja gamsasshiya da aka kawo don sanin wanda ya yi aikin. Burton (1884;9: 85) yana jaddada cewa, “Ba wani da zai ce shi ne ya wallafa shi. Ba kuma wani da zai ce ga wanda ya rubuta shi a halin yanzu, saboda jama’a da dama sun sa hannu a kan aikin, wanda ya kawo sauyawar kamarsa ta ainihi.”
Domin haka, babu gamsashen ra’ayi a kan asalin littafin ‘Alfu Laila.’ Wasu masana suna ganin na Larabawa ne, wasu kuma suna cewa ya samo asali ne daga Farisa, inda littafin da ya gina shi, shi ne ‘Hazar Afsanah,’ wannan kuma kamar yadda Burton (1884;49:85) ya tabbatar bisa ganowarsa.
Daga labaran da aka nazarta kuwa, an sa zamanin tsara ko wallafa littafin tsakanin karni na 8 zuwa na 16. Abin la’akari shi ne, shi dai matanin na Larabci ya yi tashe kwarai, ya zama mashahuri matuka, ya shiga watayawa zuwa sassan duniya daban-daban, ciki kuwa har da kasar Hausa. Shi ma matanin ‘Alfu Laila’ na Ingilishi ya iso kasar Hausa tun a wajejen 1884.
Wannan tsakure ne daga littafina na ‘Adabin Abubakar Imam.’ Na gode.”
Farfesa na aje alkalaminsa, sai Fatuhu Mustapha yam aye gurbinsa, inda ya bijiro da ta’aliki kamar haka:
“Koda yake Farfesa Malumfashi ya yi dogon bayani a kan ‘Alfu Laila Wa Laila’ amma a gaskiya ina ganin ba labarun Larabawa ba ne. Domin in za a yi wa littafin kallon tsaf, za a tabbata bai yi kama da adabin Larabawa ba.
Na farko dai batsa muraran ba ta dauki hankalin masu kagaggen labaran Larabawa ba, ko da ‘Shu’ara’ da ake zaton an yi ta ne kan jima’i, wannan ya faru ne sakamakon jita-jitar da ake yadawa, musamman a kan wakokin Imruul kaisi, sai dai an manta, ba shi kadai ba ne a cikin littafin ‘Shu’ara,’ akwai irinsu ‘Nabiga’ da su ‘Hariri.’ Shi kansa kaisi, bai fito da batsar fili kamar yadda marubutan/cin ‘Alfu Laila’ ya fito da ita ba.
Wani karin hujja, sunayen da aka yi amfani da su wajen gina labarin, sunaye ne da suka yi kama da na Musulman Indiya da Farisa. Ka dauki Sarki Sindibad (Sinbad), kowa ya san ba Balarabe ba ne, haka kuma in ka cire Sarki Umaru an Nuuman, wanda ya yi wa Ibrizatu fyade da wasu ’yan kalilan, za ka ga sunayen sun fi kama da sarakunan Mugal na Indiya ko kuma sarakunan Musulunci na Farisa, irin su Aliyu Nuraddeen da sauransu.
Ban ki in an ce an kwaso wasu tatsuniyoyi na Larabawa ba, kamar yadda Malumfashi ya bayyana, yanayin rayuwa na tasiri a adabi, to haka ma in aka lura da ‘Dare Dubu Da daya,’ in an lura daulolin Indiya da Farisa a gabar teku suke ko kuma sun yi iyaka da teku, ba kamar Larabawa ba da suka yi yayi a cikin hamada, kafin Banu Umayyad su yi karfi. In an lura, kusan labaran da dama sun nuna kasashen da labarun suka afku, suna da alaka da koguna da rafukka da teku. Haka ma yanayin garuruwan, kusan tsarin zamantakewar ya fi kama da na kasashen Farisa da Indiya, fiye da kasashen Larabawa.
Sai dai ba mamaki in an aro wasu tatsunniyoyi na Larabawa, an sanya a ciki. Amma koma da me, tatsunniyoyin ‘Kama Sutra’ ba karamin tasiri suka yi ba a rubutun labarin. Kila shi ya sa wanda ya rubuta labarin, ya ki sanya sunansa saboda gudun fushin hukuma. Ni ina kyautata zaton asalin marubucin mutumin Indiya ne. Allahu a’alamu.”