Tauhidi ginshikin Musulunci (16)

Cikin ikon Allah a yau munkawo karshen wannan rubutu daga littafin Kitabut Tauhid da DSP Imam Ahmad Adam Kutubi ya fassara bayan dogon muna gabatar da shi, muna fata an karu da abin da ya kunsa:   “Amma idan kuka yi wa makiya kofar rago suka ce sun tuba, amma a yi alkawari tsakaninsu da […]

Tauhidi ginshikin Musulunci (16)

Cikin ikon Allah a yau munkawo karshen wannan rubutu daga littafin Kitabut Tauhid da DSP Imam Ahmad Adam Kutubi ya fassara bayan dogon muna gabatar da shi, muna fata an karu da abin da ya kunsa:

 

“Amma idan kuka yi wa makiya kofar rago suka ce sun tuba, amma a yi alkawari tsakaninsu da Allah da Manzonsa, to kada ku sanya su karkashin alkawarin Allah da Manzon Allah. Idan sun yarda, ka sanya su karkashin alkawarinka da mutanenka domin ya fi sauki su warware alkawari (tsakaninka da su da warware alkwarin Allah). Ko idan kuka kewaye abokan gaba sai suka ce ku sanya mu cikin hukuncin Allah, to kada ku sanya su. Amma kana iya sanya su cikin hukuncinka. Domin idan ka sanya su a hukuncin ubangiji to ba ka sani ba ko za ka iya zartar da hukuncin Allah a kansu ko ba za ka iya ba.” Imam Muslim ya ruwaito.

Babi na Sittin da Hudu: Hani ga yanke hukuncin da yake na Allah ne:

An samu Hadisi daga jundub dan Abdullah (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Wani mutum ya ce da wani ‘Allah ba zai gafarta maka ba,’ sai Allah ya ce da wannan mutumin “Wane ne zai zama ubangiji a kaiNa cewa wai ba zan gafarta wa wane ba? To ni, hakika na gafarta masa, kai kuma aikin da ka yi Na bata shi.”  Imam Muslim ya ruwaito. 

Abu Huraira ya fassara wannan Hadisin da cewa, wani mutumin kirki ne mai ibada ya fada wa wani mai laifi cewa “Kai kam Allah ba zai gafarta maka ba,” Abu Huraira ya ce, wannan kalmar da ya fada ta bata aikinsa duniya da Lahira.

 Babi na Sittin da Biyar: Hani ga sanya tsani tsakanin Allah da bayinSa:

An samu Hadisi daga jubairu dan Mud’im (RA) ya ce, wani Balaraben kauye ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce, ya Manzon Allah! Rayuka sun halaka, iyalai kuma suna cikin yunwa, dukiya kuma ta halaka, Ubangijinka Ya shayar da mu ruwa mana. Muna rokonka ka zama mana tsani a tsakaninmu da Allah. Da kai muke neman taimako a wurin Allah! Sai Annabi (SAW) ya ce, ‘subhanallah, subhanallah (wato Tsarki ya tabbata ga Allah, tsarki ya tabbata ga Allah!) Annabi (SAW) bai gushe ba yana ta tasbihi har sahabbai suka gane haka kuskure ne. sai Annabi (SAW) ya ce Da balaraben “kaiconka! Ka san matsayin Allah kuwa? Ai wani ba ya zama tsani tsakanin Allah da bayinSa. Ai ba wani mutum da zai iya kubutar da wani a gaban Allah (idan mutumin ya sabba.)” Abu Dauda ya ruwaito.

 Babi na Sittin da Shida: Shamakin da Annabi (SAW) ya yi wa Tauhidi da toshe duk hanyar da za ta kai ga shirka:

An samu Hadisi daga Abdullahi dan shujairi (RA) ya ce, ni da jama’ar amir mun tafi wajen Annabi (SAW) sai muka ce masa, “Kai shugabanmu ne.” Sai Annabi (SAW) ya ce musu, “Allah (SWT) Shi ne Shugaba.” Sai muka dada ce masa, “Ka fi mu daraja a wajen Ubangiji kuma ka fi mu baiwa.” Sai Annabi (SAW) ya ce musu, “Ku daina wannan maganar ko kuma ku rage wani sashe na wannan maganar domin kada Shaidan ya halakar da ku.” Abu Dauda ya ruwaito. 

Anas (RA) cewa yayi, wadansu mutane sun ce, “Ya Manzon Allah! Ya fiyayyenmu! Ya dan fiyayyenmu! Ya shugabanmu! Ya dan shugabanmu!” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ya ku mutane! Ku daina wannan maganar saboda kada Shaidan ya halakar da ku. Ni dai Muhammadu ne, bawan Allah ne ni kuma Manzonsa ne. Ba ni so ku daga ni sama da matsayin da Allah Mai girma da Buwaya ya sanya ni.” Nisa’i ya ruwaito.

 Babi na Sittin da Bakwai: Mutane ba su bai wa Allah hakikanin matsayinSa ba:

Allah yana cewa, “Hakika mutane ba su bai wa Allah hakikanin matsayinsa ba, domin idan kiyama ta tsaya Allah zai damki kasa baki dayanta sannan sammai gaba dayansu a nade suke a hannun damanSa. Lallai tsarki ya tabbata a gare Shi (Allah) kuma Ya daukaka daga barin abin da suke tarayya da Shi.” Zumar: 67.

An samu Hadisi daga Ibn Mas’ud (RA) cewa wani daga cikin malaman Yahudawa ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce, “Ya Muhammad! Mun samu cewa Allah zai dauki (nade) sammai bakwai a yatsarsa, kasa bakwai ma a yatsarsS. Itatuwa ma a yatsarsa, tekuna baki daya a yatsarSa da kuma duk abin da ke karkashin kasa a yatsarsa, sauran halittu kuma duka a yatsarsa. Sai ya ce, “Ni ne sarki Allah ni kadai!’ Sai Annabi (SAW) ya yi murmushi har hakoransa na ciki suka bayyana domin gaskata Bayahuden nan malamin. Sai Annabi (SAW) ya karanta masa ayar nan ta Alkur’ani da ke cewa, “Mutane ba su bai wa Allah hakikanin matsayinsa ba domin kasa baki dayanta damkarsa ce.”

A wata ruwaya ta Imam Muslim ga yadda ta ce, “Allah zai dauki duwatsu da itatuwa a yatsa daya ya girgiza su ya ce, ‘Ni ne Sarki kuma ni ne Allah Ubangijin komai!” 

Shi kuma Imam Bukhari ga yadda ya ce, “Zai sanya sammai bakwai a yatsarsa, tekuna da sauran abubuwan da ke karkashin kasa a yatsarsa sauran halittu kuma a yatsarsa.” Bukhari da Muslim suka ruwaito.

An samu Hadisi daga Imam Muslim wanda Ibn Umar (RA) ya ruwaito daga Annabi (SAW) cewa “Allah zai nade sammai Ranar kiyama ya rike su da hannunsa na dama sannan Ya ce, “ni ne sarki. Ina sarakunan duniya, ina masu girman kai?” Sannan ya nade kassai bakwai ya rike su da hannunsa na hagu ya ce, “Ni ne Sarki. Ina masu girman kai. Ina masu karfi a bayan kasa?” Ibnu Abbas (RA) ya ce, “Sammai bakwai da kasa bakwai ba komai ba ne a hannun Ubangiji.” dan Jarir ya ce, Yunusa ya ba shi labari, shi kuma dan Wahab ya fada masa cewa “dan Zaidu ya ba ni labari daga Babansa (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, ‘Idan aka sanya sammai bakwai a kan Kursiyyun Ubangiji, kamar taro bakwai ne aka zuba cikin sahara.”

Abu Zarri (RA) ya ce “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, “Da za a dauki Kursiyyu a sanya ta a kan Al’arshi kamar wani zobe ne da aka jefa a hamada.”

Ibn Mas’ud cewa ya yi, “Nisan tsakanin kasa da sama ta daya tafiyar shekara dari biyar ce. Haka kuma yake tsakanin kowace sama zuwa ta kusa da ita tafiyar shekara dari biyar. Tsakanin sama ta bakwai zuwa Kursiyyu, tafiyar shekara dari biyar ce, tsakanin Kursiyyu da wani ruwa da ke sama tafiyar shekara dari biyar ce, sannan Al’arshi yana saman wannan ruwan, Allah yana kan Al’arshin. Duk da irin wannan nisa ba wani abu na ayyukan bayi da ke boyuwa a wajen Ubangiji.”  (Ibn Mas’ud ya fitar da shi daga Hammadu dan Salma, shi kuma daga Asim, shi kuma daga Zarri daga Abdullahi).

Wani malami da ake kira Mas’udi ya ruwaito daidai da wannan amma shi daga Asim ya ji, shi kuma daga Abu Wa’il ya ji shi kuma daga Abdullahi. Hafizuz-Zahabi ya ce masa, ai wannan Hadisi ya zo a hanyoyi masu yawa.

An samu Hadisi daga Abbas dan Abdulmuddalib (RA) ya ce, wanda Tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi ya ce, “Kun kuwa san nisan da ke tsakanin kasa da sama? Sai suka ce Allah da Manzonsa kawai suka sani.” Sai ya ce “Nisan da ke tsakanin kasa da sama tafiyar shekara dari biyar ce, kuma daga kowace sama zuwa saman da ke biye da ita tafiyar shekara dari biyar ce. Kuma kaurin kowace sama tafiyar shekara dari biyar ce. Tsakanin sama ta bakwai da Al’arshi akwai kogi wanda yake tsawonsa tafiyar shekara dari biyar ce kuma fadinsa tafiyar shekara dari biyar ce. Allah kuma na saman wadannan duka kuma babu wani abu da ke boyuwa a gare shi daga ayyukan ’ya’yan Adam.” Abu Dauda ya ruwaito.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Ta’likai.

DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja, Za a iya samunsa ta tarho: 08036095723