Tauhidi ginshikin Musulunci (11)

Babi na Talatin da Takwas: Wanda ya yi biyayya ga malamai da sarakuna (shugabanni) ya haramta abin da Allah Ya halatta, ko ya halatta abin da Allah Ya haramta, to hakika ya rike su abin bauta koma bayan Allah: Ibn Abbas (RA) ya ce, wata magana ta faru tsakaninsa da wani sai ya ce masa […]

Tauhidi ginshikin Musulunci (11)

Babi na Talatin da Takwas:

Wanda ya yi biyayya ga malamai da sarakuna (shugabanni) ya haramta abin da Allah Ya halatta, ko ya halatta abin da Allah Ya haramta, to hakika ya rike su abin bauta koma bayan Allah:

Ibn Abbas (RA) ya ce, wata magana ta faru tsakaninsa da wani sai ya ce masa Annabi (SAW) ya ce kaza. Shi kuma sai ya ce wa Ibn Abbas “Ni ma dai na ji Abubakar da Umar sun ce hukuncin abin kaza ne.” Sai mamaki ya kama Ibn Abbas sai ya ce, “An kusa a yi ruwan duwatsu daga sama. Ina ce maka Annabi (SAW) ya ce ga yadda hukuncin yake, kai kuma kana ce mini ga abin da Abubakar da Umar suka ce?”

Imam Ahmad ya ce, ‘Ina mamakin mutane wadanda suka san Hadisi da asalin Hadisin amma su rika zuwa ra’ayin Sufyannus-Sauri, bayan Allah yana cewa, “Wadanda ke saba umarnin (Manzon) Allah shin ba su tsoron wata fitina ta same su ko azaba ta sauka a kansu?” ko kun san fitina kuwa? Ai ita ce tarayya da Allah. Abin da ya sa ko yake iya shiga shirka, yana iya yiwuwa ya karyata Hadisi sai zuciyarsa ta riya masa wani abu na karkata don haka sai ya fada ga halaka.

Adiyyu dan Hatim (RA) ya ji Annabi (SAW) yana karanta ayar nan da ke cewa, “Sun riki malaman yahudu da malaman Nasara alloli koma bayan Allah har ma da Isah dan Maryam bayan kuma Allah bai ce a yi haka ba. Abin da Allah ya yi umarni shi ne a bauta wa Ubangiji guda. Babu wani abin bautawa sai shi. Tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da ake shirka da shi.” Sai Adiyyu ya ce. ‘Ai ba mu bauta musu ya Rasulullah!” Sai Annabi (SAW) ya ce masa. “Ba suna haramta muku abin da Allah ya hallata ba ku kuma ku yarda ku bi su? Kuma suna halatta muku abin da Allah ya haramta ku kuma ku halatta din? Sai ya ce, haka ne ya Rasulallah. Sai Annabi (SAW) ya ce,”To ai bautarsu ke nan” (Ahmad da Tirmizi suka ruwaito kuma ya ce Hadisi ne mai kyau).

 Babi na Talatin  da Tara

 Duk wani hukunci idan ba na Allah da ManzonSa ba ne, to hukuncin dagutu ne

 Allah ya ce, “Shin ba ka yi dubi ba ne (Ya Muhammad) zuwa ga wadanda suka ce sun yarda da abin da Allah ya saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar kafin zuwanka amma duk da haka ga su suna kokarin kai hukuncinsu zuwa ga dagutu (duk wata doka da ta saba da ta Alkur’ani da Hadisi ita ce dagutu), alhali an yi musu umarni da su kafirce mata? Sai dai mu mun san ba komai ya sa suke haka ba, sai Shaidan ne kawai yake nufin ya batar da su batarwa mai nisa (yadda ake gane munafukai). idan aka ce musu ku zo zuwa ga Littafin Allah, ku zo zuwa ga Manzon Allah (Hadisan Annabi SAW), sai ka ga munafukai suna karkata ga barinka, karkata mai nisa. To yaya halinsu zai kasance idan wata masifa ta same su dalilin laifin da hannayensu suka gabatar? Idan wata masifa ta sauka a kansu, (ko suka nemi cin mutuncin Musulunci ko Alkur’ani ko Manzon Allah (SAW) sai Allah ya tona asirinsu), za ka ga sun zo gabanka suna ta rantsuwa da Allah wai domin kyautatawa da kuma kokarin dacewa.” (Nisa’i: 60-62).

Allah ya sake cewa, “Idan aka ce (wa munafukai) kada fa ku yi barna a bayan kasa, sai su ce ‘to wuce barna za mu yi? Ai mu masu gyara ne.’ (Allah ya ba su amsa da cewa) ku saurara wadannan mutane masu barna ne sai dai su ba su sani ba.” (Bakara: 11-12).

A wata ayar kuma Allah ya ce, “Kada ku bata kasa a bayan an gyara ta. Ku bauta wa Allah kuna masu tsoron azabarsa kuma kuna masu kaunar rahamarsa domin rahamar Allah kusa take ga masu aiki na kwarai.” (A’araf: 56). Allah yana fada wa duk masu yin hukunci ba da Littafinsa ko Hadisan Annabi (SAW) ba cewa: “Yanzu hukuncin Jahiliyya kuka fi kauna (daga hukuncin Allah?) To wa ya fi Allah iya hukunci? Babu masu gane haka sai mutanen da suka sakankance da imani.” (Ma’ida: 50). 

An samu Hadisi daga Abdullah Ibn Umar (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, “Imanin dayanku ba zai cika ba sai ya zama son sa shi ne son abin da na zo da shi (wato Alkur’ani).” Imamu Nawawi ya ce wannan Hadisi sahihi ne domin mun ciro shi ne a wani littafi da ake kira “Hujja da Sanadi Mai kyau.” Sha’abi cewa ya yi, an samu rashin fahimta tsakanin wani munafuki da wani Bayahude. Sai Bayahude ya ce, “Mu je wajen Annabi Muhammad (SAW)” domin Bayahuden ya san Annabi (SAW) ba ya karbar rashawa. Sai munafikin ya ce, “A’a, mu je wajen wane Bayahuden nan,” saboda ya san suna karbar rashawa. To daga karshe dai ba su je wajen Annabi (SAW) ba, kuma ba su je wajen Bayahuden ba. Sai suka je wajen wani boka a Juhaina domin ya yi musu hukunci. Sai Allah ya saukar da wannan ayar, “Shin ba ka yi dubi ba ne…” har zuwa karshenta. To wannan shi ne dalilin saukar wannan ayar ta cikin suratu Nisa’i.

An kuma ce wadansu mutane ne su biyu suka yi fada, sai daya daga cikinsu ya ce, “Mu je wajen Annabi (SAW) mana.” dayan kuma ya ce “Mu je wajen Ka’ab dan Ashraf.” Daga karshe dai ba su je wajen Annabi (SAW) ba, kuma ba su je wajen Ka’ab ba. Sai suka je wurin Umar bin Khaddab (RA) suka fada masa abin da ke tafe da su. Sai Sayyidina Umar (RA) ya tambayi wanda bai yarda aje wajen Annabi (SAW) ba, “Haka ne?” Sai ya ce, haka ne. Umar (RA) ya zare takobi ya fille masa kai.

 Babi na Arba’in:

 Hukuncin wanda ya musamta sunan Allah ko siffofinSa:

(Lokacin da wata ayar Alkur’ani ta sauka inda Allah yake cewa, “Ka kira Allah ko Mai Rahama, kowanne ka kira daidai ne domin yana da kyawawan sunaye.” Sai kafirai suka ce sun yarda da sunan Allah amma ba su yarda da ‘Mai Rahama’ ba. Shi ne Allah ya ce, “Su suna karyata Ar-Rahman; ka ce musu shi ne Ubangijina, ba abin bautawa da gaskiya sai shi. Gare Shi na dogara, kuma gare shi makoma take.” (Ra’ad: 30).

Aliyu (RA) ya ce, idan za ku yi magana da mutane, to ku yi musu magana ta yadda hankalinsu zai iya dauka. Ko kuna son su karyata Allah da Manzonsa ne? Ibn Abbas (RA) ya ga wani mutum ya tsorata lokacin da aka ambaci wata siffa ta Ubangiji domin ba ya son ta. Sai Ibn Abbas ya ce masa, “Mene ne bambancin wadannan mutane idan suka gane aya sai su yarda da ita, amma idan aya wacce take rikitarwa ta zo sai su karyata, (to yin haka kuskure ne)? Domin kuraishawa haka suka yi, yayin da suka ji Annabi (SAW) ya ce, “Ar-Rahman,” sai suka musanta wannan sunan sai Allah Ya saukar da ayar da aka ambata a sama (wato ayar, Suratur Ra’ad).

 DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,

Abuja, 08036095723