Tauhidi ginshikin Musulunci (10)

Babi na Talatin da Biyu: Kada a ji tsoron wani kamar yadda ake tsoron Allah: Allah ya ce: “Wanda ya tsoratar da su Shaidan ne domin Shaidan yana tsoratar da masoyansa. Don haka kada ku ji tsoronsu, ku ji tsoroNa idan ku muminai ne.” (Ali Imrana: 175). A wata ayar Allah ya ce, “Hakika masu […]

Tauhidi ginshikin Musulunci (10)

Babi na Talatin da Biyu:

Kada a ji tsoron wani kamar yadda ake tsoron Allah:

Allah ya ce: “Wanda ya tsoratar da su Shaidan ne domin Shaidan yana tsoratar da masoyansa. Don haka kada ku ji tsoronsu, ku ji tsoroNa idan ku muminai ne.” (Ali Imrana: 175). A wata ayar Allah ya ce, “Hakika masu raya masallatai su ne wadanda suka yi imani da Allah da Ranar Qarshe, suka tsai da Sallah, suka ba da zakka kuma ba su ji tsoron kowa ba sai Allah. Wadannan da sannu za su zama cikin shiryayyu.” (Tauba: 18). Allah ya ce, “Akwai daga cikin mutane masu cewa sun yarda da Allah, amma idan wata fitina ta same su cikin hanyar Allah sai su dauki wannan fitina kamar azaba ce daga wajen Allah ta sauka musu saboda rashin tawakkalinsu.” (Ankabut: 10).

An samu Hadisi daga Abu Sa’id (RA) ya ce, “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, “Raunin imani ne ka nemi yardar mutane da fushin Allah, ko ka gode musu a kan arzikin da Allah ya ba ka, ko ka yi bakin ciki da mutane a kan abin da Allah bai ba ka ba. Domin kwadayin mai kwadayi ba ya kawo arzikin Allah kuma kin mai ki ba ya mayar da shi.” A’isha (RA) ta ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya nemi yardar Allah da fushin mutane to Allah zai so shi kuma ya tilasta mutane su so shi. Wanda kuma ya nemi yardar mutane da fushin Allah sai Allah ya yi fushi da shi kuma ya sanya mutane su ki shi.” (Ibn Hibban ya ruwaito).

 

 Babi na Talatin da Uku:

Dogara ga Allah:

Allah ya ce, “Ku dogara ga Allah idan kun kasance muminai ne.” (Ma’ida: 23). A wata ayar Allah ya siffanta muminai da cewa. ‘Hakika muminai su ne idan aka ambaci Allah sai zukatansu su raurawa. Idan aka karanta musu ayoyin Ubangiji, sai imaninsu ya karu, kuma su, ga ubangiji suke dogara.” (Anfal: 2) Allah ya ce a wata ayar, “Allah kadai ne Ma’ishinka (Ya Muhammad), kai da muminan da suke tare da kai.” (Anfal: 64). A wata ayar kuma ya ce, “Duk wanda ya dogara ga Allah, to Allah ya isar masa.” (Talak: 3).

Ibn Abbas (RA) ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakil.” Wannan kalmar Annabi Ibrahim (AS) ya fada lokacin da aka jefa shi cikin wuta, kuma ita ce Annabi (SAW) ya fada lokacin da aka ce masa, “Hakika mutane sun taru domin su yake ku, ku ji tsoronsu. Amma sai imaninsu ya karu. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Hasbunallah wa ni’imal wakil.” (Bukhari ya ruwaito). Ma’ana; Allah ya ishe mu kuma madalla da madogara Allah.

 

 Babi na Talatin da Hudu:

Kada mutum ya amince da makarun sai ya shiga Aljanna:

Allah ya ce, “Yanzu za ku amince wa makarun (jarraba) ubangiji? Ai ba wanda zai amince da makarun Allah sai mutane masu hasara.” (A’araf: 99). A wata ayar Allah ya ce, “Ba wanda zai debe kauna daga rahamar Ubangiji sai batattu.” (Hijri:56).

An samu Hadisi daga Ibn Abbas (RA). An tambayi Annabi (SAW) a kan manyan laifuffuka sai ya ce, “Shirka da Allah da yanke tsammani daga rahamar Allah da amince wa makarun Allah.” Ita kuma ruwayar Ibn Mas’ud (RA) ta ce, “Mafi girman laifi shi ne hada Allah da wani da amintuwa daga makarun Allah da yanke tsammani daga gafarar Ubangiji da debe tsammani daga rahamar Allah.” (Abdurrazak ya ruwaito).

 

Babi na Talatin da Biyar:

Hakuri a kan bala’in da Allah Ya dora wa mutum:

Allah ya ce, “Duk wanda ya yi imani da Allah, to Allah Zai shiryar da shi. Kuma Allah Masani ne a kan komai.” (Taghabun: 11). Alkamatu ya ce, ma’nar wannan ayar ita ce idan wata musifa ta samu mutum, ya sakankance cewa daga Allah ne, ya sallama al’amuransa baki daya ga Allah.

Abu Huraira (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, “Mutanen da ke da wadannan siffofi biyu, to suna tare da kafirci: suka ga wata kabila, da kuka a kan mamaci.”

Ibn Mas’ud (RA) ya ce Annabi (SAW), ya ce, “Wanda ya mari kuncinsa domin wani bala’i ya same shi, to ba ya cikin al’ummar Annabi (SAW), ko ya kekketa aljihunsa domin wata damuwa, ko ya yi kukan Jahiliyya (kamar ya ce na mutu na lalace bango ya fadi).”

An ruwaito daga Anas (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Idan Allah yana son bawanSa da alheri sai ya gaggauta dora masa musifa a duniya. Idan kuma Allah ya nufi mutum da sharri sai ya kame ga barin azabtarda shi a duniya har ya cika masa azaba mai tsanani a Lahira.” Annabi (SAW) ya ce, “Masu manyan sakamako su ne wadanda suka fi kowa shiga bala’i domin idan Allah yana son mutane sai ya jarrabe su. Wanda ya yarda da jarrabawar da aka yi masa, to, yana da yardar Allah tare da shi. Wanda kuma ya yi fushi da jarrabawar da Allah Ya yi masa, sai Allah ya yi fushi da shi.” (Tirmizi ya ruwaito).

 

Babi na Talatin da Shida: 

Riya:

Allah (SWT) ya ce, “Ka ce (Ya Muhammad SAW), ni mutum ne misalinku, sai dai ana yi min wahayi cewa Ubangijinku guda daya ne, wanda yake bukatar haduwa da Ubangiji (lami lafiya) to ya yi aiki mai kyau, kuma kada ya yi tarayya da Allah da kowa.” (Fussilat: 6).

Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa Allah ya ce a cikin Hadisin Qudsi, “Ni Mawadaci ne bisa a yi tarayya da ni. Duk wanda ya yi aiki ya hada nawa da na wani, zan bar shi da aikin da ya yi don wancan ya ba shi ladar.” (Muslim ya ruwaito).

Abu Sa’id (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, “Shin kuna so in ba ku labarin musifar da tafi ta Dujjal mai shafaffiyar albarka? Sai sahabbai suka ce, “eh muna so ya Manzon Allah!” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ita ce shirka boyayyiya. Kamar mutum ya tashi ya yi Sallah sai ya kawata Sallar idan ya ga ana ganinsa.” (Ahmad ya ruwaito).

 

Babi na Talatin da Bakwai:

Yi domin duniya shirka ne

 Allah ya ce, “Wanda yake Qaunar rayuwar duniya kawai da adonta, to Za mu cika masa sakamakon aikinsa a duniya har ma ba za a tauye masa wani abu daga darajarsa ko rayuwarsa ba. Amma ya sani idan Qiyama ta zo sakamakonsa wuta ne, kuma ya yi hasarar aikin da ya yi a duniya, kuma abin da ya aikata na alheri duk ya lalace.” (Hud: 15-16).

An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, ‘Bawan da yake aikinsa kawai neman kudi ne, to ya halaka. Bawan da yake aikinsa neman motoci ne ko abin hawa kawai, ya halaka. Idan ya samu abin da yake so ba wanda ya fi shi murna, idan kuma bai samu ba, sai ya kwana bakin ciki. Ya fadi ya kife (wato ya yi hasarar rayuwarsa ke nan). Koda kaya ce ta soke shi, to kada ka taimake shi. Amma madalla da bawan da ya rike akalar dokinsa domin daukaka addinin Allah, gashin kansa duk ya dunkule kuma gababuwansa duk suka yi kura. Idan tsaro aka sanya shi to yana nan tsaye ba zai bar wurin ba. Idan kuma a baya aka sanya shi, to yana nan a bayan. Koda ya nemi izini ba a yi masa izini ba, ko ya nemi a saukaka masa ba a saukaka masa ba, amma duk wannan bai dame shi ba.”         

 DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,

Abuja, 08036095723